Cikakken Sakamakon Zaben Gwamnan Ekiti kamar Yadda INEC Ta Sanar

Cikakken Sakamakon Zaben Gwamnan Ekiti kamar Yadda INEC Ta Sanar

  • Biodun Abayomi Oyebanji ya yi nasara a zaɓen jihar Ekiti na shekarar 2026, inda ya sake lashe zaɓen a matsayin gwamna a inuwar jam'iyyar APC
  • Oyebanji ya kafa tarihin samun nasara, inda ya zama gwamna mai ci na farko da ya taɓa yin tazarce ta hanyar sake lashe zaɓe a jihar Ekiti
  • Sakamakon ya nuna cewa Oyebanji ya ba wa Wole Oluyede na jam'iyyar PDP tazarar ƙuri'u masu yawa a mafi yawan ƙananan hukumomin jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Ado-Ekiti, Jihar Ekiti - An sake zaɓen Biodun Oyebanji na jam'iyyar APC mai mulki a matsayin gwamnan jihar Ekiti.

Gwamnan mai ci ya samu gagarumar nasara a zaɓen Ekiti na shekarar 2026, wanda aka gudanar ranar Asabar, 20 ga watan Yunin 2026.

Oyebanji ya yi nasara a zaben gwamnan Ekiti
Bidoun Oyebanji, Dare Bejide da Wole Oluyede Hoto: @biodunaoyebanji, @KoleShittu
Source: Twitter

Hukumar zabe ta INEC ta bayyana sakamakon zaɓen Ekiti na shekarar 2026, kamar yadda rahoton Daily Trust ya bayyana.

Kara karanta wannan

Zaben cike gurbi: APC ta ci gaba da karfafa ikonta bayan nasara a Kano

Oyebanji ya samu nasara a zaben gwamnan Ekiti

Oyebanji ya doke sauran masu ƙalubalantarsa a zaben a dukkan ƙaramomin hukumomi guda 16 na jihar Ekiti.

Farfesa Adenike Oladiji, babban jami'in tattara sakamakon zaɓe, ta sanar da sakamakon ƙarshe a cibiyar tattara sakamakon zaɓe da ke Ado-Ekiti, babban birnin jihar, a safiyar ranar Lahadi, 21 ga Yunin 2026.

Yadda sakamakon zaben da INEC ta sanar yake

Oladiji ta bayyana cewa Oyebanji ya samu ƙuri'u 319,224 inda ya doke Wole Oluyede na jam'iyyar PDP, wanda ya sami ƙuri'u 40,543, da kuma Dare Bejide na jam'iyyar ADC, wanda ya samu ƙuri'u 12,872, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Wannan nasara ta zaɓen 2026 ta sanya Oyebanji zama gwamnan jiihar Ekiti na farko da ya taɓa yin tazarce a matsayin gwamna mai ci.

Legit Hausa ta kawo muku sakamakon zaben na kowace ƙaramar hukuma kamar yadda INEC ta sanar.

1. Ƙaramar hukumar Ijero

Adadin masu zaɓe da aka yi wa rajista - 67,713

Kara karanta wannan

Bayan fafatawar APC da PDP, ADC, INEC ta sanar da wanda ya lashe zaben Ekiti

Adadin masu zaɓe da aka tantance - 30,795

ADC - 2,026

APC - 25,506

PDP - 2,479

Labour Party (LP) - 03

2. Ƙaramar hukumar Efun

Adadin masu zaɓe da aka yi wa rajista - 31,749

Adadin masu zaɓe da aka tantance - 11,393

ADC - 201

APC - 8,742

PDP - 2,051

LP - 02

3. Ƙaramar hukumar Emure

Adadin masu zaɓe da aka yi wa rajista - 39,299

Adadin masu zaɓe da aka tantance - 16,411

ADC - 732

APC - 14,325

PDP - 851

LP - 05

4. Ƙaramar hukumar Ikere

Adadin masu zaɓe da aka yi wa rajista - 69,320

Adadin masu zaɓe da aka tantance - 22,287

ADC - 245

APC - 11,116

PDP - 9,892

LP - 16

5. Ƙaramar hukumar Ido/Osi

Adadin masu zaɓe da aka yi wa rajista - 61,674

Adadin masu zaɓe da aka tantance - 20,217

ADC - 561

APC - 17,901

PDP - 1,449

LP - 0

Kara karanta wannan

Zaben Ekiti: Dan takarar gwamnan ADC ya sha kaye, APC ta yi nasara a rumfarsa

6. Ƙaramar hukumar Ekiti ta Kudu maso Yamma

Adadin masu zaɓe da aka yi wa rajista - 56,003

Adadin masu zaɓe da aka tantance - 18,094

ADC - 1,076

APC - 14,705

PDP - 1,800

LP - 2

7. Ƙaramar Hukumar Ado Ekiti

Adadin masu zaɓe da aka yi wa rajista - 118,817

Adadin masu zaɓe da aka tantance - 45,695

ADC - 1,054

APC - 38,026

PDP - 3,817

LP - 10

8. Ƙaramar Hukumar Ekiti ta Yamma

Adadin masu zaɓe da aka yi wa rajista - 65,160

Adadin masu zaɓe da aka tantance - 33,421

ADC - 674

APC - 28,258

PDP - 3,644

LP - 3

Oyebanji ya lashe zaben gwamnan Ekiti
Gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji bayan kada kuri'a Hoto: @biodunoyebanji
Source: Twitter

9. Ƙaramar Hukumar Ise Orun

Adadin masu zaɓe da aka yi wa rajista - 49,183

Adadin masu zaɓe da aka tantance - 15,219

ADC - 365

APC - 12,908

PDP - 1,627

LP - 19

10. Ƙaramar hukumar Ilejemeje

Adadin masu zaɓe da aka yi wa rajista - 20,862

Kara karanta wannan

Ekiti 2026: Rigima mai zafi ta kaure tsakanin magoya bayan APC da ADC bayan an jibge kudi

Adadin masu zaɓe da aka tantance - 11,077

ADC - 579

APC - 8,984

PDP - 1,243

LP - 0

11. Ƙaramar hukumar Moba

Adadin masu zaɓe da aka yi wa rajista - 56,346

Adadin masu zaɓe da aka tantance - 23,507

ADC - 994

APC - 20,500

PDP - 1,572

LP - 1

12. Ƙaramar hukumar Oye

Adadin masu zaɓe da aka yi wa rajista - 71,603

Adadin masu zaɓe da aka tantance - 23,577

ADC - 998

APC - 18,975

PDP - 2,891

LP - 6

13.Ƙaramar hukumar Ikole

Adadin masu zaɓe da aka yi wa rajista - 81,028

Adadin masu zaɓe da aka tantance - 28,568

ADC - 812

APC - 26,508

PDP - 750

LP - 4

14. Ƙaramar hukumar Aiyekire

Adadin masu zaɓe da aka yi wa rajista - 57,771

Adadin masu zaɓe da aka tantance - 19,405

ADC - 314

APC - 17,133

PDP - 1,563

LP - 2

15. Ƙaramar hukumar Ekiti ta Gabas

Kara karanta wannan

'Za ta karewa Tinubu a 2027,' Momodu ya fadi yadda Atiku zai kifar da APC

Adadin masu zaɓe da aka yi wa rajista - 66,171

Adadin masu zaɓe da aka tantance - 32,284

ADC - 1,730

APC - 26,359

PDP - 2,795

16. Ƙaramar hukumar Irepodun/Ifelodun

Adadin masu zaɓe da aka yi wa rajista - 75,552

Adadin masu zaɓe da aka tantance - 32,990

ADC - 511

APC - 29,278

PDP - 2,119

LP - 4

Jimillar masu zaɓe da aka yi wa rajista don zaɓen gwamnan Ekiti na 2026 - 988,251

Jimillar masu zaɓe da aka tantance don zaɓen - 383,940

Sakamakon ƙarshe na zaben a ƙasa:

ADC - 12,872

APC - 319,224

PDP - 40,543

LP - 276

ADP - 1,269

Dan takarar ADC ya sha kaye a rumfarsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar gwamnan jihar Ekiti na jam'iyyar ADC a zaben shekarar 2026, Ambassada Dare Bejide, ya sha kaye a rumfar zabensa.

Ambasada Dare Bejide, ya sha kaye a rumfarsa ta zaɓe a hannun ɗan takarar APC kuma gwamna mai ci, Biodun Abayomi Oyebanji.

Sakamakon farko daga rumfar ya nuna cewa jam'iyyar APC ta samu ƙuri’u 140, yayin da ADC ta samu ƙuri’u 37 kacal.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng