Babbar Magana: 'Yan Sanda Sun Cafke Sakataren Gwamnati da Wasu Mutum 5
- Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta kama Sakataren Gwamnatin Jihar, Teslim Igbalaye, tare da wasu mutum biyar bayan kai samame gidansa
- ‘Yan sanda sun ce sun kwato N4,810,500, katunan zabe biyu, rijistar masu zabe, kwamfutar tafi-da-gidanka da wasu kayayyaki
- Rundunar ta ce bincike ya fara domin gano alakar wadanda aka kama da zargin sayen kuri’u da sauran laifuffuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Osogbo, jihar Osun - Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta kama tare da tsare Sakataren Gwamnatin Jihar, Teslim Igbalaye, da wasu mutum biyar bayan kai samame gidansa da ke Osogbo ranar Laraba, 29 ga watan Yulin 2026.
‘Yan sanda sun ce daya daga cikin wadanda aka kama a gidan Sakataren Gwamnatin Jihar na cikin jerin mutanen da rundunar ke nema ruwa a jallo bisa zargin aikata laifuffuka.

Source: Twitter
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Abiodun Ojelabi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka samu a Osogbo, cewar rahoton jaridar The Punch.
Abubuwan da ‘yan sanda suka kwato
Ojelabi ya ce ‘yan sanda sun kwato N4,810,500 daga gidan Igbalaye, tare da katunan zabe na dindindin guda biyu, rijistar masu zabe, kwamfutar tafi-da-gidanka kirar Dynabook, na’urar yin kwafin takardu da kuma na’urar bugawa.
Sauran wadanda aka kama tare da Igbalaye sun hada da Akande Taiwo mai shekara 60, Oladele Abiodun mai shekara 38, Adeyemo Lukman mai shekara 45, Olaoye Muftau mai shekara 50 da Aderemi Musliu mai shekara 40.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ya ce wata tawagar ‘yan sanda ta kai samamen ne bayan samun bayanan sirri cewa wasu ‘yan kungiyar masu aikata laifuffuka suna buya a wani wuri a Osogbo.
"A yayin aikin, an kuma kama wadannan mutane: Hon. Igbalaye Teslim mai shekara 47, Akande Taiwo mai shekara 60, Oladele Abiodun mai shekara 38, Adeyemo Lukman mai shekara 45, Olaoye Muftau mai shekara 50 da Aderemi Musliu mai shekara 40.”
- Abiodun Ojelabi
Abin da bincike ya gano
Rundunar ta ce jami’anta sun kwato N4,810,500, kwamfutar tafi-da-gidanka kirar Dynabook, na’urar yin kwafin takardu, na’urar bugawa, katunan zabe guda biyu da rijistar masu zabe ta mazabu na daya zuwa 15.
“An adana wadannan kayayyaki cikin tsaro, kuma yanzu suna hannun ‘yan sanda domin gudanar da cikakken binciken kwararru da sauran bincike.”
- Abiodun Ojelabi
‘Yan sanda sun ce gano kudin da kuma rijistar da ke dauke da bayanan masu zabe ya haifar da damuwa mai tsanani kan yiwuwar aikata laifukan zabe da wasu laifuffuka.
Rundunar ta ce duk da cewa bincike yana ci gaba, bayanan da ake da su a halin yanzu sun ba da dalilin binciken yiwuwar aikata wasu laifuffuka.

Source: Original
Laifuffukan da ake bincike
‘Yan sanda sun ce daga cikin laifuffukan da ake bincike akwai zargin sayen kuri’u, wanda ya saba wa sashe na 121 na Dokar Zabe ta 2022.
Ana zargin an raba kudi ko wasu abubuwan amfani ga masu zabe da aka yi wa rajista domin yin tasiri kan zabinsu.

Kara karanta wannan
Tsohon IGP ya fallasa gwamnati, ya fadi abin da ya jawo lalacewar tsaron Najeriya
Sauran laifuffukan da ake bincike sun hada da hada baki wajen aikata laifi da kuma boye ko taimaka wa mutumin da ake nema ruwa a jallo.
Gwamnan Osun ya goyi bayan Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, da shugabannin jam’iyyar Accord na ƙasa, sun nuna goyon bayansu ga Shugaba Bola Tinubu.
Gwamna Adeleke da shugabannin na Accord sun amince da Shugaba Bola Tinubu a matsayin ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng

