2027: Tsofaffin Gwamnoni 12 da Suka Samu Tikitin Takarar Sanata a APC

2027: Tsofaffin Gwamnoni 12 da Suka Samu Tikitin Takarar Sanata a APC

Tsofaffin gwamnoni 12 daga jihohi daban-daban sun samu tikitin takarar Sanata a jam’iyyar APC yayin da jam'iyyar ke shirin tunkarar babban zabe mai zuwa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Nigeria - Wasu daga cikin tsofaffin gwamnonin kasar nan da suka samu tikitin takara zuwa majalisar dattawa sun samu damar ba tare da hamayya ba, yayin da wasu suka doke abokansu a zaben futar da gwani.

Rahotanni sun tabbatar da cewa sanarwa daga jam’iyyar APC ta nuna cewa akalla tsofaffin gwamnoni 11 ta tabbata za su nemi kujera a majalisar dattawa.

Tsofaffin gwamnoni akalla 12 ne suka samu tikitin takarar majalisa a APC
Tsofaffin gwamnoni Godswill Akpabio, Abubakar Sani Bello da Malam Ibrahim Shekarau Hoto: Godswill Obot Akpabio/Senator Abubakar Sani Bello/ Bashir Sheka
Source: Facebook

Legit ta tattaro wasu daga cikin tsofaffin gwamnonin da suka samu wannan dama, wanda wasu daga cikinsu a yanzu haka suna zauren majalisar suna neman tazarce ne.

Kara karanta wannan

Galadima: Mutum 1 da ya samu takara a APC cikin mukarraban Tinubu 7 da suka yi murabus

Akwai wadanda wannan ne karon farkonsu na zuwa majalisar, wasu kuma sun taba zama sanatoci amma suka rasa kujerar, yanzu suke burin sake komawa Abuja.

Tsofaffin gwamnoni 12 sun samu takara a APC

Daga cikin tsofaffin gwamnonin da suka samu damar neman koma wa majalisa akwai wadanda suka taba shiga zauren majalisa, amma daga baya ba su samu sa'ar koma wa ba.

Wasu daga cikinsu kuma manyan kusoshi ne a majalisar dattawa da suke kokarin sake wakiltar mutanen yankunan da suka fito.

Daga cikinsu akwai:

1. Godswill Akpabio

Arise News ta ruwaito cewa tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom kuma shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya samu tikitin takarar Sanatan Akwa Ibom North-West bayan zaɓen fitar da gwani na APC da aka gudanar a jihar.

Akpabio ya samu tikitin takara a APC
Tsohon gwamnan AKwai Ibom kuma shugabanmajalisar dattawa, Godswil Akpabio a Abuja Hoto: Godswill Obot Akpabio
Source: Facebook

Majiyoyi sun ce Akpabio ya samu nasarar ne bayan samun goyon bayan jiga-jigan jam'iyyar APC a jihar ba tare da wata hamayya ba.

2. Malam Ibrahim Shekarau

A ruwayar jaridar Premium Times, tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya samu tikitin takarar Sanatan Kano ta Tsakiya bayan dawowarsa APC da kuma cimma matsaya da shugabannin jam’iyyar a jihar.

Kara karanta wannan

Jerin gwamnoni 7 da suka samu tikitin takarar sanata na jam'iyyar APC a zaben 2027

Gwamna ya rarrashi yan takara an bar wa Shekarau a Kano
Malam Ibrahim Shekarau, gwamna Abba Kabir Yusuf tare da masu neman takara a zaman sulhu a Abuja Hoto: Muhammad Mustapha
Source: Facebook

Wannan na zuwa ne bayan gwamna Abba Kabir Yusuf ya zauna da sauran 'yan takara, aka lallaba su a wani zama a Abuja, har suka janye wa Shekarau.

Shekarau ya taba wakiltar Kano ta tsakiya a majalisa a inuwar APC tsakanin 2019 da 2023.

3. Aliyu Magatakarda Wamakko

A cewar rahoton Vanguard, Sanata Aliyu Wamakko, tsohon gwamnan jihar Sakkwato, ya sake samun tikitin takarar Sanatan Sakkwato ta Arewa domin ci gaba da wakiltar mazabarsa a majalisar dattawa.

Wamakko ya samu damar sake takara a APC
Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Aliyu Wamakko Hoto: Senator Aliyu Magatakarda Wamakko
Source: Facebook

Shi ma ya samu nasarar ba tare da hamayya ba bayan wakilan kananan hukumomi takwas na yankinsa sun amince ya nemi ragamar jagorantarsu.

Tun 2015 tsohon gwamnan na Sokoto yake majalisa, yana neman wa'adinsa na uku karkashin APC.

4. Mukhtar Ramalan Yero

Rahoton jaridar Punch ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mukhtar Ramalam Yero, ya lashe zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar APC domin neman kujerar Sanatan Kaduna ta Arewa.

Kara karanta wannan

Bayan 'yan ta'adda sun kutsa makaranta an sace dalibai, gwamna Zulum ya dauki mataki

Ya doke sauran ‘yan takara biyu a zaɓen da aka gudanar a Zariya ranar Litinin 18 ga watan Mayu, 2026, inda ya samu tikitin jam’iyyar APC gabanin babban zaɓe mai zuwa.

Ramalan Yero ya shiga jerin masu takarar sanata a APC
Tsohon gwamnan Kaduna, Ramalan Yero APC. Hoto: Mukhtar Ramalan Yero
Source: Facebook

Da yake bayyana sakamakon zaɓen, jami’in tattara sakamako, Hassan Saleh, ya ce Ramalan Yero ya samu ƙuri’a 6,060, inda ya kayar da Muhammad Mu’azu Mukaddas wanda ya samu ƙuri’u 1,044, yayin da Yusuf Bala Ikara ya samu ƙuri’u 372.

5. Yahaya Bello

Daily Trust ta wallafa cewa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya lashe zaɓen fitar a gwani na jam’iyyar APC domin neman kujerar Sanatan Kogi ta Tsakiya.

Jami’in da ya jagoranci zaɓen, Dakta Sadiq Mohammed, ne ya sanar da sakamakon a ranar Litinin, 18 ga watan Mayu, 2026 da ya bayyana cewa tsohon gwamnan ya samu jimillar ƙuri’a 72,349.

Yahaya Bello zai yi takarar sanatan Kogi ta Tsakiya
Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello Hoto: Alhaji Yahaya Bello
Source: Facebook

Ya doke manyan abokan takararsa biyu, Ibrahim Yakubu Adoke wanda ya samu ƙuri’u 315, da kuma Momoh Yusuf Obaro wanda ya samu ƙuri’u 188.

6. Adamu Aliero

Daily Post ta kawo rahoton cewa APC ta tabbatar tsohon gwamna Adamu Aliero a matsayin ɗan takarar jam’iyyar APC na kujerar Sanatan Kebbi ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Biyu babu: Ministocin Tinubu da suka rasa takara a APC bayan sun yi murabus

Adamu Aliero ya samu takara a zaben 2027
Hoto: Alhaji Talba Aliero
Source: Facebook

An cimma wannan bayan dukkanin masu neman tikitin sanatan Kebbi ta Tsakiya sun janye daga takarar, lamarin da ya bai wa Aliero damar zama ɗan takarar bai ɗaya na jam’iyyar.

7. Abubakar Sani Bello

Blueprint ta ruwaito cewa tsohon Gwamnan jihar Neja, Sanata Abubakar Sani Bello, ya samu tikitin takarar sanatan Neja ta Arewa a jam'iyyar APC ta hanyar masalaha.

Abubakar Sani Bello
Tsohon gwamna a Najeriya Abubakar Sani Bello Hoto: Senator Abubakar Sani Bello
Source: Facebook

Mai magana da yawun jam’iyyar APC na jihar Neja, Musa Sarkinkaji, ne ya bayyana hakan a Minna ranar Litinin 18 ga watan Mayu yayin da yake ganawa da ‘yan jarida kan yadda aka gudanar da zaɓen fitar da gwani a jihar.

8. Gabriel Suswam

Tsohon gwamnan jihar Binuwai, Gabriel Suswam, ya lashe zaɓen fitar da gwani na kujerar Sanata na yankin Benue ta Arewa maso Gabas a jam’iyyar APC, inda ya kayar da mai ci, Sanata Emmanuel Udende.

Gabriel Suswam ya samu nasara a zaben fitar da gwani na APC
Tsohon gwamnan Binuwai, Gabriel Suswam Hoto: Gabriel Suswam
Source: Twitter

A cewar sakamakon da jam’iyyar APC ta fitar a hukumance, Suswam, wanda ya rike kujerar sanatan yankin daga 2019 zuwa 2023, ya samu ƙuri’u 131,083 inda ya doke abokan takararsa.

Kara karanta wannan

Wasu fitattun sanatocin Arewa 5 da suka hakura daga neman takara a 2027

9. Simon Lalong

Channels TV ta ruwaito cewa Simon Lalong, tsohon gwamnan Filato shi ma ya samu tikitin takarar Sanatan Plateau Kudu bayan samun goyon bayan shugabannin APC a jihar.

Tsohon gwamna a Filato ya samu takara a APC
Tsohon gwamnan jihar Filato, Solomon Lalong Hoto: Simon Bako Lalong
Source: Facebook

Stella Okotete da ke shugabantar kwamitin zaɓen fitar da gwani na Majalisar Tarayya na jam’iyyar a jihar ce ta sanar da hakan a watan Mayu, 2026.

10. Orji Uzor Kalu

The Sun Nigeria ta kawo labarin cewa sohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu, ya sake samun tikitin takarar Sanatan Abia ta Arewa domin neman komawa majalisar dattawa.

Tsohon gwamnan Abia ya samu tikitin takara a APC
Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu Hoto: Senator Uzor Orji Kalu
Source: Facebook

Sanata Kalu ya samu ƙuri’a 65,651, ya doke Nto da ya samu ƙuri’u 2,103, lamarin da ya bai wa shi nasara da tazarar ƙuri’a 63,548.

11. Adams Oshiomhole

Jaridar Independent ta ruwaito cewa Sanata Adams Oshiomhole ya lashe zaɓen fitar da gwani ba tare da hamayya ba a matsayin ɗan takarar jam’iyyar APC na kujerar Sanatan Edo ta Arewa a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Magana ta kare, APC ta tsayar da 'dan takarar gwamna a jihar Gombe

Tsohon gwamna Oshiomhole ya samu takarar koma wa majalisa
Tsohon gwamnan jihar Edo, Sanata Adams Oshiomhole Hoto: Adams Oshiomhole
Source: Twitter

Oshiomhole wanda ya ci zabe a 2023 shi ne kaɗai ɗan takara a zaɓen, kamar yadda Kassim Otono, wanda shi ne tattara sakamakon zaben fitar da gwanin ya tabbatar.

12. Ifeanyi Okowa

TVC News ta wallafa cewa tsohon gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, wanda ya sauya sheƙa zuwa APC, ya samu tikitin takarar Sanatan Delta ta Arewa a jihar.

Rahotanni sun ce Sanata Okowa ya doke sanatan da ke kan kujerar, Ned Nwoko, da kuma Maryam Ali a zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar da aka gudanar a kananan hukumomi tara na shiyyar.

Ifeanyi Okowa yasamu takara a APC
Tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa Hoto: Dr. Ifeanyi Arthur Okowa
Source: Twitter

A yayin sanar da sakamakon, jami’in zaɓe na APC, Johnbull Tonukari, ya ayyana Okowa a matsayin wanda ya yi nasara bayan ya samu ƙuri’u 113,309, zai nemi ya koma majalisa a badi.

Bola Tinubu zai yi wa APC takara

A baya, mun wallafa cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya lashe jihohi 19 da aka sanar da sakamakonsu a zaben fitar da gwani na shugaban kasa na jam'iyya mai mulki na APC gabanin zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi tukwicin da zai saka wa 'yan Najeriya da shi idan ya koma Aso Villa

Rahotanni daga jihar Borno sun nuna cewa Tinubu ya samu 100% na kuri’un mambobin jam’iyyar APC da aka kada, lamarin da Tinubu ya bayyana a matsayin nasarar dimokuradiyya ta cikin gida.

Sakamakon da aka tattara daga jihohi daban-daban ya nuna cewa shugaban ya samu gagarumar nasara yayin da ake ci gaba da tattara sauran sakamako daga fadin kasar nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng