Iran Ta Tsokano Trump, Ya Sha Alwashi bayan an Shammaci Amurka

Iran Ta Tsokano Trump, Ya Sha Alwashi bayan an Shammaci Amurka

  • Shugaba Donald Trump ya ce Amurka za ta mayar da martani mai tsauri kan Iran bayan hare-haren da aka kai wa sansanonin sojin Amurka a Jordan
  • Tashin hankalin ya sake ƙaruwa a Gabas ta Tsakiya, yayin da farashin man fetur ya tashi da kashi 5 cikin 100
  • Iran ta ce ta kai hari kan sansanonin Amurka a Jordan, yayin da kafafen yaɗa labaranta suka zargi Amurka da kai hari a yankin Piranshahr

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Washington, Amurka - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar mayar da martani mai tsauri kan Iran bayan da ta kai hari kan sansanonin sojin Amurka da ke Jordan ranar Laraba.

Sabuwar barazanar ta zo ne yayin da yaƙin Gabas ta Tsakiya ya sake ƙamari, tare da sake jawo ƙungiyoyin da Iran ke goyon baya cikin rikicin.

Kara karanta wannan

Farashin mai ya sauka sosai bayan dakatar da yakin Amurka da Iran

Trump ya yi wa Iran barazana
Shugaba Donald Trump na Amurka a Oval Ofis Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Shugaba Trump ya yi barazanar ne dai yayin wata tattaunawa da tashar Fox News a ranar Laraba, 29 ga watan Yulin 2026.

An samu ɗan tsaiko a fafatawar, wanda ya sa wasu ke fatan za a koma teburin tattaunawa, amma alamun sun nuna cewa rikicin ya sake ɗaukar zafi.

Hakan ya sa farashin man fetur ya tashi da kashi 5 cikin 100, sakamakon fargabar cewa rikicin zai iya kawo cikas ga samar da man fetur a duniya.

Hare-hare sun ƙaru a Gabas ta Tsakiya

A ranar Laraba, Saudiyya da Amurka suka sanar da kai hare-hare kan sansanonin mayaƙan da ke da alaka da Iran a kasar Iraq.

A gefe guda, Isra'ila, ƙawar Amurka, ta zargi Hezbollah mai samun goyon bayan Iran da karya yarjejeniyar tsagaita wuta.

A cikin kwanaki biyu, Saudiyya, wadda ita ce ƙasar da ta fi fitar da man fetur a duniya, ta ce an kai hare-haren jirage marasa matuƙa kan wuraren da ake sarrafa ɗanyen mai.

Kara karanta wannan

Amurka ta fara fuskantar matsalar makamai, Trump ya dakatar da hare hare kan Iran

Saudiyya ta ɗora alhakin hare-haren kan ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai na Iraq da ke da alaƙa da gwamnatin Iran.

Trump ya yi barazana ga Iran

A yayin da Iran ta harba makamai masu linzami zuwa Jordan, Trump ya ce Amurka za ta mayar da martani mai ƙarfi.

Wakilin Fox News ya ruwaito Trump yana cewa:

“Za mu kai musu hari mai tsanani. Za su sha duka sosai.”

Rahoton ya ce shugaban Amurka ya yi amfani da kalamai masu ƙarfi domin jaddada matsayinsa, yana mai cewa:

“Za mu farmake su sosai.”

Iran ta zargi Amurka da kai hari

A gefe guda, gidan talabijin na ƙasar Iran ya ruwaito cewa Amurka ta kai hari a cikin yankin ƙasar.

“A ƴan mintunan da suka gabata, jiragen yaƙin maƙiya na Amurka sun kai hari a wani yanki da ke kusa da iyakar Piranshahr.”

Wannan na zuwa ne bayan kamfanin dillancin labarai na Fars ya ruwaito wani jami'i a jihar West Azerbaijan yana cewa wani makami mai linzami ya faɗa wani yanki da babu jama'a. Jami'in ya ce harin bai yi sanadin asarar rai ba.

Kara karanta wannan

An ja daga tsakanin Amurka da China kan haraji, kasar ta gargadi Trump

Trump ya yi barazana ga Iran
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tun da farko, rundunar sojin Jordan ta ce ta tare makamai masu linzami guda biyar da Iran ta harba.

Sai dai rundunar Revolutionary Guards ta Iran ta ce hare-haren sun nufi sansanonin sojin Amurka da ke Jordan.

Iran ta sayo makamai

A wani labarin kuma, kun ji cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sayo makaman kariyar sararin samaniya daga kasar China.

Yarjejeniyar ta shafi sayen makaman kariyar sararin samaniya da ake harbawa daga kafada (MANPADS) tsakanin guda 300 zuwa 400.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng