An Zo Wajen: Trump Ya Fadi Babban Burin Gwamnatinsa kan Iran

An Zo Wajen: Trump Ya Fadi Babban Burin Gwamnatinsa kan Iran

  • Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana babban burin da gwamnatinsa take da shi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran
  • Iran ta ce har yanzu ba ta yanke shawarar komawa teburin tattaunawa da Washington ba, yayin da aka samu sabani kan yarjejeniyar Islamabad
  • Rikicin diflomasiyyar ya kuma shafi zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigin ruwan Hormuz, inda aka samu raguwar yawan jiragen dakon kayayyaki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sake jaddada cewa hana Iran mallakar makamin nukiliya shi ne “babban burin farko” na gwamnatinsa.

Kalaman Trump na zuwa ne yayin da kokarin diflomasiyya na kawo karshen rikicin Gabas ta Tsakiya ke ci gaba da tangal-tangal

Trump ya ce Iran ba za ta mallaki makamin nukiliya ba
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, a fadar White House Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Trump ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Truth Social ranar Litinin, 17 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Trump ya yi barazanar kai wa kawar Amurka mummunan hari

Me Trump ya ce kan Iran?

Shugaban kasar na Amurka ya dage cewa ba za a bar Iran ta mallaki makamin nukiliya “ta kowace hanya ko salo” ba.

“Babban burin farko shi ne, kuma zai kasance haka a ko da yaushe, Iran ba za ta iya mallakar Makamin Nukiliya ta kowace hanya ko salo ba,” in ji Trump.

Kalaman nasa sun zo ne a daidai lokacin da Tehran ta nuna cewa har yanzu ba ta yanke shawarar komawa tattaunawa da Washington ba, lamarin da ya kara rage fatan samun matsaya ta diflomasiyya cikin gaggawa.

Iran ta karyata wa'adin kwanaki 60

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baqaei, ya karyata rahotannin da ke cewa an sanya wa Tehran wa'adin kwanaki 60 karkashin yarjejeniyar fahimtar juna ta Islamabad da Amurka.

Baqaei ya ce yarjejeniyar ba ta kayyade wa'adin karshe ba, sai dai ta tanadi kwanaki 60 domin tattaunawa kan sassauta takunkuman da aka kakaba wa Iran da kuma shirinta na nukiliya.

Kara karanta wannan

"Ba abu ne mai sauki ba"; Gwamna Abba ya fadi wahalar mulkin Kano

Ya ce ana iya tsawaita wannan wa'adin idan ba a cimma yarjejeniya ba. A cewarsa, ba a taba fara tattaunawar ba saboda Iran na ganin cewa Amurka ta aikata “babban take hakki kuma mai fadi” na yarjejeniyar. Saboda haka, ya ce wa'adin kwanaki 60 ya zama ba shi da wani amfani.

Iran ta yi wa Amurka martani
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi Hoto: @Araghchi
Source: Twitter

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, shi ma ya ce a karshen makon da ya gabata cewa Tehran ba ta yanke shawarar komawa tattaunawa da Washington ba.

Jami'an Iran sun kuma yi watsi da rahotannin da ke cewa akwai wata kafar sadarwa ta sirri tsakanin Tehran da Washington ta yankin Kurdistan na Iraki, inda suka bayyana rahotannin a matsayin wani bangare na yakin tunani da na kafafen yada labarai.

Trump ya yi barazana ga Oman

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi barazanar kai wa kasar Oman hari wadda take kawa ce ga Amurka.

Shugaba Trump ya yi wa Oman barazanar kai hari ne idan ta kawo cikas ga kokarin Washington na cimma yarjejeniya da Iran kan sarrafa zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng