Rikicin ADC: Takarar Atiku Abubakar 'Tana Ƙasa Tana Dabo'

Rikicin ADC: Takarar Atiku Abubakar 'Tana Ƙasa Tana Dabo'

  • Wani ɓangare na jam'iyyar hamayya ta ADC ya fara kokarin jawo tangarda ga takarar Atiku Abubakar a kakar zaben 2027 bayan ya karbi tuta
  • Tsagin ya gargaɗi Atiku da ya daina bayyana kansa a matsayin ɗan takarar ADC, yana mai cewa bai shigahaɗaka da kowace jam'iyya ba
  • Tsagin da ke karkashin jagorancin Nafi'u Bala Gombe wanda ke adawa da sy David Mark ya bayyana wanda suka sanu a matsayin 'halastaccen' dan takara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja –Wani sagin ADC ƙarƙashin jagorancin Nafiu Bala Gombe ya bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ba shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar a zaɓen 2027 ba.

Tsagin ya ce jam'iyyar ta riga ta kammala dukkannin matakan cikin gida da suka wajaba tare da amincewa da Farfesa Chris Uba a matsayin wanda zai ɗaga mata tuta a babban zaɓen shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Jerin 'yan takara 26 da APC ta sauya sunayensu bayan zaben fitar da gwani

Nafiu Bala ya nesanta tsaginsa na ADC da takarar Atiku Abubakar
Shugaban ADC, David Mark Shugaban tsagin ADC Nafiu Bala da Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar/Nafiu Bala
Source: Twitter

Jaridar Punch ta wallafa cewa a cikin wata sanarwa da Nafiu Gombe ya fitar ranar Laraba, 1 ga watan Yuli, 2026, ya ce wannan bayani ya zama dole domin kare martabar jam'iyyar yayin da ake shirin babban zaɓen ƙasa.

Tsagin ADC ya zafafa adawa da Atiku

Jaridar The Guardian ta kawo labarin cewa tsagin ADC ya yi watsi da kwamitin gudanarwa na ƙasa da tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, ke jagoranta, yana mai cewa ba shi da hurumin doka ko kundin tsarin mulkin jam'iyyar na gudanar da harkokinta.

Nafi'u Bala Gombe ya ce:

"Atiku ba shi ne, kuma bai taɓa kasancewa ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC ba."

Tsagin ya dage cewa sahihin shugabancin ADC ne ke tafiyar da harkokin jam'iyyar, kuma ba ta shiga wata haɗaka, haɗewar jam'iyyu ko yarjejeniyar siyasa da kowace jam'iyya ba.

A cewarsa:

"Sahihin shugabancin ADC yana sane da yunƙurin da wasu masu son kafa haɗaka ke yi domin tursasa jam'iyyar shiga ƙawance da wasu dandamalin siyasa."

Kara karanta wannan

2027: Peter Obi ya bayyana tanadin da ya yi wa 'yan Najeriya na ayyukan alheri

Nafi'u Bala: 'Mun yi zabe a ADC'

Tsagin ya ce an gudanar da dukkannin matakan zaɓen cikin gida bisa tanadin kundin tsarin mulkin jam'iyyar da kuma dokar zaɓe ta 2026 ƙarƙashin jagorancin INEC, inda aka tsayar da Farfesa Chris Uba a matsayin halastaccen ɗan takara.

Nafiu Bala ya yi zargin cewa Atiku ba dan ADC ba ne
Atiku Abubakar a lokacin da ya ke karban tutar yi wa ADC takarar shugaban kasa Hoto: Atiku Abubakar
Source: Twitter

Sanarwar ta ce jam'iyyar ta yi imanin cewa Chris Uba yana da ƙwarewa, nagarta da karɓuwa a faɗin ƙasa domin jagorantar Najeriya.

A cewarsa:

"Shugabancin ADC yana gargadin Alhaji Atiku Abubakar gargaɗi na ƙarshe da ya daina, bayyana kansa ko yaɗa cewa shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC."

INEC ta dora sunan Atiku a manhajarta

A wani labarin mun wallafa cewa jam'iyyar hadakar 'yan hamayya ta ADC ta ce an sanya bayanan 'yan takararta na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da mataimakinsa, Rotimi Amaechi a shafin INEC.

ADC ta ce hakan wani muhimmin mataki ne a shirye-shiryenta na tunkarar 2027, tare da jaddada aniyarta ta kawar da Bola Tinubu da gwamnatin APC da ke ci gaba da rike kujerar shugaban kasar Najeriya.

Alhaji Atiku Atiku ya zama dan takarar jam'iyyar a ADC ne bayan ya kwarfe Rotimi Amaechi da Mohammed Hayatu-Deen a zaben fitar da gwanin da aka gudanar a sassa daban-daban na jihohin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng