Bayan Fafatawar APC da PDP, ADC, INEC Ta Sanar da Wanda Ya Lashe Zaben Ekiti
- Hukumar zaɓe ta INEC ta ayyana gwamna mai ci, Biodun Oyebanji na APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Ekiti na 2026
- Oyebanji ya samu ƙuri’u 319,224 inda ya kayar da ɗan takarar PDP, Oluwole Oluyede, da na ADC, Dare Bejide a zaɓen
- Duk da koke-koken BVAS da zarge-zargen magudi daga wasu jam’iyyu, masu sa ido sun yaba da zaman lafiya da yadda zaɓen ya gudana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, ta sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar Ekiti da aka gudanar a ranar Asabar.
Hukumar INEC ta ayyana gwamna mai ci na Ekiti, Biodun Oyebanji na jam’iyyar APC, a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar na shekarar 2026.

Source: Twitter
An sanar da sakamakon zaben gwamnan Ekiti
Jami’ar da ta jagoranci tattara sakamakon zaɓen, Adenike Oladiji, ta sanar da sakamakon da misalin ƙarfe 3:13 na safiyar Lahadi 21 ga watan Yunin 2026, cewar Channels TV.
Ta bayyana cewa Biodun Oyebanji ya samu jimillar ƙuri’u 319,224, wanda ya ba shi nasara a kan manyan abokan hamayyarsa a zaɓen da aka gudanar a ƙananan hukumomi 16.
Farfesa Oladiji, wadda ita ce mataimakiyar shugabar jami’a, ta ce ɗan takarar PDP, Oluwole Oluyede, ya samu ƙuri’u 40,543.
Ta ƙara da cewa ɗan takarar ADC, Dare Bejide, ya samu ƙuri’u 12,872 a zaɓen da aka yi jiya Asabar 20 ga watan Yunin 2026.
A cewarta, an tantance masu zaɓe 384,940 yayin da aka samu sahihan ƙuri’u 375,777 da aka kaɗa a faɗin jihar.
Ta kuma bayyana cewa an soke ƙuri’u 6,332, lamarin da ya kai jimillar ƙuri’un da aka kaɗa zuwa 382,109.

Source: Facebook
Yawan korafe-korafe da aka samu a zaben Ekiti
Sakamakon ya kawo ƙarshen zaɓen gwamna da aka sa ido sosai, inda al’ummar Ekiti suka fito domin zaɓar gwamna cikin yanayi mai cike da zaman lafiya.

Kara karanta wannan
Ekiti 2026: Rigima mai zafi ta kaure tsakanin magoya bayan APC da ADC bayan an jibge kudi
Sai dai an samu wasu ƙalubalen na'urori da kuma zarge-zargen kura-kurai a wasu wuraren zaɓe duk da cewa lamarin bai hana gudanar da zaɓen ba, cewar Punch.
Kafin sanar da sakamakon, zaɓen ya haɗa da tsarin kaɗa ƙuri’a cikin tsari, wasu matsalolin BVAS da kuma zargin rashin bin ƙa’ida daga wasu ‘yan takara.
Hukumar INEC ta ce dukkan rumfunan zaɓe 2,445 da aka tanada sun buɗe domin gudanar da zaɓen a ranar Asabar.
A cewarta, rumfunan zaɓe 2,257, da ke wakiltar kashi 92.31 cikin ɗari, sun fara aiki kafin ƙarfe 8:30 na safe.
Sauran rumfunan zaɓe 188 sun samu ɗan jinkiri kaɗan amma sun fara aikin zaɓe kafin ƙarfe 10:30 na safe.
Ɗan takarar PDP, Oluwole Oluyede, ya koka kan matsalolin BVAS a mazabarsa da ke Ikere, inda ya ce wasu masu zaɓe sun kasa kaɗa ƙuri’arsu.
An kona ofishin yan sanda a Ekiti
A wani labarin, an ji cewa hankulan al'umma sun tashi a jihar Ekiti bayan wasu matasa sun bankawa ofishin yan sanda wuta.
Tsohon gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, ya yi tir da kona ofishin ‘yan sanda yayin da ake zaben gwamna a jihar.
Ya buƙaci mazauna Ekiti su ci gaba da zaman lafiya, yana mai cewa al’ummar Isan-Ekiti masu son zaman lafiya ne duk da abin da ya faru.
Asali: Legit.ng
