"Bai Shafi Shari'armu ba": Nafiu Bala Ya Yi Magana kan Hukuncin Halasta David Mark

"Bai Shafi Shari'armu ba": Nafiu Bala Ya Yi Magana kan Hukuncin Halasta David Mark

  • Hon. Nafi'u Bala Gombe ya ce hukuncin kotun da ya amince da jagorancin David Mark bai shafi ƙarar da tsaginsu ya shigar ba
  • Ya bayyana haka ne a hira da ya yi da Legit, inda ya bayyana dalilin da 'dan majalisa, Leke Abejide, ya gaza samun nasara a karar da ya shigar
  • Nafi'u Bala Gombe, wanda ke takaddama da halaccin su Davida Mark ya kuma 'karyata cewa an dora sunayen su Atiku Abubakar a manhajar INEC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Gombe – Shugaban tsagin jam'iyyar ADC, Hon. Nafi'u Bala Gombe, ya bayyana cewa hukuncin kotun da ya halasta tsagin David Mark bai shafi shari'arsu da ke gaban kotu ba.

Ya bayyana haka ne bayan wani hukuncin kotu da ya tabbatar da jagorancin David Mark a shari'ar da ɗan majalisa, Leke Abejide, ya shigar a gaban kotu.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun ji jiki da dakarun sojoji suka farmake su a Plateau

Nafi'u Bala ya yi magana kan hukuncin kotu
Shugaban tsagin ADC mai adawa da 'yan hadaka, Nafi'u Bala Hoto: Hon. Nafi'u Bala
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa a hukuncin, kotun ta bayyana cewa ɗan majalisar ba shi da hurumin shigar da ƙara da zai ƙalubalanci jagorancin David Mark.

Kotu ta ba mu dama - Nafi'u Bala

A zantawarsa da Legit game da batun, Hon. Nafi'u Bala ya bayyana cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta san da zamansu, har ta ba su damar tura sunayen ƴan takara.

A kalamansa:

"Mutane su kwantar da hankalinsu, mu masu bin doka da oda ne. Kuma muna nan muna bi."
"Maganar gaskiya ita ce waɗancan mutanen suna yaɗa ƙarya cewa sun dora sunan Atiku Abubakar ko wani abu. Ƙarya ne wannan."
"Mu jam'iyya, dukkaninmu INEC ta ba mu dama, kuma muna nan muna tantance ƴan takara, kuma za mu kai su. Farfesa Chris Uba shi ne halastaccen ɗan takara a ADC."

Karin bayanin Nafi'u Bala kan hukuncin kotu

Kara karanta wannan

Sheikh Mansur Sokoto: Ma'anar batanci ga Annabi Muhammad SAW da hukuncinsa a Musulunci

Da yake ƙarin haske game da shari'ar da ɗan majalisar ya rasa a kotu, Nafi'u Bala Gombe ya ce wanda ya shigar da ƙarar ba shi da hurumi.

Nafiu Bala ya yi ce har yanzu ana jiran hukuncin kotu
Nafi'u Bala tare da mutanensa a wani tattakin adawa da su David Mark da suka yi a Abuja Hoto: Hon. Nafi'u Bala
Source: Twitter

A cewarsa:

"A tsarin shari'a, da kuma tsarin dokar ƙasa da dokar zaɓe, shi ba shi da hurumin shigar da ƙara kan shugabancin jam'iyya."
"Akwai abin da muke kira 'locus standi', shi ba shi da wannan, abin da kotu ta faɗa ke nan."

Ya ƙara da cewa ɗan majalisa Leke Abejide ya jima da ficewa daga jam'iyyar ADC zuwa APC, saboda haka babu wani dalili da zai sa ya shigar da ƙara a kotu kan shugabancin jam'iyyar.

Hon. Nafi'u Bala Gombe ya ce suna ci gaba da jiran hukuncin kotu game da ƙarar da suka shigar a matsayinsu na masu da'awar halaccin jagorantar ADC a Najeriya.

Nafi'u Bala ya karyata barazana ga rayuwarsa

A baya, kun samu labarin cewa shugaban tsagin ADC a Najeriya, Nafi’u Bala ya yi magana game da barazanar da aka ce an yi masa kan jam'iyyar adawa bayan ya kafa ya tsare cewa shi ne halastaccen jagora.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fadi abin da zai gudana a taron cika shekara 1 da rasuwar Buhari

Nafiu Bala ya musanta rahoton da ke cewa ya yi nadamar rikicin jam’iyya, ya kuma kara da cewa zargin da ake yi na cewa ana yi wa rayuwarsa barazana ba shi da tushe ballantana makama.

Ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya da farfaganda, yana mai cewa bai ba da wata hira ba kuma bai tura kowa ya yi magana madadinsa ba inda aka bayyana cewa akwai masu kawo wa ransa hari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng