Jerry Adams: Mutumin da Uba Sani Ya Dauko Abokin Takara Ya Bayyana Matsayarsa
- Shugaban hukumar tara harajin cikin gida ta Kaduna, Jerry Adams, ya yi magana kan zama mataimakin Gwamna Uba Sani a zaben 2027
- Nadin Jerry Adams ya kawo karshen shekaru bakwai da APC ta daina tsayar da Kirista a matsayin dan takarar mataimakin gwamna a Kaduna
- Jerry Adams ya ce zai yi aiki tare da Uba Sani wajen gina jihar Kaduna mai zaman lafiya, wadata da adalci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Shugaban hukumar tara harajin cikin gida ta jihar Kaduna (KADIRS), Jerry Adams, ya amince da zama abokin takarar Gwamna Uba Sani a zaben gwamnan jihar na 2027.
Gwamna Uba Sani ya bayyana Adams a matsayin wanda zai yi takarar mataimakin gwamna tare da shi a ranar Talata, 28 ga watan Yulin 2026.

Source: Twitter
A wata sanarwa da Adams ya fitar a ranar Laraba, 28 ga watan Yulin 2026 a shafinsa n. Facebook, shugaban na KADIRS ya ce tun bayan sanar da nadinsa a matsayin dan takarar mataimakin gwamna, ya samu sakonnin taya murna, ziyara da addu’o’i masu yawa.
APC ta sauya tsari a Kaduna
Nadin Adams shi ne karo na farko cikin shekaru bakwai da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta tsayar da Kirista a matsayin dan takarar mataimakin gwamna a jihar Kaduna.
Hakan ya nuna sauyi daga tsarin tikitin Musulmi da Musulmi da jam’iyyar ta yi amfani da shi a zabukan gwamnan jihar na 2019 da 2023.
Adams ya karbi nadin
Adams ya ce zai yi aiki tare da Gwamna Uba Sani, tare da taimakon Allah, domin gina jihar Kaduna mai zaman lafiya, wadata da adalci ga kowane dan jihar.
“Cike da godiya a zuciyata, na amince da wannan nadi na zama abokin takarar Mai Girma Sanata Uba Sani, CON, gwamnan jihar Kaduna, a babban zaben 2027."
“Tun bayan sanar da nadin, na cika da matukar farin ciki. Kira, sakonni, ziyara da addu’o’in da na samu sun zo a yalwace daga kowane bangare na jihar Kaduna da ma wasu wurare."
“A gaskiya, na yi kokarin samun kalmomin da zan amsa ko kadan daga cikin sakonnin, amma abin ya gagare ni."
“Ga duk wanda ya tuntube ni, iyali, abokai da kuma wadanda ba mu san juna ba amma yanzu sun zama kamar iyali, ina rokon ku gafara idan ban amsa wa kowa daban-daban ba."
“Ku sani cewa kowane sako ya taba zuciyata, ko da kuwa bai kai ga wayata ba tukuna.”
- Jerry Adams

Source: Facebook
Adams ya gode wa Uba Sani
Adams ya ce bai dauki wannan lokaci da wasa ba, yana mai bayyana nadin a matsayin wata alamar amincewa da aka yi da shi.
Ya ce Gwamna Uba Sani ya nuna jajircewa wajen tabbatar da adalci, daidaito da bai wa kowa dama tun bayan rantsar da shi a watan Mayun 2023.
“Mai girma gwamna, na gode da ka ga wani abu a tare da ni da ya sa ka ga na dace a damka min wannan nauyi. Ina addu’a kullum Allah ya ba ni ikon sauke wannan nauyi yadda ya kamata.”
- Jerry Adams
An bukaci Isa Ashiru ya sauya abokin takara
A wani labarin kuma, kun ji cewa masu ruwa da tsaki na jam'iyyar ADC a Kudancin Kaduna sun yi gargadi bayan nada dan takarar mataimakin gwamna.
Masu ruwa da tsakin sun bukaci dan takarar gwamnan Kaduna, Isa Ashiru, da ya dakatar da nada Barrista Emmanuel Kantyok a matsayin mataimakin takara domin zaben 2027.
Asali: Legit.ng


