An Taso Dan Takarar Gwamnan Kaduna a Gaba kan Zaben Mataimakinsa, Ya Kira Ruwa

An Taso Dan Takarar Gwamnan Kaduna a Gaba kan Zaben Mataimakinsa, Ya Kira Ruwa

  • Masu ruwa da tsaki na ADC a Kudancin Kaduna sun yi gargadi game da daukar dan takarar mataimakin gwamna
  • Sun bukaci Isa Ashiru ya dakatar da nada mataimakin takararsa har sai kwamitin NWC ya yanke hukunci kan rikicin tikitin gwamna
  • Mutanen jam'iyyar suka ce nada Barrista Emmanuel Kantyok kafin warware rikicin tikitin gwamna zai iya kara raba kan jam'iyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Masu ruwa da tsaki na jam'iyyar ADC a Kudancin Kaduna sun yi gargadi bayan nada dan takarar mataimakin gwamna.

Masu ruwa da tsakin sun bukaci dan takarar gwamnan Kaduna, Isa Ashiru, da ya dakatar da nada Barrista Emmanuel Kantyok a matsayin mataimakin takara domin zaben 2027.

An gargadi zabin dan takarar mataimakin gwamnan Kaduna
Dan takarar gwamnan Kaduna a ADC, Ashiru Kudan da mataimakinsa, Emmanuel Kantyok. Hoto: Isa Ashiru Kudan.
Source: Facebook

Sun bayyana hakan ne yayin taron manema labarai da aka gudanar a Kafanchan da ke karamar hukumar Jema'a, inda suka ce ya dace a jira Kwamitin Ayyuka na Kasa (NWC) ya yanke hukunci kan rikicin tikitin gwamna, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

An bayyana babban abin da ya haddasa ayyukan daba a jihar Kano

An gargadi Ashiru Kudan kan zaben mataimakinsa

Masu ruwa da tsakin sun gargadi cewa nada mataimakin takara kafin a warware rikicin tikitin gwamna na iya kara tsananta rikicin cikin jam'iyyar tare da raunana hadin kai kafin babban zaben 2027.

Mai magana da yawun kungiyar, Solomon Chindo, ya ce takaddamar ta samo asali ne bayan zaben fidda gwani na gwamna, inda aka samu sabani kan wanda ya lashe zaben.

Ya ce dakatar da nada mataimakin takara har sai NWC ta bayyana halastaccen dan takara zai tabbatar da adalci, karfafa dimokuradiyyar cikin gida da kuma hada kan jam'iyyar.

Rikici zai iya dawowa a jam'iyyar ADC a Kaduna
Dan takarar gwamnan Kaduna karkashin ADC, Isa Ashiru Kudan. Hoto: Isa Ashiru Kudan.
Source: Facebook

'Wanda ya lashe zaben fitar da gwani'

Chindo ya bayyana cewa Isa Ashiru ne aka fara ayyana a matsayin wanda ya lashe zaben fitar da gwani, amma Kwamitin Daukaka Kara ya soke sakamakon bayan gano zargin kura-kurai da suka shafi sahihanci da gaskiyar zaben.

A cewarsa, kwamitin ya ayyana Shua'aibu Miqati a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaben, lamarin da ya sa duka bangarorin biyu ke ikirarin mallakar tikitin gwamnan jam'iyyar, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

"Dole mu yi nasara," APC ta dauki babban mataki kan zaben gwamnan jihar Osun

Shi ma Isiyaka Zango ya yabawa Kwamitin Daukaka Kara bisa abin da ya kira sahihin bincike mai cike da gaskiya, tare da rokon mambobin ADC su kwantar da hankalinsu suna jiran hukuncin NEC da sauran hukumomin jam'iyyar.

Masu ruwa da tsakin sun ce bisa hukuncin kwamitin daukaka kara, Shua'aibu Miqati ne halastaccen wanda ya lashe zaben fidda gwani har sai wata hukuma mai iko ta yanke akasin haka.

Sun kuma nuna damuwa kan matsalolin tsaro, hauhawar farashin kayayyaki, rashin aikin yi da tsadar rayuwa, suna cewa wadannan kalubale na ci gaba da jefa 'yan Najeriya, musamman masu rauni, cikin mawuyacin hali.

An kawo karshen rikicin ADC a Kaduna

An ji cewa jam'iyyar adawa ta ADC reshen jihar Kaduna ta yi nasarar hade kan 'ya'yanta wuri guda yayin da babban zaben 2027 ke kara matsowa a Najeriya.

An samu cimma matsaya ne bayan Isa Ashiru, 'dan takarar gwamna a jihar ya zauna da dukkanin bangarorin da ke adawa da juna tare da jin matsalar su.

Bayan zaman, shugabannin sun amince da zubar da makamin, sannan an kuma fara ɗaukar matakan warware sauran shari'un da suka shafi rikicin shugabanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.