Gwamnati Ta Fusata, Ta ba da Umarnin Cafke Mai Kamfanin Telegram, Pavel Durov
- Gwamnatin Rasha ta zargi Telegram da kin dakatar da tashoshin da ake amfani da su wajen daukar ma'aikata domin ayyukan ta'addanci
- Hukumar tsaron cikin gidan kasar ta fitar da sammacin kama Pavel Durov, tana zarginsa da taimaka wa ayyukan ta'addanci ta hanyar Telegram
- Pavel Durov ya taba barin Rasha tun 2014 bayan ya ki bin umarnin gwamnati, kuma yana fuskantar bincike daban a Faransa tun 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Rasha – Hukumomin Rasha sun gurfanar da wanda ya kafa manhajar Telegram, Pavel Durov, kan zargin taimaka wa ayyukan ta'addanci, suna masu cewa an yi amfani da manhajar wajen daukar ma'aikata da shirya hare-haren leken asirin Ukraine.
Hukumar tsaron cikin gida ta Rasha (FSB) ta ce an yi amfani da Telegram wajen "shirya da kuma daidaita ayyukan zagon kasa da ta'addanci" a cikin kasar, tana zargin kamfanin da gaza rufe tashoshi, rukuni da kuma bots da hukumomin Ukraine ke amfani da su.

Source: Getty Images
Telegram ya mayar da martani
Sakamakon haka, Rasha ta fitar da sammacin kama Durov a matakin kasa da kasa, wanda ke nufin ana nemansa ruwa a jallo, in ji rahoton BBC.
Jim kadan bayan sanar da tuhumar, shafin Telegram na X ya wallafa hoton Durov yana nuna yatsa na tsakiya, alamar martani ga matakin da hukumomin Rasha suka dauka.
A baya, Durov ya taba zargin gwamnatin Rasha da kirkirar sabbin dalilai domin takaita wa 'yan kasar damar amfani da Telegram.
Durov ya bar Rasha tun shekarar 2014
Telegram na da matukar farin jini a Rasha, inda miliyoyin mutane ke amfani da ita duk da matakan da gwamnati ke dauka na takaita wasu ayyukan intanet. Haka kuma, manhajar na daga cikin hanyoyin sadarwa da aka fi amfani da su a Ukraine.
Durov mai shekaru 41, wanda haifaffen Rasha ne, ya dade da barin kasar kuma yanzu yana da fasfo na Faransa da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).
Sai dai ba a san ko sauran kasashe za su amince su aiwatar da sammacin kama da Rasha ta fitar ba.
Dalilin ficewarsa daga Rasha da binciken Faransa
Durov ya bar Rasha ne a shekarar 2014 bayan ya ki amincewa da bukatar gwamnati ta rufe shafukan 'yan adawa a dandalin VKontakte, kamfanin sada zumunta da ya kafa wanda ake yi wa lakabi da "Facebook na Rasha."
Telegram, wadda ke da kusan masu amfani miliyan 950 a duniya, ta dade tana bayyana kanta a matsayin manhajar da ke bai wa sirrin masu amfani muhimmanci fiye da sauran kafafen sada zumunta.
Sai dai manhajar ta sha suka kan yadda take sa ido kan abubuwan da ake wallafawa, zargin da kamfanin ya musanta.
A shekarar 2024, hukumomin Faransa sun kama Durov tare da fara bincikensa kan zargin rashin daukar isassun matakan dakile amfani da Telegram wajen aikata laifuka. Daga baya an sake shi, yayin da binciken ke ci gaba.
Asali: Legit.ng

