Ta Faru Ta Kare: An Daura Sunan Atiku cikin 'Yan Takara a Shafin INEC
- Jam'iyyar ADC ta sanya bayanan 'yan takararta na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da mataimakinsa, Rotimi Amaechi a shafin INEC
- ADC ta ce hakan wani muhimmin mataki ne a shirye-shiryenta na tunkarar 2027, tare da jaddada aniyarta ta kawar da Bola Tinubu
- Atiku ya zama dan takarar jam'iyyar a ADC ne bayan ya kwarfe Rotimi Amaechi da Mohammed Hayatu-Deen a zaben fitar da gwani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Jam'iyyar ADC ta ɗaura sunaye da bayanan ɗan takararta na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da mataimakinsa, Rotimi Amaechi, a shafin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC).
An daura sunayen Atiku da Amaechi a shafin hukumar INEC da ke karɓar bayanan 'yan takara gabanin babban zaɓen shekarar 2027 a daren Talata.

Kara karanta wannan
NDC ta ɗauki mataki bayan hukuncin kotu, ta fara tura sunayen 'yan takara ga INEC

Source: Twitter
An sa sunan Atiku a shafin INEC
Mai magana da yawun jam'iyyar ADC na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ne ya sanar da hakan a ranar Talata ta cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X da aka tabbatar da sahihancinsa.
Ya ce:
“Muna farin cikin sanar da cewa mun yi nasarar ɗaura sunaye da bayanan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar (GCON), da ɗan takararmu na mataimakin shugaban ƙasa, Rotimi Amaechi (CON), a shafin INEC na karɓar sunayen 'yan takara.
“Wannan wani muhimmin mataki ne a shirye-shiryenmu na babban zaɓen 2027, kuma yana nuna ƙudurinmu na bai wa 'yan Najeriya damar samar da gwamnati mai cike da ƙwarewa, haɗin kai da farfaɗo da ƙasa.”
Dalilin daura sunan Atiku
Punch ta wallafa cewa daura sunaye da bayanan 'yan takara a shafin INEC na daga cikin sharuɗan doka da jam'iyyun siyasa ke bi wajen miƙa bayanan 'yan takararsu ga hukumar zaɓe cikin wa'adin da ta gindaya.

Kara karanta wannan
Kungiyar Obidient ta bada tabbaci kan takarar Obi da Kwankwaso a 2027 duk da hukuncin kotu
Atiku ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC bayan ya doke tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, da masanin tattalin arziki Mohammed Hayatu-Deen a zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar da aka gudanar a watan Mayun 2026.
Daga baya Amaechi ya amince ya zama mataimakin Atiku, lamarin da ya samar da cikakkun 'yan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar.
ADC ta bayyana kanta a matsayin babbar jam'iyyar adawa da ke shirin tunkarar zaɓen 2027, yayin da Atiku ke neman sake yin takarar shugaban ƙasa bayan ya yi takara a ƙarƙashin jam'iyyar PDP a shekarun 2019 da 2023.

Source: Facebook
NDC ta ce ta shirya hadaka
A wani labarin, mun kawo muku cewa jagoran jam'iyyar NDC na kasa, Sanata Seriake Dickson ya ce kofar su a bude ta ke domin yin hadaka a 2027.
Sanata Seriake Dickson ya bayyana cewa a shirye ya ke domin hada kai a lokacin da aka tambaye shi ko zai hada hanya da ADC ta su Atiku Abubakar.
A yanzu haka jam'iyyar NDC da Dickson ke jagoranta ta tsayar da Peter Obi a matsayin wanda zai mata takara a 2027 da Rabiu Kwankwaso a mataimaki.
Asali: Legit.ng