Ana Tunkarar Zaben 2027, An Ji Matsalar da APC ke Fuskanta bayan Mutuwar Buhari
- Masana da 'yan siyasa sun ce zaben 2027 zai kasance karo na farko cikin kusan shekara 20 da APC za ta fafata ba tare da tasirin Buhari ba
- Wasu na ganin ayyukan Gwamna Dikko Radda za su taimaka wa APC, yayin da adawa ke cewa babu wanda zai iya maye gurbin Buhari
- Masana sun ce hadin kan APC da yadda jam'iyyun adawa za su shirya ne za su tantance sakamakon zaben Katsina a shekarar 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Katsina - Zaben shekarar 2027 zai zama karo na farko cikin kusan shekara 20 da jam’iyyar APC za ta shiga fafatawar siyasa a Katsina ba tare da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin babban jigon da ke jawo kuri’u ba.
Wannan ya haifar da tambayar ko jam’iyyar za ta iya ci gaba da rike jihar ta hanyar ayyukan gwamnati da tsarin jam’iyya kadai.

Source: Twitter
Tasirin rasuwar Buhari a siyasar Katsina
Tun kafin kafuwar APC a 2013, Buhari ya kasance jagoran siyasa mai farin jini a Katsina, inda yake samun gagarumin goyon baya a karkashin jam’iyyun ANPP, APP da CPC, cewar rahoton Daily Trust.
Shigarsa APC ta kara karfafa jam’iyyar a Arewa maso Yamma har ta kai ga samun nasarar shugaban kasa a 2015.
Masu goyon bayan APC sun ce yanzu nauyin tabbatar da wannan karfi ya rataya ne a wuyan Gwamna Dikko Umaru Radda.
Alhaji Mua’zu Bello ya ce gwamnatin Radda ta mayar da hankali kan tsaro, noma, ilimi, lafiya da ababen more rayuwa domin nuna wa jama’a cewa jam’iyyar na iya samun kuri’u bisa ayyukan da ta yi.
Sai dai Ibrahim Aminu Chiranchi na ADC ya ce rasuwar Buhari za ta sa masu kada kuri’a su daina bin siyasar mutum guda, su mayar da hankali kan batutuwan tsaro, tattalin arziki, aikin yi da walwalar jama’a.
Matsayar jam'iyyun adawa kan mulkin APC
Jam’iyyun adawa na kallon wannan a matsayin wata dama ta musamman wajen kalubalantar APC.
Masanin siyasa Umar Abdul Kurfi ya ce idan jam’iyyun adawa suka hada kai kuma suka kauce wa rikice-rikicen cikin gida, za su iya samun karin karbuwa musamman a yankunan da matsalar tsaro da talauci suka fi tsanani.
Shugaban jam’iyyar NDC a Katsina, Aliyu Ilu Barde, ya yi watsi da ra’ayin cewa nade-naden gwamnati da aka bai wa fitattun ‘yan siyasar jihar za su iya maye gurbin tasirin Buhari.
Ya ce irin wadannan mukamai ba za su iya samar wa APC irin farin jinin da Buhari ke da shi a tsakanin talakawa ba.
Rikice rikicen Gida a APCn Katsina
Har ila yau, wasu na ganin babban kalubalen APC ba daga adawa ba ne, illa rikice-rikicen cikin gida.
Hamisu Dauda ya ce yadda jam’iyyar za ta gudanar da zaben fidda gwani da sasanta masu neman mukamai zai taka muhimmiyar rawa wajen sakamakon zaben.

Source: Twitter
Duk da haka, APC na ci gaba da samun tagomashi saboda tana mulki, tana da ingantaccen tsarin jam’iyya a matakin kasa da jiha, tare da ayyukan gwamnatin Radda da ake ganin sun jawo hankalin wasu masu kada kuri’a.
Zarge zargen da ke kan gwamnatin APC
Sai dai mai fafutukar siyasa Abdulmuminu Shehu Sani ya yi zargin cewa gwamnatin APC ta gaza wajen magance matsalolin tsaro, ilimi da tattalin arziki, yayin da jam’iyyun adawa kuma ke fama da rikice-rikice.
Ya ce idan masu kada kuri’a suka kara wayewa kafin 2027, zaben na iya bude sabon babi a siyasar Katsina inda za a fi duba nagartar dan takara da ayyukan gwamnati fiye da dogaro da tasirin mutum guda.
Burin APC a Kano da Katsina
A wani labari, mun ruwaito cewa, shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya yi magana kan zaben 2027 da ke tafe da makomar jam'iyyarsu a wasu jihohin Arewa.
Farfesa Nentawe Yilwatda ya jaddada cewa APC na cigaba da samun karbuwa a jihohin Arewa musamman a yankunan Kano da Katsina.
Ya kuma sanar da cewa sauya shekar da 'yan siyasa ke yi zuwa jam'iyyarsu ba zai haifar da wata matsala ba, sabanin tunanin wasu mutane.
Asali: Legit.ng



