Takarar Obi da Kwankwaso Ta Gamu da Koma Baya bayan Kotu Ta Yanke Hukunci kan NDC
- A kwanakin baya wata kotu ta bayar da umarni ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) domin ta yi wa jam'iyyar NDC rajista
- Wannan kotun a yanzu kuma ta janye wannan hukuncin sakamakon bukatar da aka shigar a gabanta kan lamarin
- Alkalin kotun ya bayyana cewa hukuncin ba zai iya ci gaba da aiki ba saboda ba a saurari wasu bangarori da ke cikin karar ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kogi - Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Lokoja, jihar Kogi, ta soke hukuncin da ta yanke a baya kan rajistar jam'iyyar NDC.
Kotun dai ta soke hukuncin wanda ta yanke a ranar 10 ga watan Disamba, 2025, wanda ya umarci hukumar zaɓe ta INEC da ta yi rajistar jam'iyyar NDC.

Kara karanta wannan
Bayan Boko Haram, ISWAP da Lakurawa, sabuwar kungiyar 'yan ta'adda ta bayyana a Arewa

Source: Facebook
Jaridar Tribune ta kawo rahoton cewa mai shari'a Isah Dashen ne ya yanke hukuncin a ranar Juma'a, 26 ga watan Yunin 2026.
Kotu ta janye hukunci kan rajistar NDC
Ya bayyana cewa tsohon hukuncin ba zai iya ci gaba da aiki ba saboda ba a saurari dukkan ɓangarorin da suka dace ba kafin kotun ta yanke hukunci.
Kotun ta bayyana cewa buƙatar da Peace Movement Party (PMP) ta shigar, wadda ke neman a sanya ta cikin shari'ar, tana da kwararan hujjoji, bayan ta tabbatar da cewa ita ma wani ɓangare ne mai muhimmanci a cikin lamarin.
Alkalin ya bayyana cewa tsarin shari'ar na baya yana da naƙasu, inda ya jaddada cewa rashin sauraron dukkan ɓangarorin da ke da hakki a cikin lamarin ya mayar da hukuncin a matsayin mara inganci.
Wane sabon umarni kotun ta bada?
Sakamakon haka, alƙalin kotun ya umarci da a koma yadda ake a baya har sai an tantance ainihin ƙarar.

Kara karanta wannan
A wata 1 kacal, hukumar kwastam ta tara kudin shiga sama da Naira biliyan 100 a tashar TinCan
Ya ƙara lura da cewa an ɓoye wasu muhimman shaidu wajen samun hukuncin na shekarar 2025, wanda hakan ya sa ya zama dole kotun ta soke hukuncinta na baya.
Bayan haka, alƙalin ya umarci da a sake fara shari'ar ta ainihi tun daga farko, tare da bayyanar INEC, Peace Movement Party (PMP) da kuma NDC a matsayin ɓangarori a cikin shari'ar.
An tunkari kotu kan rajistar NDC
Yayin da yake mayar da martani, lauyan masu shigar da buƙatar, C.S. Ekeocha, ya ce sun tunkari kotun ne bayan sun gano cewa rajistar NDC ta dogara ne a kan wani tambari da PMP ta riga ta miƙawa INEC kafin fara shari'ar.
Ya ce kotun ta amince cewa an taɓa haƙƙoƙin masu shigar da bukatar, kuma sakamakon haka ta soke hukuncin na baya, rahoton Leadership ya tabbatar da hakan.
“Kotun ta umarci dukkan ɓangarorin da su koma matsayin da suke da shi kafin hukuncin 10 ga Disamba, 2025."
- C.S Ekeocha

Source: Facebook
Me hukuncin kotun ke nufi?
Ya yi bayanin cewa tasirin wannan hukunci shi ne cewa kowane mataki da INEC ta ɗauka domin biyayya ga hukuncin da aka soke a yanzu ya zama wanda babu shi.
“Amincewa da jam'iyyar NDC, ba ta takardar shaidar rajista, sanya ta a cikin kundin bayanan INEC, da kuma kowane irin bayyana a kan takardun zabe da ya samo asali daga wancan hukunci dole ne a janye su har sai an kammala sauraron ainihin ƙarar."
- C.S Ekeocha
To sai dai kuma, ya fayyace cewa ainihin shari'ar tana nan a gaban kotu kuma ba a yanke hukunci a kanta ba tukuna.
Peter Obi ya maka Okonkwo kara kotu
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya kai Kenneth Okonkwo kara gaban kotu.
Peter Obi ya shigar da karar ne inda yake neman Naira biliyan 8 daga wajen Kenneth Okonkwo, kan zargin ɓata masa suna.
An dai shigar da karar ne bayan Kenneth Okonkwo ya yi wasu zarge-zarge kan Peter Obi wadanda ke nuna cewa ya karbi kudade a hannun masu neman takara a NDC.
Asali: Legit.ng
