2027: Gwamna Fintiri Ya Mika Fom din INEC ga 'Yan Takarar Majalisar Adamawa

2027: Gwamna Fintiri Ya Mika Fom din INEC ga 'Yan Takarar Majalisar Adamawa

  • Gwamna Ahmadu Fintiri, ya gana da ‘yan takarar majalisar tarayya na APC tare da mika musu takardun tabbatar da nasarar zaben fitar da gwani
  • Barista Aliyu Wakili Boya ya karbi takardar INEC bayan ya lashe tikitin APC na mazabar Song/Fufore domin neman wa’adi na biyu a zaben 2027
  • Wasu daga cikin masu magana da Boya sun bayyana cewa ya gudanar da ayyuka da dama ciki har da hanyoyi, tallafin matasa, noma da samar da ayyuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Yola, Adamawa - Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa ya gana da 'yan takarar majalisar tarayya daga jam'iyyar APC a jihar.

Gwamnan ya ba yan takarar majalisar tarayya daga jihar Adamawa fom na tabbatar da nasararsu bayan zaben fitar da gwanin jam'iyyar da aka gudanar.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya kai karar jigon ADC kotu, ya nemi N8bn kan zargin bata suna

Gwamna Fintiri ya gana da 'yan takarar majalisar wakilai na APC a Adamawa
Gwamna Ahmad Fintiri (hagu) da Barista Aliyu Wakili Boye da ya ba takardar shaidar cin zabe. Hoto: Paul Barnabas Bulus
Source: Facebook

Fintiri ya mika fom ga 'yan takarar APC

Mai tallafawa gwamnan jihar Adamawa ta fuskar kafafen watsa labarai na zamani, Paul Barnabas Bulus ne ya wallafa hakan a shafinsa na Facebook.

Paul Barnabas Bulus ya sanar da cewa:

"Hon. Aliyu Boya Wakili ya karbi takardar INEC daga jagoran jam'iyyar APC na jihar Adamawa, Rt. Hon. Ahmadu Umaru Fintiri.
"Engr. Ahmad Salihijo Ahmad shi ma ya ziyarci mai girma gwamna domin karbar wannan takarda ta INEC. Duk wanda ba shi da wannan takarda ya fadawa yaransa gaskiya, ta kare masa."

Karanta sakon a nan kasa:

Rahoto ya nuna cewa, daga cikin wadanda aka ba fom ɗin akwai ɗan majalisar da ke wakiltar mazabar Song/Fufore, Barista Aliyu Wakili Boya.

Ɗaya daga cikin yaransa, Gambo PA Loko shi ya tabbatar da haka ga wakilin Legit Hausa yayin wata tattaunawa inda ya bayyana ƙoƙarin da ya yi a mazabarsa.

Kara karanta wannan

APC na shirin sauya dan takararta na gwamna a Adamawa? Jam'iyyar ta yi bayani

Kokarin Barista Aliyu Wakili Boye

Gambo PA Loko ya ce:

"An zabe shi karo na farko a zaben da ya gabata a matsayin dan majalisar tarayya na Song/Fufure, kuma daga zuwanshi sai ya yi sa a ya samu shugaban kwamitin majalisa mai kula da cibiyoyin 'yan sanda.
"Tun ba a je ko ina ba, akwai hanyar da ta fi shekara 20, aikinta ya gagara, hanyar tana nan kan titin Mubi; wannan babbar hanya ce a Arewa maso Gabas, wacce take zuwa har Kamaru, yanzu yana nan yana yinta.
"Ya kuma nemawa fiye da yara 150 aikin dan sanda, sannan ya raba motoci fiye da 60, mashina sama da 300 ga matasa don samun dogora da kai."

Gambo PA ya ce dan majalisar ya magance matsalar ruwa da ake fama da ita a yankuna masu yawa na mazabarsa, sannan ya bunkasa ilimi da matasa don ganin mazabar Song/Fufure sun samu ci gaba.

Gwamna Fintiri ya mika fom din shaidar cin zaben fitar da gwani ga 'yan takarar APC a Adamawa
Gwamna Ahmadu Fintiri yana mika takardar shaidar cin zabe ga Aliyu Wakili Boya. Hoto: Paul Barnabas Bulus
Source: Facebook

Mutane sun saya da Boya fom din takara

Kara karanta wannan

Tsagin PDP ya yi watsi da Pantami, ya gabatar da dan takarar gwamna a Gombe

Hakazalika, Gambo P.A ya tuna cewa al'ummar mazabar Fufure/Song ne suka taru, suka tara N30m domin saya wa dan majalisar nasu fom din takara, wadda N10m ne ake sayen fom din.

Ya ce ayyukan da ya yi wa al'ummar mazabar ne ya sanya suka ga dacewar sake ba shi damar ya wakilce su a 2027, kuma har ma ya samu nasara a zaben fitar da gwani na APC.

"Kuma a fuskar noma, ya raba famfunan ban ruwa masu amfani da rana, ya raba na'urorin bada haske masu amfani da rana, ya raba kayan noma rani, ya raba abubuwa da dama don ganin kauyuka sun koma birane.
"A bangaren mata, ya raba kekunan dinki, injunan markade, duk don ganin sun yi sana'o'i sun dogara da kansu, wanda zai bunkasa tattalinsu da na mazabar baki daya."

- Gambo PA Loko.

Kwamishina a Adamawa ya rasu

A wani labari, mun ruwaito cewa, daya daga cikin kwamishinonin jihar Adamawa, mai kula da ma'aikatar noma, Farfesa David Jatau, ya yi bankwana da duniya.

Farfesa David Jatau ya rasu ne bayan ya yi jinyar rashin lafiya a Abuja, inda daga karshe ya ce ga garinku nan a wani asibiti.

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya aika da sakon ta'aziyyarsa kan rasuwar kwamishinan wanda ya bayyana a matsayin jajirtaccen mutum.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com