2027: Malami Ya Gana da Ɗan Takarar Mataimakin Shugaban Kasa na Jam'iyyar ADC a Abuja
- Tsohon Antoni Janar kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, ya gana da dan takarar mataimakin shugaban kasa na ADC, Rotimi Amaechi
- Ganawar ta biyo bayan ziyarar da Amaechi ya kai wa Sanata Aminu Tambuwal, daya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar adawa ta ADC
- Jam'iyyar ADC na ci gaba da tuntuba, shawarwari da shirye-shirye domin tunkarar babban zaɓen 2027 da ke tafe a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tsohon Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, ya yi wata ganawa a sirrance da ɗan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Rotimi Amaechi.
Rahotanni sun nuna cewa wannan ganawa ta jiga-jigan biyu ta gudana ne yau, ranar Juma'a, 3 g watan Yulin 2026 a gidan Malami da ke Abuja.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a bayyana cikakken abin da suka tattauna ba.
Amaechi ya ziyarci Tambuwal
Ganawar ta zo ne kasa da sa'o'i 24 bayan Amaechi ya kai ziyara ga tsohon gwamnan Jihar Sokoto, Sanata Aminu Tambuwal, a Abuja.
Ziyarorin na zuwa ne yayin da shugabannin ADC ke ci gaba da tuntuba da shawarwari gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Tambuwal ya taya Amaechi murna
Bayan ganawarsu ranar Alhamis, Tambuwal ya taya Amaechi murnar zama ɗan takarar mataimakin shugaban kasa na ADC.
Ya bayyana shi a matsayin gogaggen ɗan siyasa, wanda kwarewarsa da jajircewarsa wajen kare dimokuraɗiyya za su ƙarfafa manufofin jam'iyyar.
Tambuwal ya ce:
"Ganawar ta ba mu damar sake nazari kan babban nauyin da ke gabanmu yayin da muke aiki tare da sauran 'yan Najeriya masu kishin kasa domin gina dandali mai ƙarfi da zao dawo da fata, ta ƙarfafa dimokuraɗiyya tare da samar wa al'umma shugabanci nagari."

Source: Facebook
Tambuwal ya yaba da hukuncin kotu
Tambuwal ya k0puma yi maraba da hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta tabbatar da sahihancin shugabancin ADC karkashin Sanata David Mark, kamar yadda Channels tv ta kawo.
A cewarsa, hukuncin ya ba jam'iyyar damar mayar da hankali wajen ƙarfafa haɗin kanta da kuma gabatar wa 'yan Najeriya wata sahihiyar mafita da ta ginu kan adalci, haɗin kai, ƙwarewa da sabunta kasa.
A baya-bayan nan ne jam'iyyar ADC ta bayyana Rotimi Amaechi a matsayin mataimakin ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, Alhaji Atiku Abubakar, a babban zaɓen 2027.
ADC ta tura sunan Atiku da Amaechi
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta sanya bayanan 'yan takararta na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da mataimakinsa, Rotimi Amaechi a shafin INEC.
Mai magana da yawun jam'iyyar ADC na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ne ya sanar da hakan a ranar Talata da ta gabata bayan INEC ta bai wa jam'iyyu damar tura sunayen yan takara.
Ya ce an daura sunayen Atiku da Amaechi a shafin hukumar INEC da ke karɓar bayanan 'yan takara gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Asali: Legit.ng

