Jihar Ekiti
Gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji ya maye gurbin shugaban alkalan jihar wanda Allah ya yi wa rasuwa bayan doguwar jinya ranar 4 ga watan Nuwamba, 2024.
Allah ya yi wa babban alkalin Ekiti, Mai shari'a Oyewole Adeyeye rasuwa bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya. An ce gini ya rufta kan alkalin shekarar baya.
Kanin tsohon gwamnan Ekiti, Isaac Fayose ya musanta zargin da ake yaɗawa cewa ya yi kudi ne lokacin da Ayodele Fayose ke mukin jihar inda ya ce shi ɗan kasuwa ne.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yabawa gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji kan kokarin kawo sauyi da yake yi a jiharsa da kuma ayyukan alheri.
Jam'iyyar PDP a jihar Ekiti ta gabatar da rahoto ga kwamitin ladabtarwa bayan binciken tsohon gwamnan jihar, Ayodele Fayose inda ya bukaci a kore shi daga jam'iyyar.
Elebute-Halle, tsohuwar ƴar takarar gwamna a inuwar ADP a jihar Ekiti, ya jagoranci dubban magoya bayanta zuwa APC, ta ce sun gamsu da mulkin Tinubu.
Gwamnan Ekiti, Biodun Oyebanji, ya karawa wasu hazikan ma’aikatan gwamnati 82 kyautar N42m tare da ba su tabbacin biyan N70,000 a matsayin mafi karancin albashi.
Kanin tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose mai suna Isaac Fayose ya ce daga yau shi ne shugaban PDP inda ya ce duk wanda ba yarda ba ya je kotu yana jiransa a can.
Za ku ji cewa gwamnonin Kudu maso Yammacin kasar nan sun sake hallara a jihar Legas inda su ka kammala fitar da matsaya kan magance yunwa a yankin.
Jihar Ekiti
Samu kari