Bayan Zaben Osun, An Kwo Hanyar da Atiku, Kwankwaso da 'Yan Adawa Za Su Samu Nasara a 2027
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na PRP, Donald Duke, ya buƙaci ‘yan siyasar adawa su ajiye son zuciya da burin kansu domin kayar da APC a zaɓen 2027
- Tsohon gwamnan Cross River ya ce babbar matsalar adawa ita ce rashin iya haɗa kai da fifita muradin ƙasa
- Duke ya ce dole ne ‘yan adawa su gina kawance bisa manufa, ƙwarewa da shirin ceto Najeriya daga matsalolin tattalin arziki da tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abuja, Nigeria - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PRP, Donald Duke, ya shawarci ‘yan adawa da su binne son zuciyarsu da burins domin kayar da APC mai mulki a zaɓen 2027.
Duke, wanda tsohon gwamnan Jihar Cross River ne, ya ce babbar ƙalubalen da ke gaban ‘yan adawa ba wai ƙarfin jam’iyya mai mulki ba ne, illa rashin iya ajiye muradun kansu da yin aiki tare domin cimma manufa guda.

Source: Facebook
Leadership ta rahoto cewa a wata hira da aka yi d shi, ya ce ‘yan siyasar da ke son ƙalubalantar APC dole ne su kasance a shirye kuma su hada kai wuri guda.

Kara karanta wannan
'Yan takarar shugaban ƙasa 3 sun haɗa kai domin ƙwace mulki daga hannun Tinubu a 2027
Manyan yan adawar d ke harin kujerar shugaban kasa da mataimakinsa sun hada da Atiku Abubakar/Rotimi Amaechi da Peter Obi/Sanata Rabiu Kwankwaso.
Duke ya ja hankalin yan adawar Najeriya
Amma a cewar Donald Duka, ‘yan adawa ba za su iya cimma burinsu na zama shugaban ƙasa ba matukar ba su hada kansu ba.
Duke ya ce ‘yan Najeriya na neman wata madafa ta siyasa mai inganci, kuma nauyin samar da irin wannan madafa yana kan ‘yan siyasar adawa.
Ya ce ya kamata ‘yan siyasa su wuce batun wanda zai zama shugaban ƙasa, su fara cimma matsaya kan abubuwan da ya kamata a yi domin ceto ƙasar daga matsalolin tattalin arziki da tsaro.
Ɗan takarar na PRP ya ce burin kashin kai ya sha kawo cikas ga ƙoƙarin gina ingantattun kawancen siyasa a Najeriya.
Ya yi gargadin cewa idan jam’iyyun adawa suka ci gaba da tunkarar zaɓen 2027 kansu a rabe, za su iya raba ƙuri’un masu adawa da APC, ba tare da sani ba su ƙara wa jam’iyyar mai mulki ƙarfi.
Donald Duke ya ba yan adawa mafita
Duke ya ce dole ne a gina ƙawancen adawa na gaske bisa manufofi, ƙwarewa da kuma jajircewa wajen ciyar da ƙasa gaba, cewar Punch.
Ya kuma yi kira da a ƙara mayar da hankali kan matsalolin da talakawan Najeriya ke fuskanta, ciki har da tsadar rayuwa, rashin aikin yi, rashin tsaro, matsalar makamashi da ƙarancin ababen more rayuwa.

Source: Twitter
A cewarsa, ya zama dole ‘yan adawa su gamsar da ‘yan Najeriya cewa ba kawai sun haɗa kai ne domin kwace ikon siyasa ba, illa suna da cikakken shirin tafiyar da ƙasar.
'Yan takara 3 sun kulla hadaka a Rivers
A wani labarin, kun ji cewa ‘yan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyun Accord, AAC da SDP sun amince da haɗa ƙarfinsu domin samar da hadaka a zaɓen 2027.
Dr Gbenga Olawepo-Hashim na Accord, Omoyele Sowore na AAC da Prince Adewole Adebayo na SDP ne suka cimma wannan matsaya bayan wata ganawa da suka yi a Fatakwal.
Sun nuna damuwa kan yadda ake tattara ikon siyasa a hannun wasu, raunana cibiyoyin dimokuraɗiyya da kuma rage damar nuna adawa ta gaskiya.
Asali: Legit.ng
