Jerin Jihohin da APC, APGA da Sauran Jam'iyyu ke Mulki gabanin Zaben Gwamnan Ekiti
Ado-Ekiti, Ekiti – Cikin ƙasa da sa’o’i 24 masu zuwa, al’ummar Ekiti za su fita rumfunan zaɓe ranar Asabar, 20 ga Yunin 2026, domin zaɓen wanda zai zama gwamnan jihar na gaba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Gwamna mai ci, Biodun Oyebanji na jam’iyyar APC, na neman sake wa’adin mulki na biyu a wannan zabe, wanda ake ganin zai ja hankalin yan Najeriya.

Source: Facebook
APC na neman tazarce a jihar Ekiti
Gwamna Oyebanji zai fafata da wasu ‘yan takara 13 masu neman karɓe masa kujerar gwamna, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.
Ko da yake akwai ‘yan takara 14 a zaɓen, manyan yan takarar da ake ganin za su iya yin tasiri sun haɗa da Gwamna Biodun Oyebanji na APC da Dakta Wole Oluyede na PDP da Dare Bejide na jam'iyar ADC.

Kara karanta wannan
An jibge jami'an tsaro, sun hana mutane zirga zirga a kananan hukumomi 2 a jihar Kano
Yayin da ake shirin zaben gwamnan Ekiti na gaba, Legit Hausa ta tattaro muku jihohin da APC da sauran jam'iyyun siyasa ke mulki a Najeriya. Ga su kamar haka.
Jihohin da APC ke mulki
Tashar TVC News ta ruwaito cewa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya na da jihohi 31 da ke karkashinta bayan sauya shekar da wasu gwamnonin PDP suka yi bayan zaben 2023
1. Adamawa – Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri
2. Akwa Ibom – Gwamna Umo Eno
3. Bayelsa – Gwamna Duoye Diri
4. Benue – Gwamna Hyacinth Alia
5. Borno – Gwamna Babagana Zulum
6. Cross River – Gwamna Bassey Otu
7. Delta – Gwamna Sheriff Oborevwori
8. Ebonyi – Gwamna Francis Nwifuru
9. Edo – Gwamna Monday Okpebholo
10. Ekiti – Gwamna Biodun Oyebanji
11. Enugu – Gwamna Peter Mbah
12. Gombe – Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya
13. Imo – Gwamna Hope Uzodinma
14. Jigawa – Gwamna Umar Namadi
15. Kaduna – Gwamna Uba Sani
16. Kano – Gwamna Abba Kabir Yusuf
17. Katsina – Gwamna Dikko Umaru Radda
18. Kebbi – Gwamna Nasir Idris
19. Kogi – Gwamna Ahmed Usman Ododo
20. Kwara – Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq
21. Lagos – Gwamna Babajide Sanwo-Olu
22. Nasarawa – Gwamna Abdullahi Sule
23. Niger – Gwamna Mohammed Umar Bago
24. Ogun – Gwamna Dapo Abiodun
25. Ondo – Gwamna Lucky Aiyedatiwa
26. Plateau – Gwamna Caleb Mutfwang
27. Rivers – Gwamna Siminalayi Fubara
28. Sokoto – Gwamna Ahmad Aliyu
29. Taraba – Gwamna Agbu Kefas
30. Yobe – Gwamna Mai Mala Buni
31. Zamfara – Gwamna Dauda Lawal.

Source: Twitter
Wace jihar ke hannun jam'iyyar APGA?
Jihar Anambra da ke yankin Kudu maso Gabashin Najeriya ce kaɗai jam’iyyar APGA ke mulki, ƙarƙashin Gwamna Charles Chukwuma Soludo.
Gwamna Soludo ya koma wa'di na biyu ne bayan sake lashe zabe a ranar 8 ga Nuwamba, 2025, a karkashin jam'iyyar APGA, kamar yadda BBC ta ruwaito.
Jihohin da APM ke mulki
Jam’iyyar adawa ta APM na da jihohi biyu da ke ƙarƙashin mulkinta, wadanda dukansu suka fito daga jam'iyyar PDP.
1. Bauchi – Gwamna Bala Mohammed
2. Oyo – Gwamna Seyi Makinde
Jihar da jam'iyyar Accord ke mulki
Jihar Osun ce kaɗai jam’iyyar Accord Party ke mulki, ƙarƙashin Gwamna Ademola Adeleke, wanda ya bar jam'iyyar PDP saboda rigingimun cikin gida.
Gwamna Adeleke na neman tazarce zuwa zango na biyu a zaben gwamnan jihar Osun, wanda za a gudanar ranar 15 ga watan Agusta, 2026, cewar rahoton Guadian.
Jam'iyyar LP na mulki a jiha 1
Kamar dai jam'iyyun Accord da APGA, jihar Abia ce kaɗai jam’iyyar LP ke mulki, inda Gwamna Alex Otti ke jagoranci.
Gwamna Alex Otti ya karbi mulkin Abia ne bayan nasarar da ya samu a zaben 2023, lokacin LP ta ba da mamaki saboda tasirin dan takararta na shugaban kasa, Peter Obi.

Source: Facebook
Ekiti: Dalilan da za su jawo faduwar PDP
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar PDP na ciki jam'iyyun siyasada za su gwabza a zaben gwamnan jihar Ekiti ranar Asabar, 20 ga watan Yuni, 2026.
Wole Oluyede, wanda likitan lafiya ne, ya zama ɗan takarar PDP a watan Nuwamba na shekarar 2025 bayan ya sami ƙuri'u 279 a zaɓen fitar da gwani.
Jam'iyyar PDP ta fuskanci matsaloli gabanin zaben Ekiti, wadanda ake ganin za su iya kawo mata gangarda ko ma ga sha kasa a zaben.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


