Wata Sabuwa: INEC Ta Fasa Gudanar da Zaben Gwamnan Osun a Ranar 8 ga Agusta
- Hukumar INEC ta sanar da sauya ranar kammala yaƙin neman zaɓen gwamnan Osun bayan matsar da ranar babban zaɓen jihar
- Sabuwar dokar zaɓe ta shekarar 2026 ta tanadi cewa dole ne a dakatar da dukkan yakin neman zabe sa'o'i 24 kafin fara zabe
- Hukumar ta buƙaci dukkan jam'iyyun siyasa da ƴan takara da su bi wannan sabon tsarin domin tabbatar da yin zaɓe na gaskiya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja – Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanar da sauye-sauye a jadawalin yaƙin neman zaɓen gwamnan jihar Osun mai zuwa.
Wannan mataki ya biyo bayan ɗan takaitaccen sauyi da aka samu a ranar gudanar da zaɓen kanta, kamar yadda hukumar ta bayyana a ranar Alhamis, 16 ga Afrilu, 2026.

Source: Twitter
INEC ta canza ranar zaben gwamnan Osun
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da ilimantar da masu zaɓe na ƙasa, Mohammed Haruna, ya sanya wa hannu, in ji rahoton Daily Trust.
A cikin sanarwar Mohammed Haruna, hukumar INEC ta tunatar da jama'a cewa an riga an ɗan matsa da ranar zaɓen jihar ta Osun da mako guda.
Tun farko dai INEC ta sanar a watan Fabrairu cewa za a gudanar da zaɓen ne a ranar 15 ga watan Agusta maimakon ranar 8 ga watan yadda aka tsara da farko.
Dalilin sauya jadawalin zaben gwamna a Osun
INEC ta bayyana cewa wannan sauyi ya zama dole ne domin yin daidai da tanadin sabuwar dokar zaɓe ta shekarar 2026.
Dokar ta tanadi cewa dole ne kowane ɗan takara ko jam'iyyar siyasa su dakatar da kowane irin yaƙin neman zaɓe sa'o'i 24 kafin fara zaɓen kansa.
A sakamakon haka, INEC ta sanar da cewa ranar ƙarshe ta yaƙin neman zaɓe a jihar Osun yanzu ita ce tsakar daren ranar Alhamis, 13 ga watan Agusta, 2026.
Wannan ya yi daidai da sashe na 98 (1) na sabuwar dokar zaɓen ƙasar nan. Hukumar ta buƙaci dukkan masu ruwa da tsaki su kiyaye wannan rana domin guje wa fuskantar hukunci.

Source: Getty Images
Alƙawarin INEC kan ingancin zaɓe
Hukumar zaɓen ta ƙara jaddada aniyarta na tabbatar da ganin an gudanar da zaɓe cikin adalci da gaskiya ba tare da nuna son kai ba, in ji rahoton Punch.
INEC ta bayyana cewa tana yin duk abin da ya dace domin ganin an samar da yanayi mai kyau ga masu kaɗa ƙuri'a da kuma ƴan takara a faɗin ƙasar nan.
Hukumar ta kuma yi kira ga jam'iyyun siyasa da su rika wayar wa magoya bayansu kai game da muhimmancin bin dokokin zaɓe.
Osun ta fi Kano a yawan rajistar katin zabe
A wani labari, mun ruwaito cewa, INEC ta ce babu abin mamaki a cikin alkaluman rajistar katin zabe da aka samu daga Osun, kamar yadda jam’iyyar ADC ta yi zargi.
Kakakin shugaban INEC, Rotimi Oyekanmi, ya ce tun a baya Osun ke kan gaba wajen yin rajista ta yanar gizo tun daga shekarar 2021.
Hukumar zabe ta kasar ta ce dole ne duk masu yin rajista ta yanar gizo su je cibiyoyinta domin tabbatar da bayanansu tare da amfani da tsarin tantancewa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

