Amurka Ta Sanar da Kammala Zagayen Manyan Hare Hare a Iran
- Amurka ta ce ta kai manyan hare haren sama kan wurare da dama na sojin Daular Musulunci ta Iran
- CENTCOM ta ce an lalata cibiyoyin umarni, wuraren makamai masu linzami da wasu manyan kayan aiki
- Ta kuma ce sama da sojojin Amurka 50,000 da ke yankin na ci gaba da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana na kai hare-hare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
USA – Rundunar sojin Amurka da ke kula da yankin Gabas ta Tsakiya, wato CENTCOM, ta bayyana cewa ta kammala wani "babban jerin hare-haren sama" da ta kai kan Iran.
A cewar ta, wannan martani ne ga yunkurin harba makamai masu linzami da aka yi jiya kan dakarun Amurka da ke Jordan.

Source: Getty Images
Al-Jazeera ta wallafa cewa a cikin wata sanarwa, CENTCOM ta ce jiragen yakinta sun kai hare hare kan wurare da dama na rundunar Revolutionary Guard ta Iran.
Amurka ta kuma kai hari Iran
Anadolu Ajansi ta kawo labarin cewa CENTOM ta ce hare-haren sun shafi cibiyoyin umarnin soja, wuraren adana da harba makamai masu linzami.
Haka kuma an farmaki sansanonin jiragen yaki marasa matuƙa, cibiyoyin sa ido da kariyar gabar teku, da kuma ƙarfin sojojin ruwan Iran.
CENTOM ta kara da bayyana manufar hare-haren a lokacin da ake ƙoƙarin dawowa kan teburin sulhu tsakaninta da Iran a Gabas ta Tsakiya.
Manufar harin Amurka a Iran
CENTCOM ta bayyana cewa manufar hare haren ita ce ƙara rage barazanar da Iran da ƙawayenta ke haifarwa ga dakarun Amurka.
Haka kuma tana son kare jiragen kasuwanci da ke zirga zirga a teku, da kuma ƙasashen yankin Tekun Fasha a Gaban ta Tsakiya.
Har ila yau, rundunar ta ce sama da sojojin Amurka 50,000 da ke aiki a yankin suna ci gaba da kasancewa cikin cikakken shirin ko-ta-kwana, tare da kasancewa cikin shiri don kare muradun ƙasarsu da ƙawayenta.

Source: Getty Images
Wadannan hare-hare sun zo ne a lokacin da yaƙin ke neman daukan zafi bayan Saudiyya ta zargi Iran ta kai mata hari.
Amma Iran ta ƙaryata cewa ta kai harin ko ta na da alaƙa da waɗanda suka farmaki muhimmanci wurare da kadarorin Amurka a ƙasa Saudiyya.
Duk da haka, Amurka da Iran sun haɗa kai inda suka kai manyan hare-hare a muhimman wurare a Iran.
Iran ta taso Saudiyya a gaba
A baya, mun kawo labarin cewa Saudiyya ta fara kai farmaki tare da Amurka kan ƙawayen Iran a Iraki bayan zargin su da kai hare-haren jiragen sama marasa matuki.
Yarima Mohammed bin Salman na kokarin kare shirin Vision 2030 saboda rikicin Gabas ta Tsakiya na barazana ga zuba jari da muhimman cibiyoyin tattalin arziki.
Hare-haren da aka kai kan cibiyoyin man fetur na Saudiyya sun nuna irin barazanar da jiragen sama marasa matuki da makamai masu linzami ke haifarwa.
Asali: Legit.ng

