Dalilan da Za Su Iya Sanyawa PDP Ta Sha Kashi a Zaben Gwamnan Jihar Ekiti na 2026

Dalilan da Za Su Iya Sanyawa PDP Ta Sha Kashi a Zaben Gwamnan Jihar Ekiti na 2026

Jihar Ekiti - Masu kada kuri'an na shirin zaɓen gwamnan jihar Ekiti wanda za a gudanar a ranar Asabar, 20 ga Yunin 2026.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Takarar za ta zama kamar wani gwaji ne na ganin ko jam’iyyun hamayya za su iya doke gagarumin rinjayen da ke tattare da ikon gwamnati mai ci, goyon bayan tarayya, da kuma ingantaccen tsarin siyasa.

PDP za ta fafata a zaben gwamnan jihar Ekiti
Dr. Wole Oluyede, dan takarar gwamnan Ekiti na PDP Hoto: Natasha H Akpoti
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro wasu abubuwa da za su iya sanyawa jam'iyyar PDP mai adawa ta yi rashin nasara a zaben.

Gwamnan jihar Ekiti yana fuskantar adawa

A tsakiyar wannan zaɓe akwai Biodun Oyebanji, gwamnan jihar kuma ɗan takarar jam'iyyar APC, wanda ke neman wa'adin mulki na biyu bayan ya shafe shekaru huɗu a kan kujerar.

Babban ƙalubalensa sun fito ne daga wurin Wole Oluyede na jam'iyyar PDP da kuma Oluwadare Bejide na jam'iyyar ADC.

Kara karanta wannan

Ba ɗan Kwankwaso tikitin mataimakin ɗan takarar gwamna a NDC ya bar baya da kura

Wane ne dan takarar PDP?

Wole Oluyede, wanda likitan lafiya ne, ya zama ɗan takarar PDP a watan Nuwamba na shekarar 2025 bayan ya sami ƙuri'u 279 a zaɓen fitar da gwani na gwamna na jam'iyyar, inda ya doke abokin hamayyarsa mafi kusa, jaridar Premium Times ta kawo labarin.

Mista Oluyede ba sabon bako ba ne a tseren gwamna na Ekiti domin ya taɓa tsayawa takara a shekarar 2022 a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar ADC daga baya ya koma PDP.

Kamfen ɗinsa ya mayar da hankali ne a kan garambawul ga fannin kiwon lafiya, samar da ayyukan yi, tsaro, da kuma hujjar karba-karba da ke cewa ya kamata yankin Kudancin Ekiti ya samar da gwamna na gaba.

Abubuwan da za su iya kawo cikas ga PDP

Jam'iyyar PDP ta fuskanci matsaloli gabanin zaben na ranar Asabar, 20 ga watan Yunin 2026 wadanda za su iya kawo mata cikas.

Wadannan matsalolin za su iya sanyawa ta kasa samun kuri'u masu kauri a zaben, wanda hakan na iya sanyawa ta zo a bayan APC da ADC.

Kara karanta wannan

Matasan 'yan takara 4 a zaben gwamnan jihar Ekiti na shekarar 2026

Ga jerinsu nan kasa:

1. Cire sunan dan takarar PDP

Hukumar INEC ta cire sunan Wole Oluyede daga cikin jerin sunayen 'yan takara na wucin gadi da na ƙarshe.

INEC ta kafa hujja da hukunce-hukuncen kotu da ba a warware ba dangane da shugabancin jam'iyyar da zaɓen fitar da gwani, rahoton The Cable ya nuna hakan.

Cire sunan da hukumar zabe ta iNEC ta yi, ya yi barazanar rushe daukacin yakin neman zaben PDP baki ɗaya a jihar Ekiti.

Sai da aka samu hukuncin babbar kotun tarayya da ke Abuja, wanda daga baya kotun daukaka kara da ke Akure ta tabbatar, kafin a tilasta wa hukumar zaɓe ta amince da Oluyede a matsayin ɗan takarar jam'iyyar.

2. Rikicin cikin gida

Jam'iyyar PDP ta shiga fagen zaɓen tana fama da rarrabuwar kawuna sakamakon rikicin shugabanci da na cikin gida.

Rikicin ya bazu zuwa kotuna kuma daga baya ya shafi shigar jam'iyyar cikin tseren neman kujerar gwamna.

Kara karanta wannan

Jerin gwamnonin jihar Ekiti daga 1999 zuwa yau yayin da ake shirin sabon zabe a 2026

Dr. Oluyede ya zama dan takarar gwamnan Ekiti na PDP
Dan takarar gwamnan jihar Ekiti na PDP, Dr. Wole Oluyede Hoto: Dr. Wole Oluyede
Source: Facebook

3. Gwamna a PDP ya goyi bayan Oyebanji

Jagoran jam'iyyar PDP kuma tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, yana cikin tsofaffin gwamnonin da ke goyon bayan sake zaɓen Gwamna Oyebanji.

Jaridar The Nation ta ce a kalamansa a wurin taron amincewa da tsofaffin gwamnonin Ekiti suka gudanar, Ayo Fayose ya ce ya yanke shawarar marawa Gwamna Oyebanji baya domin gudanar da harkokin jihar cikin lumana, saboda yana wakiltan abin da ya siffanta da “Ekiti Agenda".

“Ya kamata na kasance fuskar hamayya a jihar Ekiti, amma dole ne na yi abin da nake kira 'Ekiti Agenda'. Ni ɗan Ekiti ne kafin na zama gwamna."
"Dubi yadda wannan gwamna ya haɗa kanmu duka, ina kallonsa a matsayin wanda ke wakiltar manufar Ekiti kuma dole ne na ba shi goyon baya."
“Zan fara hamayyata bayan ya sake lashe zaɓen. Amma don wannan zaɓe mai zuwa, muna tare kuma muna ba shi goyon baya."

Kara karanta wannan

Dalilai 3 da za su iya sanya APC lashe zaben gwamnan Ekiti na 2026

- Ayodele Fayose

Kotu ta soke zaben fitar da gwanin PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a babban birnin Ado-Ekiti ta soke zaben fitar da gwanin gwamnan na PDP a jihar Ekiti.

Kotun ta soke zaben fitar da gwanin gwamnan jam’iyyar PDP mai adawa a jihar da ya haifar da tsaida Dr. Wole Oluyede.

An yanke hukuncin ne yayin sauraron karar da wani dan takarar gwamna, Funsho Ayeni, ya shigar kan PDP da hukumar INEC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng