Jerin Gwamnonin Jihar Ekiti daga 1999 zuwa Yau yayin da Ake Shirin Sabon Zabe a 2026
A ranar Asabar mai zuwa, 20 da watan Yuni, 2026 ne za a gudanar da zaben gwamnan jihar Ekiti da ke yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Tuni dai hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta (INEC) ta fara aiwatar da shirye-shiryen gudanar da wannan zabe cikin lumana da bin ka'idojin da doka ta tanada.

Source: Facebook
Tashar Channels tv ta ruwaito cewa INEC ta fara rabon muhimman kayayyakin zabe ranar Alhamis, 18 ga watan Yuni, 2026 duk a wani bangare na ganin zaben ya gudana lafiya.
Sai dai yayin da shirye-shirye suka yi nisa, Legit.ng Hausa ta tattaro muku jerin gwamnonin da suka mulki jihar Ekiti tun daga dawowar mulkin dimokuradiyya a 1999 zuwa yau.
1. Otunba Niyi Adebayo
A rahoton da Gwamnatin Ekiti ga wallafa shafin yanar gizo, Niyi Adebayo ne gwamnan farar hula na farko da aka zaba a jihar bayan dawowar dimokuradiyya a Najeriya a shekarar 1999.
Adebayo ya karbi mulki a ranar 29 ga Mayu, 1999 bayan nasarar da ya samu karkashin inuwar jam'iyyar AD, kuma ya kammala wa’adinsa na shekaru hudu.

Source: Facebook
2. Ayodele Fayose
Ayo Fayose na jam'iyyar PDP ne ya zama gwamna na biyu da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya a Jihar Ekiti a ranar 29 ga Mayu, 2003.
Amma wa'adin mulkinsa ya kare kafin lokacinsa a ranar 16 ga Oktoba, 2006, sakamakon tsige shi da majalisar dokokin jihar ta yi saboda zargin aikata ba daidai ba, kamar yadda The Nation ta kawo.

Source: Facebook
Tsige Fayose da Majalisar Dokokin Jihar Ekiti ta yi a ranar 16 ga Oktoba, 2006, ya samo asali ne daga zargin yin sama-da-fadi da dukiyar gwamnati, kura-kurai wajen bada kwangiloli, da kuma hannu a tashe-tashen hankula na siyasa
3. Janar Tunji Olurin (Mai Ritaya)
Bayan ayyana dokar ta-baci a jihar Ekiti, tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya nada Birgediya Janar Tunji Olurin mai ritaya a matsayin mai gudanar da harkokin jihar.
Shugaba Obasanjo ya yi haka ne domin dawo da zaman lafiya da daidaito kafin gudanar da sabon zabe, inda shugaban rikon ya yi mulki daga ranr 19 ga Oktoba, 2006 zuwa 27 ga Afrilu, 2007.
4. Cif Tope Ademiluyi
Tope Ademiluyi ya karbi gudanar da harkokin jihar Ekiti a matsayin mukaddashin gwamna daga ranar 27 ga watan Afrilu, 2007 zuwa ranar 29 ga Mayu, 2007
Ya jagoranci harkokin jihar na wani dan gajeren lokaci kafin sabuwar gwamnatin da aka zaba ta karbi mulki.
5. Segun Oni
Segun Oni na jam'iyyar PDP ya hau mulkin jihar Ekiti bayan nasarar da ya samu a babban zaben 2007. Sai dai Kayode Fayemi ya kalubalanci sakamakon zaben a kotu.
A rahoton Vanguard, bayan shekaru uku ana shari’a, Kotun Daukaka Kara da ke Ilorin ta soke nasararsa a ranar 15 ga Oktoba, 2010, bayan ta gano kura-kurai da suka shafi gudanar da zaben.

Source: Facebook
6. Tunji Odeyemi
Bayan kotun daukaka kara ta sauke Segun Oni, Tunji Odeyemi ya karbi ragamar mulki a matsayin mukaddashin gwamna daga ranar 17 ga Fabrairu, 2009 zuwa 6 ga Mayu, 2009
Ya jagoranci harkokin gwamnatin Ekiti a lokacin sauyin mulki da ya biyo bayan hukuncin kotu da rigingimun siyasa.
7. Kayode Fayemi
Kayode Fayemi ya zama gwamna bayan hukuncin kotu ya tabbatar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi takaddama a kansa.
Fayemi ya kammala wa'di daya a kan mulki daga ranar 16 ga Oktoba, 2010 zuwa 16 ga Oktoba, 2014, inda ya sauka daga mulki bayan ya sha kaye a zaben Ekiti na 2014.

Source: Twitter
8. Ayo Fayose
Fayose ya dawo kan mulki karo na biyu bayan ya kayar da Fayemi a zaben gwamnan jihar Ekiti na shekarar 2014, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Nasarar da Fayose ya samu a karkashin inuwar PDP a shekarar 2014 a kan gwamna mai ci, Fayemi ta fuskanci ƙalubale a kotu amma an tabbatar da hakan.
9. Kayode Fayemi
Fayemi, wanda ya yi murabus daga kujerar ministan ma'adanai a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari, ya sake komawa kan mulki a jihar Ekiti a zaben gwamna na 2018.
Ya samu wannan nasara ne karkashin inuwar jam'iyyar APC mai mulki, inda ya gaji Fayose daga ranar 16 ga Oktoba, 2018 zuwa 16 ga Oktoba, 2022.

Kara karanta wannan
Bincike: 'Yan bindiga ne suka mika gawar Janar Rabe hannu da hannu? Gaskiya ta fito
9. Biodun Oyebanji
Gwamna Biodun Oyebanji na jam'iyyar APC shi ne Gwamnan jihar Ekiti mai ci, wanda ya gaji Kayode Fayemi bayan zaben da aka gudanar a shekarar 2022.
Daily Trust ta ce Oyebanji ya karbi mulki a ranar 16 ga watan Oktoba, 2022 karkashin inuwar APC kuma a halin yanzu yana daga cikin yan takarar da za su fafata a zaben ranar Asabar mai zuwa.

Source: Twitter
INEC ta yi alkawari kan zaben Ekiti
A wani labarin, kun ji cewa shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, Farfesa Joash Amupitan ya ce kuri’un masu zabe za su yi tasiri a zaben gwamnan jihar Ekiti.
Farfesa Amupitan ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar tantance shirye-shiryen zabe da ya kai jihar Ekiti tare da sauran kwamishinonin INEC gabanin zaben gwamna mai zuwa.
A cewarsa, cikin manyan ayyuka tara da hukumar INEC ta tsara domin zaben gwamnan Ekiti, an kammala guda bakwai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


