'Ba Jira': Kwankwaso Ya Fadi Tanadin NDC Wajen Nada Mukamai idan an Zabe Ta

'Ba Jira': Kwankwaso Ya Fadi Tanadin NDC Wajen Nada Mukamai idan an Zabe Ta

  • Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana tasirin da kusanci zai yi wajen raba mukaman gwamnati idan yan Najeriya suka zabe shi da Peter Obi
  • Kwankwaso ya bayyana cewa kwarewa da cancanta za su fi komai taka rawa a gwamnatin da jam'iyyar NDC ke kokarin kafa wa a Najeriya
  • 'Dan takarar mataimakin shugaban kasar ya ce gwamnatin NDC za ta yi gaggawar kafa majalisar ministoci domin fara aiki nan take bayan rantsar da ita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya bayyana wasu daga cikin shirye-shiryen jam’iyyar idan ta lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Ya bayyana cewa za a rika yin naɗe-naɗen mukaman siyasa ne bisa cancanta da kuma bukatun ƙasar ba wai wasu dalilai na kusanci ba.

Kara karanta wannan

'Ba su da sauran mamora a siyasa': Kwankwaso ya ce ta karewa su Ganduje a Kano

Kwankwaso ya ce da kwarewa za su yi aiki idan sun ci zabe
Peter Obi tare da Rabiu Musa Kwankwaso a wani taron jam'iyya a Abuja Hoto: Henry Seriake Dickson
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta kawo labarin cewa Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da da aka yi da shi a Abuja ranar Lahadi 16 ga watan Agusta, 2027.

Shirin gwamnatin NDC - Kwankwaso

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Kwankwaso ya ce gwamnati na buƙatar ƙwararrun mutane da suka haɗa da masana, kwararru da ‘yan siyasa masu gogewa domin tafiyar da ma’aikatu, hukumomi da sassan gwamnati yadda ya kamata.

Ya ce:

“Za a raba iko bisa bukatun ƙasa; za a naɗa masana da ƙwararrun ‘yan siyasa masu ilimin da ya dace.”

A cewarsa, shugaban ƙasa da mataimakinsa ba za su iya tafiyar da ƙasa su kaɗai ba, don haka akwai buƙatar mutanen da suka dace su taimaka wajen gudanar da gwamnati.

Alkawarin Kwankwaso kan nada mukamai

Kwankwaso ya ce gwamnatin NDC, idan har ta samu mulki, ba za ta yi jinkirin kafa majalisar ministocinta ba bayan rantsar da shugabanninta.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: 'Babu mai iya girgiza tikitin mu da Peter Obi a 2027'

Sanata Kwankwaso ya ce NDC ba za ta ja kafa wajen nada mukamai ba
Rabiu Musa Kwankwaso a tsakiyar masoyansa a wani taro a jihar Kano Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Twitter

Ya ce saboda zaɓaɓɓun shugabanni na da wa’adin shekaru huɗu kacal domin cika alkawuran da suka ɗauka, ya kamata su fara aiki nan take bayan kama aiki.

Ya bayyana cewa gwamnatin NDC za ta fifita cancanta, gogewa da iya aiki wajen zaɓar mutanen da za su yi wa Najeriya hidima.

Tsohon ministan tsaro ya kuma ce bai damu da zama mataimakin shugaban ƙasa ba, domin a ganinsa hidimar jama’a ta kamata ta kasance hanyar bayar da gudummawa wajen ci gaban ƙasa, ba neman mukamin siyasa kawai ba.

Kwankwaso ya dura kan wasu gwamnoni

A baya, mun ruwaito cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya ce gwamnonin da ke tunanin za su yi amfani da magudin zaɓe da ikon hukumomin jihohi domin ci gaba da mulki bayan 2027 za su sha kunya.

Tsohon gwamnan Kano ya ce rashin tsaro, talauci, rashin aikin yi da tabarbarewar ayyukan gwamnati na iya shafar yadda masu zaɓe za su kada ƙuri’unsu a babban zaben da ke kara karatowa.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce ’yan Najeriya na ƙara wayewa a siyasance kuma za su iya ƙin zaɓen gwamnonin da ke neman komawa kan kujerunsu idan ba su yi masu abin da ake bukata ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng