Cutar Apollo Ta Ɓarke a Wasu Jihohin Arewacin Najeriya, Ta Fara Yaduwa cikin Jama'a

Cutar Apollo Ta Ɓarke a Wasu Jihohin Arewacin Najeriya, Ta Fara Yaduwa cikin Jama'a

  • Asibitin Kwararru na Jihar Yobe da ke Potiskum ya tabbatar da samun masu fama da cutar Apollo, watau ciwon idanu a garin
  • Mahukunta sun shawarci jama’a da su riƙa wanke hannu, guje wa taɓa ido da kuma kayan da wani ya riga ya yi amfani da su
  • Legit Hausa ta tataro cewa wanna buta ta sake bulla a wasu sassan jihar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Yobe, Nigeria - Asibitin Kwararru na Jihar Yobe da ke Potiskum ya tabbatar da samun masu fama da cutar kumburin ido mai tsanani, wato Apollo, yayin da ake nuna damuwa kan yadda cutar ke yaɗuwa a garin.

Asibitin ya buƙaci mazauna garin da su kula da tsaftar jikinsu da muhalli tare da bin matakan kariya domin dakile yaɗuwar cutar.

Kara karanta wannan

Dalilai 15 da suka sa APC ta sha kasa a zaben jihar Osun

Asibiti.
Gadajen da ake kwantar da marasa lafiya a asibiti Hoto: Picture Alliance
Source: Getty Images

Cutar Apollo ta bulla a garin Potiskum

Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban Kwamitin Ba da Shawarar Likitoci na asibitin, Dr Abubakar Sadiq Zakari, wanda ya wakilci Daraktan Lafiya na asibitin, ya ce an samu masu fama da cutar.

Sai dai ya ce mai yiwuwa adadin ya fi haka yawa saboda wasu daga cikin waɗanda suka kamu da cutar ba sa zuwa asibiti, suna jinyar kansu a gida.

Zakari ya shawarci mazauna garin da su riƙa wanke hannayensu a kai a kai, su guji taɓa idanunsu, sannan kada su raba tawul, tufafi, kayan kwanciya, kayan abinci da sauran kayayyakin amfanin wasu.

Ya kuma buƙaci waɗanda suka kamu da cutar da su rage kusanci da sauran mutane tare da zuwa asibiti da zarar sun fara nuna alamomin cutar.

Gwamnatin Yobe ta tabbatar da lamarin

Kwamishinan Lafiya da Ayyukan Jin Ƙai na Jihar Yobe, Dr Muhammad Lawan Gana, ya ce ma’aikatar ta ɗauki matakan dakile yaɗuwar cutar.

Kara karanta wannan

Yadda motoci suka nutse, komai ya tsaya cak bayan ambaliya a Abuja

Ya ce an samar da muhimman bayanai kan cutar tare da raba su ga masu ruwa da tsaki da kuma ta kafafen sada zumunta.

Ya ƙara da cewa an umarci jami’an wayar da kan jama’a kan lafiya da su ilmantar da al’umma ta hannun masu wayar da kan jama’a a ƙauyuka.

Mutanen Potiskum sun koka

Mazauna sassa daban-daban na Potiskum sun rika bayyana samun ƙaruwar masu fama da jajayen idanu ko kumburin ido, kaikayi, ciwo da kuma zubar hawaye.

Wani mazauni, Haladu Badejo, ya bayyana lamarin a matsayin abin tayar da hankali, yana cewa cutar na yaɗuwa cikin sauri, kamar yadda Punch ta kawo.

Wani mazaunin, Idris Bello Danchuawa, ya ce: “Subhanallahi! cutar Apollo (ciwon ido) har yanzu tana yaɗuwa a Potiskum.”

Apollo.
Mai fama da utar Apollo da wasu gadajen asibiti Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Cutar ta shiga yankunan Katsina

Binciken Legit Hausa ya tabbatar da cewa cutar ciwon idon ta bulla a wasu sassan jihar Katsina, ciki har da garin Dabai da ke karamar hukumar Danja.

Wani da ya kamu da Apollo, Husaini Lawal ya ce tun da mutum daya ya kamu a gidansu, sai da kusan kowa ya yi wannan ciwo saboda rashin kula da matakan kariya.

Kara karanta wannan

Ana korafi a kan zargin lakadawa Musa Mai Sana'a duka kan tallan Tinubu a Katsina

Wani ma'aikacin lafiya, Shu'aibu Saadu ya shaidawa Legit Hausa cewa ba a kamuwa da cutar ta hanyar kallon idon majinyaci kamar yadda mutane ke yadawa.

"Mutane na cewa wai da an kalli mai Apollo shikenan ka kamu, ba haka abin yake ba, ana kamuwa ne ta hanyar mu'amala da mai cutar, shiyasa ake so a rika wanke hannu da nesantar masu ita," in ji shi.

Kwalara ta barke a jihar Bauchi

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Jihar Bauchi ta tabbatar da bullar cutar kwalara bayan gwaje-gwajen dakin bincike.

An samu mutane 398 da ake zargin sun kamu da kwalara, yayin da mutane 16 suka mutu a kananan hukumomi 13 na jihar da ke Arewa maso Gabas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262