2026: Manyan Abubuwa 3 da Za Su iya Kawo wa APC Cikas a Zaben Gwamnan Ekiti
Ekiti – Idan ranar Asabar, 20 ga Yunin 2026 ta zo, hankulan ‘yan Najeriya za su karkata zuwa jihar Ekiti yayin da masu kada kuri’a za su je rumfunan zabe domin zabar wanda zai jagoranci jihar na tsawon shekaru hudu masu zuwa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Zaben na zuwa ne a wani lokaci da ake ganin zai kasance gwaji ga jam’iyyar APC, wadda ke kokarin ci gaba da rike mulki a jihar.

Source: Twitter
Zaben jihar Ekiti na 2026
Babban abin da ake jira a gani shi ne ko masu kada kuri’a za su zabi ci gaba da gwamnatin da ake ciki ko kuma su nemi sabon shugabanci, kamar yadda rahoton BBC ya nuna.
Gwamnan jihar Ekiti mai ci, Biodun Oyebanji, ya hau mulki ne a ranar 16 ga Oktoban 2022 karkashin tutar APC, kuma yanzu yana neman damar komawa wa’adi na biyu.

Kara karanta wannan
Jerin gwamnonin jihar Ekiti daga 1999 zuwa yau yayin da ake shirin sabon zabe a 2026
Tambayar da ta ke gaban masu lura da harkokin siyasa ita ce: Shin al’ummar Ekiti za su sake bai wa gwamnan dama saboda ayyukan da yake ikirarin ya gudanar, ko kuwa za su sauya alkiblar siyasar jihar?
Abubuwan da za su iya jawo faduwar APC
A wannan rahoto, Legit.ng ta duba abubuwa uku da ka iya kawo wa APC cikas a zaben gwamna na Ekiti 2026.
1. Gajiya da mulkin APC
Daya daga cikin manyan kalubalen da APC za ta iya fuskanta shi ne batun gajiya da mulki.
Jam’iyyar ta kasance a kan mulki a jihar Ekiti tun shekarar 2018, lamarin da wasu masu nazarin siyasa ke ganin zai iya sa wasu masu kada kuri’a su fara neman sauyi.
A wasu lokutan, masu zabe kan nuna bukatar sabon salo idan suka ji cewa jam’iyyar da ke mulki ta dade ba tare da sauya shugabanci ba.
Masana sun ce akwai yiwuwar wasu jama’a su kalli gwamnatin APC a matsayin wadda ta samu damar yin aiki na dogon lokaci, amma yanzu suna son ganin lokaci ya yi da za su zabi wani sabon jagora.
Yadda masu kada kuri’a za su tantance ayyukan gwamnatin Oyebanji da kuma bukatarsu ta sauyi na iya zama babban abin da zai tsara sakamakon zaben.
2. Batun wakilcin addini
Wani batu da ka iya taka rawa a zaben shi ne batun wakilcin addini.

Source: Twitter
Tun bayan dawowar mulkin dimokuradiyya a Najeriya a shekarar 1999, jihar Ekiti ba ta taba samun gwamna Musulmi da aka zaba ta hanyar kuri’ar jama’a ba.
Wasu masu bibiyar siyasa na ganin cewa wannan na iya zama wani batu da zai shafi ra’ayoyin wasu masu kada kuri’a, musamman wadanda ke ganin akwai bukatar a samu karin daidaito wajen wakilci.
Ko da yake, wata sanarwa da aka wallafa a shafin gwamnatin Ekiti ta nuna cewa al'ummar Musulmi na Ekiti sun fito sun nuna goyon baya ga Gwamna Oyebanji, wanda ake ganin ba lallai addini ya yi tasiri a zaben ba.
3. Matsin tattalin arziki
Matsalar tattalin arziki na daga cikin manyan kalubalen da jam’iyyun da ke mulki ke fuskanta a Najeriya a halin yanzu.
Karin farashin kayayyaki, hauhawar farashi da tsadar rayuwa na daga cikin abubuwan da suka janyo damuwa ga al’umma, in ji rahoton The Nation.
Duk da cewa gwamnatin APC ta ce sauye-sauyen da take aiwatarwa za su taimaka wajen samun ci gaba na dogon lokaci, masu nazarin siyasa sun bayyana tattalin arziki da tsaro a matsayin manyan wuraren da gwamnatocin da ke mulki ke fuskantar matsin lamba.
Maganar Tinubu kan tsadar rayuwa

Source: Twitter
Legit.ng ta ruwaito cewa a jawabin Ranar Dimokuradiyya ta 2026 ranar Juma’a, 12 ga Yuni, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince cewa har yanzu ‘yan Najeriya da dama na fuskantar matsin tattalin arziki duk da matakan da gwamnatinsa ke dauka.
Tinubu ya ce:
“Duk da matakan da aka dauka, har yanzu ‘yan Najeriya da dama suna fuskantar matsin tattalin arziki. Muna ci gaba da mayar da hankali wajen rage hauhawar farashi, kara samar da abinci, samar da ayyukan yi, inganta rayuwa da dawo da kwarin gwiwa ga tattalin arzikinmu.”
Tasirin halin da ake ciki ga APC
Wasu masu kada kuri’a a Ekiti na iya amfani da zaben wajen nuna ra’ayinsu kan yadda suke kallon yanayin tattalin arziki a kasa.
Gwamna Oyebanji da Shugaba Tinubu na da alaka ta siyasa, kuma yadda jama’a ke kallon manufofin gwamnatin tarayya na iya yin tasiri ga yadda za su kada kuri’a a zaben jihar.
Duk da wadannan kalubale, APC na dogaro da ayyukan gwamnatin Oyebanji da goyon bayan jam’iyya wajen neman ci gaba da mulki a Ekiti.
Za a shawo kan talaka da shinkafa
A wani labari, mun ruwaito cewa, hukumar zabe ta kasa (INEC) ta yi magana game da shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnan jihar Ekiti da za a yi a 2026.
Kungiyar Yiaga mai saka ido a kan harkokin zabe ta yi zargin cewa wasu 'yan siyasa sun fara shirye-shiryen raba shinkafa da taliya ga masu zabe don su zabe su.
Wannan na zuwa ne bayan shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan ya bayyana cewa an samu karin masu kada kuri'a fiye da yadda aka samu a jihar a zaben 2023.
Asali: Legit.ng


