Binciken Majalisa Ya Gano Rawar da Gwamnatin Tinubu Ta Taka a Kafa PFIPC

Binciken Majalisa Ya Gano Rawar da Gwamnatin Tinubu Ta Taka a Kafa PFIPC

  • Shugabar Ma'aikatan Gwamnatin Tarayya, Didi Esther Walson-Jack, ta amince ofishinta ya ba wa PFIPC izini bisa takardun bogi
  • Kwamitin Majalisar Wakilai ya gano wasiƙar naɗi da dokar kafa hukumar bogi da ta dauki hankali a ciki da wajen Najeriya da takardun bogi
  • A yanzu haka an janye duk wata amincewa da aka bai wa hukumar PFIPC, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano inda gizo ya yi saka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugabar Ma'aikatan Gwamnatin Tarayya (HoS), Didi Esther Walson-Jack, ta bayyana wa kwamitin musamman na majalisar wakilai da ke binciken hukumar bogi ta PFIPC abin da ta sani.

Ta bayar da tabbacin cewa ofishinta ya ba wa wannan hukuma izinin gudanar da aiki ne bisa takardun da aka gabatar masa.

Kara karanta wannan

Badakalar PFIPC: 'Yan sanda sun kasa kawo Adeniyi gaban Majalisa, an ji dalili

Majalisa ta kara gano bayanai game da kafa PFIPC
Adeyemi Adeniyi, mutumin da ya nada kansa shugabancin hukumar bogi Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa Esther ta ce takardun sun haɗa da wasiƙar naɗin Prince Adeniyi Adeyemi a matsayin shugaban Hukumar.

An gano sakaci kan hukumar PFIPC

Jaridar Punch ta ruwaito Didi Esther Walson-Jack ta amince cewa da an gudanar da cikakken bincike yadda ya kamata, da an gano cewa takardun na bogi ne.

A kalamanta:

"Lokacin da wannan batu ya taso, na nemi a kawo min takardun, kuma na gano cewa dokar kafa hukumar ba ta sahihiyar dokar Majalisar Dokoki ba ce."

Kwamitin da Yusuf Gagdi ke jagoranta na binciken yadda PFIPC ta samu ofis a Sakatariyar Tarayya da ke Phase III da kuma yadda aka saka mata fiye da N1.3 biliyan a cikin kasafin kuɗin 2026.

Tun da farko, Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya musanta kafa PFIPC.

Yadda ake bincike kan PFIPC

Daga baya Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana Adeyemi a matsayin ɗan damfara, tana mai cewa 'yan sanda sun gurfanar da shi a kotu.

Kara karanta wannan

Likitan El Rufa'i ya rubuta zungureriyar takarda, ya yi bayani kan zargin ICPC

Sai dai bayanan ba su yi magana kan yadda aka saka hukumar cikin kasafin kuɗi ba, ko kuma zargin da Adeyemi ya yi na cewa ya biya N400m ta hannun wasu domin a sauƙaƙa masa samun muƙamin.

Majalisar wakilai ta na ci gaba da binciken PFIPC
Wasu daga cikin yan majalisar wakilan Najeriya Hoto: House of Representatives
Source: Facebook

Bincike ya kuma nuna cewa Adeyemi ya samu amincewar ɗaukar ma'aikata 300, tare da buɗe asusun kuɗin waje a Babban Bankin Najeriya (CBN).

Didi Esther Walson-Jack ta ce ofishinta kan amince da sababbin hukumomi idan an gabatar masa da dokar kafa su da kuma wasiƙun naɗi.

Ta ce:

"Mun karɓi wasiƙar naɗi da dokar kafa hukumar, sannan bisa waɗannan takardu da kuma tattaunawar da muka yi da wakilan PEAC da PFIPC, muka ba su izinin kafa hukuma da kuma izinin ɗaukar ma'aikata."

Ta ƙara da cewa:

"Yanzu da muka ga dukkan takardun, mun amince cewa ya kamata mu gudanar da ƙarin bincike kafin bayar da waɗannan amincewa."

ICPC ta titsiye Gbajabiamila kan PFIPC

A baya, mun kawo labarin cewa hukumar yaki da cin hanci ta ICPC ta titsiye Femi Gbajabiamila kan zargin da ake yi game da PFIPC da ake takaddama a kai.

Mai ikirarin shugabantar PFIPC, Adeniyi Adeyemi ya zargi shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa da karbar N400m domin ya samu shugabancin hukumar.

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasar, Femi Gbajabiamila ya musanta zarge-zargen tare da shigar da ƙarar N15bn kan Adeniyi .

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng