Tafiyar Pantami Ta Samu Gagarumar Nakasu, Tsohon Sanata Ya Yi Murabus daga PDP

Tafiyar Pantami Ta Samu Gagarumar Nakasu, Tsohon Sanata Ya Yi Murabus daga PDP

  • Tafiyar Farfesa Isa Ali Pantami ta ci karo da gagarumar matsala bayan rasa wani babban jigo a PDP mai adawa a Najeriya
  • Tsohon sanata da ya wakiltar Gombe ta Arewa, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP a jihar Gombe
  • Takardar murabus din mai kwanan wata 12 ga Yulin 2026 ta isa hannun shugaban mazabarsa ta Nafada ta Gabas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gombe - Sanata Usman Bayero Nafada, CON, mai sarautar Sarkin Yakin Nafada, ya yi murabus daga jam'iyyar PDP mai adawa a jihar.

Tsohon sanatan da ya wakilci Gombe ta Arewa ya sanar da murabus dinsa daga jam'iyyar yayin da siyasa ta fara zafi a jihar bayan komawar Pantami PDP.

Tsohon sanata ya raunana Pantami bayan ficewa daga PDP
Tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami. Hoto: Professor Isa Ali Pantami.
Source: Twitter

Hakan na cikin wata sanarwa da hadiminsa, Boza Boza ya wallafa a shafinsa na Facebook ta wakilin Legit Hausa ya bibiya.

Kara karanta wannan

2027: Pantami ya yi zargin an shirya kaiwa tawagarsa hari a Gombe

Tsohon sanata ta fice daga jam'iyyar PDP

Bayero Nafada ya taba zama kakakin majalisar dokokin Gombe, sannan mataimakin kakakin majalisar wakilai na tsawon shekaru kafin daga baya ya zama sanata mai wakiltar Gombe ta Arewa, kujerar da Gwamna Inuwa ke nema.

Haka kuma, ya kasance dan takarar gwamnan PDP a Jihar Gombe a babban zaben shekarar 2019, inda ya wakilci jam'iyyar a fafatawar kujerar gwamna.

A cikin takardar murabus mai dauke da kwanan wata 12 ga Yulin 2026, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP a hukumance.

Shugaban jam'iyyar PDP ya karbi takardar murabus

An aike da takardar ne zuwa ga shugaban jam'iyyar na mazabar Nafada ta Gabas da ke karamar hukumar Nafada a Jihar Gombe.

Sanarwar ta tabbatar da cewa murabus din ya fara aiki ne bayan mika takardar ga shugabannin jam'iyyar a matakin mazaba.

Sanarwar ta bayyana cewa tsohon sanatan ya yanke shawarar barin PDP, amma ba ta bayyana dalilan da suka sa ya dauki wannan mataki ba.

Kara karanta wannan

Dan takarar shugaban kasa zai ba da ilimi kyauta, a rika ba dalibai abinci

Inuwa, Jamilu da Bayero Nafada sun gana a Gombe
Manyan APC a Gombe da Najeriya da suka hallara gidan Bayero Nafada. Hoto: Dr Jamil Gwamna.
Source: Facebook

Ganawar Bayero Nafada da Jamilu

Wannan lamari ya kara tabbatar da cewa Nafada na shirin komawa APC bayan ganawa da gwamna da ɗan takarar gwamna a APC.

A yayin ganawar, an gano Nafada tare da shugaban APC, Nentawe Yitwalda da Gwamna Inuwa Yahaya da Jamilu Isiyaku Gwamna.

Wannan ziyara ta faru ne a ranar Lahadi, 12 ga Yuli 2026, inda Gwamna ya samu rakiyar gwamnan jihar, Muhammadu Inuwa Yahaya, shugaban APC na kasa da Alhaji Yunusa Yakubu.

Mazauna jihar sun yi sharhi kan ziyarar tare da bayyana ra'ayoyi daban-daban game da makomar siyasar Gombe kafin babban zaben 2027.

Ana hasashen nasarar Pantami

A wani labarin, mun kawo muku cewa wani malamin jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Dr Kabiru Danladi Lawanti ya yi hasashe kan siyasar jihar Gombe.

Ya bayyana cewa har yanzu akwai alamun cewa dan takarar PDP, Sheikh Isa Ali Pantami na da damar da zai lashe zaben gwamna a Gombe.

Dr Lawanti ya gina hasashen ne da cewa Pantami ya samu karɓuwa a wajen jama'ar Gombe, tasirin ministan Abuja, Nyesom Wike da wasu abubuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.