'Yan Adawa Sun Tsokano Tinubu, Ya Aika Sako Mai Zafi kan Zaben 2027

'Yan Adawa Sun Tsokano Tinubu, Ya Aika Sako Mai Zafi kan Zaben 2027

  • Shugaba Bola Tinubu ya ce ba zai yi wa masu neman kwace mulki daga hannunsa a 2027 sassauci ba
  • Mai girma shugaban kasar ya ce siyasa gasa ce da kowa ke da damar shiga, kuma za su fafata har zuwa ƙarshe
  • Shugaban kasar ya bayyana cewa sauye-sauyen da gwamnatinsa ta yi sun fara haifar da sakamako mai kyau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya gargadi abokan hamayyarsa masu neman kwace mulki daga hannunsa a zaben 2027 cewa ba zai ja da baya ba tare da fafatawa ba.

Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Talata lokacin da ya karɓi tawagar taron Bishof-Bishof na Katolika na Najeriya a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Shugaba Tinubu ya ja kunnen 'yan adawa
Mai girma Bola Ahmed Tinubu, shugaban kasar Najeriya Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Me Tinubu ya gayawa 'yan adawa?

Jaridar The Punch ta kawo rahoton cewa shugaban kasar ya ce masu neman karɓar mulki daga hannunsa za su iya jaraba sa'arsu, amma ya jaddada cewa siyasa gasa ce da kowa ke da damar shiga.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa na neman hada Obi fada da ƙabilarsa, ta fadi yadda zai cutar da su

“Waɗanda ke son karɓe mulki daga hannuna za su iya jaraba sa'arsu. Za su yi ƙoƙari. Komai halal ne a siyasa, kuma kowa na da dama iri ɗaya.
“Ba zan shimfiɗa musu jan kafet na girmamawa ba. Ba zan ba su igiyar da za su ɗaure ni a gida ba."
“A'a, za mu yi kokawa da juna har zuwa ƙarshen fafatawar. Wannan ita ce gaskiya. Hakan adalci ne a siyasa.”

- Shugaba Bola Tinubu

Tinubu ya kare hukumar INEC

Shugaba Tinubu ya kuma yi watsi da damuwar da ake nunawa kan tsarin zaɓe, inda ya kare Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) daga zargin nuna son kai.

Ya ce hukumar tana tsaka-tsaki kuma ba ta taɓa tsoratar da kowa ba.

“INEC ba ta nuna son kai. Ba ta taɓa tsoratar da kowa ba. Idan abokan hamayyar siyasa na fargaba ba, to suna tsoron inda suke ne da kuma rashin tabbas da ke tattare da waɗanda suke hulɗa da su.”

- Shugaba Bola Tinubu

Tinubu ya tabo batun ASUU

A wajen taron da bai wuce awa ɗaya ba, Tinubu ya shaida wa malaman addinin cewa sauye-sauye masu wahala da gwamnatinsa ta yi cikin shekaru uku sun fara haifar da sakamako a fili, TheCable ta kawo labarin.

Kara karanta wannan

An goyi bayan harbe 'yan ta'adda da zarar an gan su ba tare da jiran izini ba

Ya ce ci gaba da tafiyar da tsarin karatun jami'o'i ba tare da tsaiko ba na daga cikin abubuwan da talakawan Najeriya ke iya gani a rayuwarsu.

Shugaba Tinubu ya magantu kan zaben 2027
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Tinubu ya bayyana rashin yajin aikin Ƙungiyar Malaman Jami'o'i (ASUU) a matsayin amsar addu'arsa da kuma ta ɗimbin 'yan Najeriya.

“Babu ɗaya daga cikin 'ya'yanku da ke jami'a a yau, kuma zan ce dukkansu 'ya'yanku ne saboda ku Malaman Coci ne, da zai ce karatun shekara huɗu bai ɗauki shekara huɗu ba."
“ASUU ba ta yajin aiki. Ba sa jefa gidajenku cikin wahala. Shin wannan ba amsar addu'o'inmu ba ce? A gare ni, wannan amsa ce.”

- Shugaba Bola Tinubu

Peter Obi ya ba Tinubu shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa Dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya soki salon isar da sakon Shugaba Bola Tinubu.

Peter Obi ya roƙi shugaban kasar da ya riƙa yi wa ’yan Najeriya magana kai tsaye game da halin da ƙasar ke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng