APC Ta Gano Dalilin da Ya Sa Aka Lallasa Ta a Zaben Gwamnan Osun

APC Ta Gano Dalilin da Ya Sa Aka Lallasa Ta a Zaben Gwamnan Osun

  • APC ta yi magana kan abubuwan da suka jawo mata rashin nasara a zaben gwamnan jihar Osun da aka gudanar
  • Farouk Aliyu ya ce wasu mambobin jam’iyyar sun ki yin aiki tukuru saboda ba su ji dadin dan takarar da aka zaba ba
  • Hakazalika ya bayyana rashin nasarar a matsayin gargadi ga jam'iyyar APC gabanin babban zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Osun - Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta tabo batun rashin nasararta a zaben gwamnan jihar Osun.

Jam'iyyar APC ta amince cewa rikicin cikin gida, rashin jituwa kan dan takararta da kuma raina karfin masu kada kuri’a sun taimaka wajen kayar da ita a zaben gwamnan jihar Osun na 2026.

APC ta yi rashin nasara a zaben gwamnan Osun
Bola Oyebamiji wanda ya yi takarar gwamnan Osun a inuwar APC Hoto: Bola Oyebamiji
Source: Twitter

Farouk Aliyu, wani jigo a jam’iyyar APC ya bayyana hakan yayin wata hira da aka yi da shi a tashar Arise Tv ranar Litinin, 17 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan

Bayan shan kashi a Osun, shugaban matasan APC ya ba jam'iyyar mafita kan zaben 2027

Ya ce jam'iyyar APC “ta kayar da kanta” a Osun duk da dimbin albarkatun da ta yi amfani da su da kuma kokarin da ta yi domin samun nasara.

Rikicin APC ya yi tasiri

Farouk Aliyu ya ce rashin jituwa tsakanin mambobin jam’iyyar kan zabin dan takara ya shafi yadda APC ta gudanar da yakin neman zaben, inda wasu mambobi suka ki yin aiki wa jam’iyyar saboda ba su ji dadin dan takarar ba.

“Mun yi duk abin da mutum zai iya yi domin samun nasara a zaben. Akwai rikicin cikin gida mai yawa tsakanin mambobinmu a jihar Osun. Akwai mutanen da ba su ji dadin zabin dan takararmu ba,” in ji shi.

Ya ce ya kamata jam’iyyar ta tabbatar a zabubbukan da ke tafe cewa dan takararta yana da cikakken goyon bayan mambobinta.

“Wasu mambobin jam’iyyarmu ba su yi abin da ya kamata su yi ba saboda fushi, domin ba su son dan takararmu. Wannan shi ne babban matsalar cikin gida da muka samu; APC ta kayar da kanta a Osun,” In ji shi.

Kara karanta wannan

Abubuwa 3 da za su iya sa gwamna Adeleke doke APC a zaben Osun

Sai dai ya ki bayyana sunayen shugabannin jam’iyyar da yake ganin sun taka rawa wajen rashin nasarar, yana mai cewa ya kamata a warware batun a cikin gida.

APC ta raina masu zabe

Farouk Aliyu ya kuma soki APC kan yadda ta dauki masu kada kuri’a a Osun da wasa, yana mai cewa wasu mambobin jam’iyyar sun yi zaton tasirin gwamnatin tarayya zai tabbatar musu da nasara.

“Wasu sun yi tunanin gwamnatin tarayya za ta shigo kawai ta rubuta sakamakon zaben. Mambobinmu da magoya bayanmu sun raina Adeleke da tafiyarsa. Abin da ya kamata mu yi a wasu wurare, ba mu yi ba saboda muna tunanin za mu ci zaben ko ta yaya. Amma hakan bai faru ba,” in ji shi.

Ya kuma soki kalaman da sakataren jam’iyyar APC na kasa, Sanata Ajibola Basiru, ya yi a lokacin yakin neman zabe, yana mai cewa sun taimaka wajen jefa jam’iyyar cikin rashin nasara.

APC ta yi magana kan rashin nasararta a zaben gwamnan Osun
Dan takarar APC a zaben gwamnan Osun, Bola Oyebamiji Hoto: Bola Oyebamiji
Source: Twitter

Farouk Aliyu ya yaba wa Tinubu

Duk da haka, Aliyu ya yabawa Shugaba Bola Tinubu kan kin amfani da karfin gwamnatin tarayya wajen yin tasiri a zaben.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwan sani 11 kan jihar Osun yayin da ake gudanar da zaben gwamna

Ya kuma yabawa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) kan yadda ta loda sakamakon zaben a fili a shafinta na IReV.

Gwamna Adeleke ya yabawa Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Ademola Adeleke ya yabawa Shugaba Bola Tinubu bayan nasarar da ya samu a zaben gwamnan Osun.

Gwamna Adeleke wanda ya lallasa dan takarar APC, ya tabbatar da cewa Shugaba Tinubu ya kira shi domin taya shi murnar nasarar da ya samu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng