An Daure Dalibin Jami'ar Jos, an Masa Duka da Katako sai da Ya Mutu kan Waya
- An cafke mutum hudu da ake zargi da hannu a kisan Ibrahim Mbaye, dalibin Jami'ar Jos, bayan sun bayyana yadda suka azabtar da shi kan zargin satar waya
- Bidiyon yadda aka dinga dukansa da katakai da bulalai ya tayar da hankulan jama'a, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a fadin kasar nan
- Wadanda ake zargin sun amsa cewa sun lakada masa duka domin tilasta masa bayyana inda wayar da ake zargin ya sata take kafin daga bisani ya rasu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Plateau - Mutum hudu da ake zargi da hannu a kisan Ibrahim Mbaye, dalibin fannin Kimiyyar Siyasa na Jami'ar Jos (UniJos), sun bayyana yadda suka azabtar da shi har ya mutu.
Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi a wani gida da dalibai ke zama a bayan unguwar City of David da ke kan hanyar Ring a karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Plateau.

Kara karanta wannan
'Ba Abuja ba ne,' 'Yan sanda sun gano jihar da 'yan ta'adda suka kashe babban soja

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa bidiyon yadda aka azabtar da marigayin ya bazu a kafafen sada zumunta, lamarin da ya jawo fushin jama'a saboda tsananin dukan da aka yi masa.
Yadda aka kashe dalibi a Jos
Yayin da rundunar 'yan sandan jihar Plateau ta gabatar da su ga manema labarai, Emmanuel Newyear mai shekara 30 ya amince cewa ya shiga cikin dukan marigayin.
Ya ce da farko ya mari Ibrahim Mbaye a cikin daki kafin daga bisani ya fitar da shi waje inda ya bugi jikinsa da katako sau uku saboda yana zargin ya san inda wayar da ta bata take.
A cewarsa:
"Da farko na mare shi a cikin daki, daga baya na fito da shi waje. Ni ne na bugi jikinsa da katako sau uku saboda ina son ya fada mana inda wayar take."
Newyear ya kara da cewa marigayin ya ambaci wurare uku daban-daban da ya ce wayar tana ciki, amma bayan sun bincika ba su gano komai ba.

Source: Original
Bayani wasu da ake zargi
Wani da ake zargi mai suna Teslor Joshua ya amince cewa ya taimaka wajen rike Ibrahim Mbaye yayin da ake daure shi.
Shi ma mai wayar da ta bace, Rinji Daniel, ya ce marigayin ya kwana a dakinsa bayan sun dawo daga wani taro.
Daniel ya ce da misalin karfe 4:000 na asuba ya tashi ya tarar Ibrahim Mbaye baya cikin dakin, sannan ya gano wayarsa ta bata.
Ya ce bayan ya kira lambar wayarsa ba a dauka ba, daga bisani ya sanar da dan uwansa abin da ya faru, wanda daga nan ne aka fara zargin marigayin.
A nasa bangaren, Nensemka Fwanji, dan uwan Daniel, ya ce lokacin da ya dawo dakin ya tarar an yi wa Ibrahim Mbaye mugun duka.
Ya ce:
"Ni ne na kai shi asibiti bayan na ga irin munanan raunukan da ya samu."
A wani sako da ta wallafa a Facebook, kungiyar Amnesty International ta yi kira ga hukumomi su dauki mataki kan lamarin.
An yanke zakarin saurayi
A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kama wata mata mai shekara 25 bisa zargin yanke mazakutar saurayinta bayan ta gano yana shirin auren wata.
Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce lamarin ya faru ne a wani otel, inda ake zargin matar ta kai wa saurayin hari da wuka.
Kiyawa ya ce jami'an 'yan sanda sun kama matar tare da garzayawa da wanda aka ji wa rauni zuwa asibiti domin samun kulawa.
Asali: Legit.ng

