Kalaman Tinubu Sun Harzuka ADC, Ta Yi Martani Mai Zafi ga Shugaban Kasa
- ADC ta ce ya kamata Shugaba Bola Tinubu ya mayar da hankali kan yaƙar ƴan ta'adda maimakon adawa
- Jam'iyyar ta ce kalaman Tinubu sun zo ne yayin da rashin tsaro ke ci gaba da ɗaukar rayukan 'yan Najeriya
- ADC mai adawa a Najeriya ta ce nasarar zaɓe na samuwa ne bisa nagartar aiki, ba barazanar nuna ƙarfin siyasa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) ta caccaki Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan furucinsa na cewa a shirye yake ya “ya ga abin da ya turewa buzu nadi” a fagen siyasa.
Jam'iyyar ta ce ya kamata shugaban ƙasar ya mayar da hankali wajen murƙushe ƴan ta'adda, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuffuka, maimakon yaƙar ƴan adawa.

Source: Facebook
Jaridar Tribune ta ce a wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na ƙasa na jam'iyyar, Mallam Bolaji Abdullahi, ADC ta ce kalaman shugaban ƙasar sun tayar da hankali.
Ta ce Tinubu ya yi furucin ne yayin ganawa da mambobin taron Bishof-Bishof na Cocin Katolika a Najeriya (CBCN), a daidai lokacin da rashin tsaro ke ƙara ta'azzara a ƙasar.
ADC ta yi magana kan harin Kaduna
Jam'iyyar ta yi nuni da harin da aka kai ƙauyen Naridon da ke karamar hukumar Kauru a jihar Kaduna, wanda ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 30.
ADC ta ce an kai harin ne da daddare, sa'o'i kaɗan kafin shugaban ƙasar ya yi kalaman nasa, jaridar The Punch ta kawo labarin.
A cewar jam'iyyar, an ƙona gidaje tare da raba iyalai da matsugunansu, yayin da wani ƙauye ya sake fuskantar mummunar asara.
"Saƙonmu ga shugaban ƙasa shi ne, yaƙin da ƴan Najeriya suka zaɓe ka domin ka jagoranta ba yaƙi ne da ƴan adawa ba.”
“Yaƙi ne da ƴan ta'adda, masu garkuwa da mutane da masu aikata laifuffukan da ke ci gaba da kashe fararen hula tare da kawo cikas ga zaman lafiya a al'ummomi daban-daban.”
- Bolaji Abdullahi
ADC ta soki yadda gwamnati ke mayar da martani
ADC ta kira Tinubu da “babban mai bayar da sanarwa na Najeriya,” tana mai cewa shugaban ƙasar ya zama mai sharhi idan ana maganar rashin tsaro.
Sai dai jam'iyyar ta ce idan maganar ƴan adawa ce, shugaban ƙasar yana nuna kamar mai yaƙi.
Jam'iyyar ta zargi gwamnatin Tinubu da mayar da martani ga hare-hare da Allah-wadai da fitar da sanarwa, maimakon ɗaukar matakan da za su kawo ƙarshen matsalar.
“Yaƙin da ya kamata Tinubu ya yi”
Jam'iyyar ta ce bayan fiye da shekaru uku a kan mulki, gwamnatin Tinubu ba ta da wani ingantaccen tarihin tsaro da zai tabbatar da irin ƙarfin gwiwar da shugaban ƙasar ya nuna a siyasa.
Ta ce saboda gazawar gwamnati wajen kare rayuka da dukiyoyin jama'a, abin da ya dace shi ne shugaban ƙasar ya yi nazari kan aikinsa, ba wai ya ƙara tsunduma cikin yaƙin siyasa ba.
“Ya kamata shugaban ƙasa ya ajiye kalamai da matakai masu ƙarfi irin su ‘yaƙi har ƙarshe’ domin murƙushe ƴan ta'adda, ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane."
- Bolaji Abdullahi

Source: Twitter
Ta ƙara da cewa bai kamata a yi amfani da irin waɗannan kalamai kan ƴan adawar da ke ƙoƙarin ceto ƴan Najeriya daga abin da jam'iyyar ta kira rashin kyakkyawan shugabanci da gazawar gwamnati ba.
“Abokan hamayyar shugaban ƙasa na gaskiya ba ƴan adawa ba ne. Su ne ta'addanci, ƴan bindiga, garkuwa da mutane da ƙaruwar rashin tsaron da ke ci gaba da kashe rayukan ƴan Najeriya.”
- Bolaji Abdullahi
ADC ta nuna yatsa ga Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa sakataren yaɗa labarai na ƙasa na jam'iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ya yi magana kan ci gaba da tsare Malam Nasir Ahmad El-Rufai.
Bolaji Abdullahi ya ce za a ɗora alhakin duk wani abu da ya samu tsohon gwamnan na jihar Kaduna, kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Legit.ng


