Gwamna Ya Dora Alhaki kan APC bayan 'Yan Daba Sun Harbi Babban Basarake
- Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya yi zargi kan jam'iyyar APC mai adawa a jihar dangane da harin da aka kaiwa wani babban basarake
- Ademola Adeleke ya zargi jam'iyyar APC da tura 'yan daban da suka harbi Ataoja na Osogbo, Oba Jimoh Olanipekun Larooye II
- Gwamnan ya kalubalanci sakataren jam'iyyar APC na kasa, Ajibola Basiru, da ya fito ya yi magana kan harin da aka kaiwa basaraken
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Osun - Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya ce wasu 'yan daba sun harbi Oba Jimoh Olanipekun Larooye II, wato Ataoja na Osogbo.
Gwamna Adeleke ya bayyana cewa 'yan daban sun harbi babban basaraken ne a lokacin da suka farmaki fadarsa kwanan nan.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a cikin wani sako da Gwamna Adeleke ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, 13 ga watan Yunin 2026.
Gwamna Adeleke ya yi zargi kan APC
Gwamna Ademola Adeleke ya yi zargin cewa jam'iyyar APC ce ta ɗauki nauyin 'yan daban da suka kai harin.
Ya ce an farmaki Ataoja ne saboda ya fito fili ya goyi bayansa domin yin tazarce a wa'adi na biyu a kan mulki, matakin da ya yi iƙirarin bai yi wa shugabannin APC na jihar Osun daɗi ba.
“Ataoja na Osogbo, ɗaya daga cikin sarakunan gargajiya da ake girmamawa a Najeriya, ya ce 'yan daban APC sun harbe shi a cikin fadarsa kunkum. Harsashi ya samu talakawansa. Kabiyesi da kansa aka kawowa harin."
“Me yasa? Saboda ya tsaya tsayin daka da mutanensa. Saboda ya zaɓi kyakkyawan shugabanci a kan dabanci. Duk da haka Kabiyesi ya tsaya da girmansa sannan ya bayyana cewa: ‘Osogbo tana tare da Imole’.”
- Gwamna Ademola Adeleke
Adeleke ya kalubalanci sakataren APC
Gwamna Ademola Adeleke ya kuma buƙaci Ajibola Bashiru, sakataren jam'iyyar APC na ƙasa, wanda ya bayyana shi da ɗan asalin birnin Osogbo, da ya yi magana kan wannan lamari.

Kara karanta wannan
"Muna da mutane," APC ta hango nasara a jihar Ekiti da zaben shugaban kasa a 2027

Source: Facebook
“APC ta jihar Osun ta wuce gona da iri, kuma ina ƙalubalantar sakataren APC na kasa kai tsaye, wanda ɗan Osogbo ne, da ya tsawatar wa mambobin jam'iyyarsa."
“Me yasa suka tura 'yan daba zuwa fadar mahaifarka? Me yasa suka wulakanta masarautar da ta yi renonka?"
“Jam'iyyarka ce ta aikata wannan. Basarakenka na gargajiya shi ne aka farmaka. Osogbonka tana zubar da jini. Yin shiru zaɓi ne. Ka yi naka zabin cikin hikima.”
- Gwamna Ademola Adeleke
Gwamna Adeleke ya tube rawanin basarake
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya amince da tube rawanin Oba Joseph Oloyede daga matsayin Apetumodu na Ipetumodu.
Matakin da Gwamna Adeleke ya dauka, ya biyo bayan samun Oloyede da laifi da aka yi a ƙasar Amurka kan zargin damfara ta haraji da kuma halasta kuɗaɗen haram.
Gwamnan ya nuna cewa halayyar da tsohon basaraken ya nuna ta rashin gaskiya ta zubar da kima da darajar masarautar a idon duniya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
