Ekiti 2026: Manyan 'Yan Takara 3 da Ake Ganin Za Su Iya Samun Nasara a Zaben

Ekiti 2026: Manyan 'Yan Takara 3 da Ake Ganin Za Su Iya Samun Nasara a Zaben

  • Jam’iyyar APC mai mulki ta tsayar da Gwamna Biodun Oyebanji takara karo na biyu a zaben gwamnan Ekiti da za a gudanar
  • 'Dan takarar ADC, Oluwadare Bejide, ya shiga zaben da gogewar siyasa sama da shekaru 30, yayin da hadakar jam’iyyun adawa ke kara karfi
  • Farfesa Oyebanji Olajuyin na jam'iyyar LP ya yi alkawura da dama, da suka hada da tausayi, kwarewa a mulki yayin neman kuri’un al’umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ekiti - Jihar Ekiti da al’ummarta na shirin gudanar da zaben gwamna a ranar Asabar 20 ga watan Yuni, 2026.

Hakan ya biyo bayan tsare-tsaren Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta tsara wacce ta tabbatar za a yi adalci.

Manyan yan takarar gwamna a zaben Ekiti
Dan takarar gwamnan Ekiti a LP, Oyebanji Olajuyin da na APC, Biodun Oyebanji da Oluwadare Bejide na jam'iyyar ADC. Hoto: Bioldun Oyebanji, Oluwadare Bejide.
Source: Facebook

Dalilan yin zabuka wasu jihohi daban-daban

Wannan zabe yana cikin zabukan da ake gudanarwa a lokuta daban-daban a Najeriya, sakamakon rikicin shari’ar zaben da ya samo asali tun daga babban zaben shekarar 2007, cewar Punch.

Kara karanta wannan

An jibge jami'an tsaro, sun hana mutane zirga zirga a kananan hukumomi 2 a jihar Kano

Kotun daukaka kara ta soke nasarar jam’iyyar PDP a lokacin, lamarin da ya haifar da sabon tsarin jadawalin zabukan gwamna a jihar.

Yayin da ake kara kusantar ranar zabe, yakin neman zabe ya kara zafi tsakanin jam’iyyun siyasa, tare da kalamai masu kaifi da wasu rikice-rikice a wurare daban-daban.

Masana na ganin wannan zabe mai zama zakaran gwajin-dafi duba da cewa ana shirin gudanar da babban zabe a Najeriya musamman yadda wasu ke ganin APC ta gaza a kusan dukkan bangarori.

Shirin Birtaniya kan zaben Ekiti

Babban Kwamishinan Birtaniya a Najeriya, Richard Montgomery, ya bayyana cewa kasarsa za ta tura masu sa ido.

Ya ce Birtaniya za ta sanya ido kan zabukan gwamnan Ekiti da Osun, tana mai jaddada cewa tana mutunta ikon Najeriya da tsarin dimokuradiyyarta.

Montgomery ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ya kai wa shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, a hedikwatar jam’iyyar.

Sai dai rahotanni sun nuna cewa an samu kwanciyar hankali bayan shiga tsakani da kokarin masu ruwa da tsaki domin tabbatar da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Jerin gwamnonin jihar Ekiti daga 1999 zuwa yau yayin da ake shirin sabon zabe a 2026

Legit Hausa ta duba muku wasu daga cikin ƴan takara da ake ganin suna da damar yin nasara.

1. Gwamna Biodun Oyebanji - APC

Daya daga cikin manyan ‘yan takarar shi ne Gwamna Biodun Oyebanji na APC, wanda ke neman wa’adi na biyu a matsayin gwamnan jihar.

Ana ganin yana da damar lashe zaben saboda kasancewarsa mai mulki, tare da goyon bayan jam’iyya mai mulki a matakin tarayya.

Kafin zamansa gwamna, Biodun Oyebanji ya taba rike mukamin Sakataren Gwamnatin Jihar a gwamnatin tsohon gwamna Kayode Fayemi.

Ya samu digirin farko a fannin Kimiyyar Siyasa daga Jami’ar Ekiti, sannan ya yi digirin digirgir a Dangantakar Kasa da Kasa da Nazarin Dabarun Mulki.

Gwamna ya shirya fafata wa da yan takara a zaben gwamnan Ekiti
Gwamna Biodun Oyebanji na jihar Ekiti. Hoto: Biodun Oyebanji.
Source: Twitter

2. Oluwadare Bejide - ADC

Gogaggen dan takara, Oluwadare Bejide na jam’iyyar ADC, ya samun karin karbuwa bayan hadakar jam’iyyun adawa.

Daily Trust ta ce Bejide mai shekaru 66 gogaggen dan siyasa ne wanda ya shafe sama da shekaru 30 yana aiki a harkokin siyasa da gudanarwa.

Ya taba zama sakataren NRC a tsohuwar Ondo, sannan ya kasance sakataren farko na PDP da kuma shirin UNDP a Ekiti.

Kara karanta wannan

'Yan takara 6 mafi yawan shekaru da za su fafata a zaben gwamnan Ekiti

Dan takarar ADC na daga cikin wadanda ake masu hasashen nasara
Sakataren ADC, Rauf Aregbesola, shugaban jam'iyyar, David Marka da dan takarar gwamna, Oluwadare Bejide. Hoto: @iamhistory.
Source: Twitter

3. Farfesa Oyebanji Olajuyin - LP

'Dan takarar jam'iyyar Labour, Farfesa Oyebanji Olajuyin, ya samu tikitin takara a jam’iyyarsa ta hanyar yarjejeniyar hadin kai a zaben fitar da gwani.

Olajuyin ya kasance likitan kunne, hanci da makogwaro, malami kuma dan siyasa daga Ikere Ekiti mai gogewa a fannin ilimi da lafiya, cewar Tribune.

Ya yi alkawarin kawo gaskiya, kwarewa da tausayi a tafiyar da mulki idan al’ummar Ekiti suka ba shi damar jagorantar jihar.

Dan takarar gwamnan Ekiti na LP ya shirya kalubalantar gwamna mai ci
Dan takarar gwamna a zaben Ekiti karkashin jam'iyyar LP, Oyebanji Olajuyin. Hoto: Oyebanji Olajuyin.
Source: Facebook

APC ka iya lashe zaben Ekiti

Mun ba ku labarin cewa za a gudanar da zabena Ekiti a ranar Asabar, 20 ga Yuni, 2026, domin zaɓen gwamna, inda sama da masu jefa ƙuri'a miliyan 1 suka yi rajista.

Gwamna mai ci, Biodun Oyebanji na jam’iyyar APC, na neman wa’adi na biyu a yayin da yake samun gagarumin goyon baya da amincewar ‘yan siyasa daban-daban.

Ana hasashen cewa tsarin APC a matakin ƙasa da wasu abubuwa za su ƙara wa jam'iyyar damar samun nasara a zaɓen gwamnan da ke tafe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.