Zaben Ekiti: Yadda Gwamna Biodun Oyebanji Ya Samu Tazarce a Inuwar Jam'iyyar APC

Zaben Ekiti: Yadda Gwamna Biodun Oyebanji Ya Samu Tazarce a Inuwar Jam'iyyar APC

Ekiti – Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ayyana Gwamna Biodun Oyebanji, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Ekiti da aka gudanar ranar Asabar, 20 ga Yunin 2026.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jami’ar tattara sakamakon zabe, Adenike Oladiji, ce ta sanar da sakamakon da misalin karfe 3:13 na asubahin Lahadi, inda ta bayyana cewa Oyebanji na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 319,224.

Gwamna Biodun Oyebanji ya lashe zaben gwamnan jihar Ekiti
Gwamna Biodun Oyebanji yana kada kuri'arsa a zaben gwamnan Ekiti da aka gudanar ranar Asabar. Hoto: @biodunaoyebanji
Source: Twitter

Yadda Oyebanji ya samu tazarce a Ekiti

Da wannan nasarar, gwamnan ya samu damar komawa karo na biyu a ofis, bayan ya doke manyan abokan hamayyarsa daga jam’iyyun adawa, a cewar rahoton BBC.

A wannan rahoto, Legit Hausa ta duba yadda Gwamna Biodun Oyebanji ya samu tazarce, ya kafa tarihi a siyasar jihar Ekiti:

Kara karanta wannan

2026: Tinubu ya yi martani da dan takarar APC ya lashe zaben gwamnan jihar Ekiti

1. Lashe dukkan kananan hukumomi

Gwamna Oyebanji ya samu gagarumar nasara inda ya lashe dukkan kananan hukumomi 16 na jihar Ekiti, abin da ya hana jam’iyyun adawa samun wata kafa mai karfi a yankunan jihar.

A zaben da ‘yan takara 14 suka fafata, dan takarar APC ya samu tazarar kuri’u mai yawa tsakaninsa da na biyu a zaben.

Dan takarar jam’iyyar PDP, Wole Oluyede, ya samu kuri’u 40,543, yayin da dan takarar ADC ya samu kuri’u 12,872 kacal a zaben.

Daga babban birnin jihar, Ado Ekiti, zuwa kananan hukumomi na karkara kamar Moba da Ekiti East, Oyebanji ya samu rinjaye mai yawa.

2. Wuraren da APC ta samu kuri’u masu yawa

Daya daga cikin wuraren da APC ta fi karfi shi ne Ado Ekiti, inda Oyebanji ya samu kuri’u 38,026, kusan ninki 10 na kuri’un PDP da suka kai 3,817.

Sauran wuraren da gwamnan ya samu kuri’u masu yawa sun hada da:

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Ekiti: APC ta aika sako ga Oyebanji bayan samun tazarce

  • Irepodun/Ifelodun – kuri’u 29,278
  • Ekiti West – kuri’u 28,258
  • Ikole – kuri’u 26,508
  • Ekiti East – kuri’u 26,359
  • Ijero – kuri’u 25,506
  • Moba – kuri’u 20,500
  • Aiyekire – kuri’u 17,133

A dunkule, adadin masu rajistar zabe ya kai 988,251, yayin da wadanda aka tantance suka kada kuri’a suka kai 383,940.

Sakamakon karshe ya kasance:

  • APC – kuri'u 319,224
  • PDP – kuri'u 40,543
  • ADC – kuri'u 12,872
  • ADP – kuri'u 1,269
  • LP – kuri'u 276

Duk da yadda APC ta mamaye jihar, karamar hukumar Ikere, wadda dan takarar PDP Wole Oluyede ya fito daga cikinta, ita ce wurin da aka samu gagarumar fafatawa.

A can ne tazarar kuri’u tsakanin APC da PDP ta fi kusa, inda bambancin ya kasance kuri’u 1,224 kacal, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Gwamna Biodun Oyebanji na APC ya lashe zaben jihar Ekiti da kuri'u masu yawa.
Daruruwan masu kada kuri'a a rumfar da Gwmamna Biodun Oyebanji yake zabe a jihar Ekiti. Hoto: @biodunaoyebanji
Source: Twitter

3. Sauran abubuwan da suka taimaka wa Oyebanji

Daga yadda sakamakon ya kasance, akwai manyan abubuwa uku da suka fito fili:

  • Na farko, Oyebanji ya lashe dukkan kananan hukumomi 16, abin da ya hana jam’iyyun adawa samun wani yanki da za su dogara da shi.
  • Na biyu, APC ta samu kuri’u masu yawa a manyan cibiyoyin zabe kamar Ado Ekiti, Irepodun/Ifelodun da Ekiti ta Yamma.
  • Na uku, kuri’un adawa sun watse a fadin jihar, inda PDP ta rasa samun damar samun rinjaye a mafi yawan wurare.

Kara karanta wannan

Cikakken sakamakon zaben gwamnan Ekiti kamar yadda INEC ta sanar

Bisa ga tazarar sama da kuri’u 278,000 da ke tsakanin Oyebanji da babban abokin hamayyarsa, sakamakon ya nuna cewa APC ta lashe zaben cikin ruwan sanyi.

Korafe-korafen sayen kuri’u

Duk da cewa INEC ta bayyana zaben a matsayin wanda aka gudanar cikin kwanciyar hankali, wasu masu sa ido sun nuna cewa an samu wasu matsaloli da suka hada da rashin daidaito a wasu kayan zabe da kuma rahotannin sayen kuri’u a wasu wurare.

Rahoton Punch dai ya nuna cewa an fara kada kuri’a da karfe 8:30 na safe a rumfunan zabe 2,445 da ke jihar a zaben na ranar Asabar.

Gwamna Biodun Oyebanji ya godewa 'yan Ekiti da suka sake zabensa a matsayin gwamna.
Gwamna Biodun Oyebanji tare da uwargidansa a lokacin da yaje kada kuri'a a zaben gwamnan Ekiti. Hoto: @biodunaoyebanji
Source: Twitter

Bayan kammala kada kuri’a, an tattara sakamakon rumfuna zuwa unguwanni 177 kafin a kai ga tattara sakamakon kananan hukumomi 16.

Ekiti na da masu rajistar zabe fiye da miliyan daya, amma wadanda suka samu katin zabe ne suka cancanci shiga zaben, inda adadin wadanda suka kada kuri’a bai kai rabin wadanda suke da katin ba.

APC ta aika sako ga Oyebanji

A wani labari, mun ruwaito cewa, jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta aika da sakon taya murna ga gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji.

Kara karanta wannan

Zaben cike gurbi: APC ta ci gaba da karfafa ikonta bayan nasara a Kano

Jam'iyyar APC ta taya Biodun Oyebanji murnar nasarar da ya samu a zaben gwamnan jihar Ekiti na ranar Asabar, 20 ga watan Yunin 2026.

Jam'iyyar APC ta bayyana cewa nasarar Biodun Oyebanji cike take da tarihi, domin ya zama gwamnan farko da ya yi tazarce a jihar Ekiti.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com