Amurka Ta Kashe Mata da Miji da Yaro Dan Shekara 2 a Iran, Wasu Yara Sun Jikkata

Amurka Ta Kashe Mata da Miji da Yaro Dan Shekara 2 a Iran, Wasu Yara Sun Jikkata

  • Hukumomin Iran sun ce mutane uku 'yan gida daya sun mutu bayan harin da sojojin Amurka suka kai kan wani gida a tsibirin Qeshm da ke Kudancin kasar
  • Rundunar sojin Amurka ta ce ta kai hare-haren ne a matsayin martani ga yunkurin harba makamai masu linzami kan dakarunta da ke Gabas ta Tsakiya
  • A lokaci guda, dakarun kare juyin juya halin Iran sun ce wasu tankokin dakon mai guda biyu sun janye daga mashigin Hormuz bayan daya daga cikinsu ya kama da wuta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Tehran, Iran – Hukumomin Iran sun sanar da mutuwar mutane uku bayan wani hari da sojojin Amurka suka kai kan wani gida da ke unguwar Chah Tangu a tsibirin Qeshm da ke Kudancin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Iran ya ruwaito cewa wadanda suka mutu sun hada da uba, uwa da daya daga cikin 'ya'yansu, yayin da wasu yara biyu na gidan suka samu raunuka kuma aka garzaya da su asibiti domin kula da lafiyarsu.

Kara karanta wannan

Amurka ta sanar da kammala zagayen manyan hare hare a Iran

Jirgin yakin Amurka a sama
Yadda wani jirgin yaki ke tafiya a sama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton Anadolu ya ce mataimakin gwamnan lardin Hormozgan, Ahmad Nafisi, ya tabbatar da cewa an kammala aikin ceton da aka kaddamar.

Karin bayani daga Iran

Haka kuma, wasu kafafen yada labaran Iran sun ruwaito cewa hare-haren sun shafi wasu wurare da ke kusa da tsibirin Qeshm da kuma birnin Abadan.

A cewar Ahmad Nafisi:

"Da misalin karfe 4:00 na asuba ne sojojin makiya na Amurka suka kai hari kan wani wuri da ke kusa da tsibirin Qeshm."

Hakazalika, kamfanin dillancin labarai na Fars ya ce mataimakin gwamnan Khuzestan ya tabbatar da cewa an kai hare-haren makamai masu linzami a wasu wurare da ke kusa da birnin Abadan.

Shugaba Donald Trump
Donald Trump a wajen wani taro a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Iran ta kai farmaki Hormuz

A wani labarnin kuma, Dakarun Kare Juyin Juya Halin Iran (IRGC) sun bayyana cewa wasu tankokin dakon mai guda biyu sun yi yunkurin bi ta mashigin Hormuz tare da goyon bayan Amurka.

Sai dai sun ce bayan daya daga cikin jiragen ya kama da wuta, dukkansu sun janye ba tare da ci gaba da tafiya ba.

Kara karanta wannan

Yadda aka shirya amfani da Boko Haram, JTF domin kifar da gwamnatin Tinubu

Roya News ta rahoto sanarwar ta ce:

"A daren jiya wasu tankokin dakon mai guda biyu, da jiragen saman Amurka suka karfafa musu gwiwa, sun yi yunkurin wucewa ta hanyar kudancin mashigin
"Hormuz. Bayan da daya daga cikinsu ya kama da wuta sosai, dukkansu suka yi gaggawar juyawa."

An farmaki tankar Amurka

A wani labarin, mun ruwaito cewa wata tankar ajiyar iskar gas mallakin wani kamfanin Amurka ta kama da wuta a tashar jiragen ruwa ta Damietta da ke gabar tekun Bahar Rum a kasar Masar.

Kamfanin Ambrey mai sa ido kan tsaron teku ya bayyana cewa akwai yiwuwar wani jirgi mara matuki ne ya kai harin, duk da cewa ma'aikatar man fetur ta Masar ba ta tabbatar da hakan ba.

Lamarin ya kara tayar da hankalin kasashen duniya kan yiwuwar yakin da ke tsakanin Iran da Amurka ya kara fadada zuwa wasu sassan Gabas ta Tsakiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng