Babbar Kotu Ta Soke Tsarin INEC, Ta Sauya Lissafin Babban Zaben 2027 a Najeriya

Babbar Kotu Ta Soke Tsarin INEC, Ta Sauya Lissafin Babban Zaben 2027 a Najeriya

  • Babbar kotun tarayya ta soke wa'adin zaben fitar da gwani da na mika sunayen yan takara da hukumar INEC ta sanya wa jam'iyyun siyasa
  • Mai shari'a Mohammed Umarya bayyana cewa wa'adin da INEC ta sanya sun saba wa tanade-tanaden dokar zabe ta 2026
  • Sauran wadanda kotun ta soke sun hada da miƙa bayanan ‘yan takara, janye ko sauya ‘yan takara, fitar da jerin sunayen ƙarshe da kuma wa’adin dakatar da kamfe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta soke Sabon Jadawalin Zaɓen 2027 da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta fitar, lamarin da ya bai wa ‘yan siyasar da suka faɗi zaɓen fitar da gwani sabon fata.

Kotun ta ce wa’adin da INEC ta ɗora wa jam’iyyun siyasa domin gudanar da zaɓen fitar da gwani, miƙa sunayen ‘yan takara, maye gurbin wasu “ya saɓa da Dokar Zaɓe ta 2026."

Kara karanta wannan

Yayin da ake rigima kan magajin gwamna, an dakatar da zaben fitar da gwanin APC

Kotu.
Gudumar da alkalai ke amfani da ita a zaman shari'a a kotu Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Mai shari’a Mohammed Umar na babbar kotun mai zama a Abuja ne ya yanke hukuncin a ranar Laraba, 20 ga watan Mayu, 2027, kamar yadda This Day ta ruwaito.

An shigar da ƙarar ne domin ƙalubalantar jadawalin da INEC ta tsara na zaɓen 2027, wanda aka ce an yi ne domin hana waɗanda suka faɗi zaɓen fitar da gwani komawa wata jam’iyya su sake neman takara.

Kwafin hukuncin kotun ya nuna cewa jam’iyyar Youth Party ce ta shigar da ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/517/2016, inda ta sanya INEC a matsayin wadda ake ƙara.

Kotu ta yi wa INEC gyara

Bayan sauraron ɓangarorin biyu, Mai shari’a Umar ya ce bisa sashe na 29(1) na Dokar Zaɓe ta 2026, jam’iyyun siyasa na da damar miƙa bayanan ‘yan takararsu har zuwa kwanaki 120 kafin zaɓe.

Saboda haka, ya ce INEC ba ta da ikon rage wannan wa’adi ta hanyar saka ƙarin takura a jadawalinta.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu Alkali ya bi sahun Pantami, ya janye daga takarar gwamna a Gombe

Haka kuma kotun ta ambaci sashe na 31 na dokar, wanda ya bai wa jam’iyyu damar janye ko sauya ɗan takara har zuwa kwanaki 90 kafin zaɓe.

Hukuncin da babbar kotun ta yanke

Daga ƙarshe, kotun ta soke duk wa’adin da INEC ta saka a sabon jadawalin zaɓen 2027 wanda ya saɓa da tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026.

Wadanda kotun ta soke sun haɗa da wa’adin gudanar da zaɓen fitar da gwani, miƙa bayanan ‘yan takara, janye ko sauya ‘yan takara, fitar da jerin sunayen ƙarshe da kuma wa’adin dakatar da yaƙin neman zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262