Tsakani da Allah Peter Obi ba zai iya cin zabe ba in ji Sanatan NDC, Rufai Hanga

Tsakani da Allah Peter Obi ba zai iya cin zabe ba in ji Sanatan NDC, Rufai Hanga

  • Rufai Sani Hanga ya yi hasashen faduwar jam’iyyar hammayarsu wato NDC a zaben shugaban kasa da za a yi a 2027
  • Ko da jam’iyyar hamayyar ta tsaida Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso, sanatan na Kano ya fi ganin nasarar ADC
  • Sanata Hanga ya ce rashin tsaro da kuncin rayuwa da ake fama da shi za su iya yi wa Bola Tinubu illa wajen neman tazarce

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Rufai Sani Hanga ya bullo bayan an shafe kwana da kwanaki ba a jin duriyarsa, ya yi dogon husufi a fagen siyasar Najeriya.

Sanatan Kano ta tsakiya, Rufai Sani Hanga ya yi hasashen rashin nasarar NDC a zaben shugaban kasa duk da shi ‘dan jam’iyyar ne.

Hanga
Rabiu Kwankwaso, Rufai Hanga da Peter Obi Hoto: Saifullahi Hassan/Rufai Hanga/Peter Obi
Source: Facebook

Rufai Hanga ya yi hasashen zaben 2027

An yi hira da Sanata Rufai Sani Hanga a gidan rediyon Freedom a Kano, a nan ya nuna shakku kan samun galabar Peter Obi a babban zaben 2027.

Kara karanta wannan

Adeyemi: 'Yadda na samo aron N400m wajen kafa hukumar bogi

Duk da ya ce har gobe shi ‘dan NDC ne, amma bai ganin jam’iyyar hamayyar za ta lashe zaben shugaban kasa da za a yi a farkon badi.

“Duk dan siyasa na gari da ya san me yake yi, idan ya duba halin da ake ciki, ya san (Peter Obi) bai da kuri’un da za su ci zabe.
"A nan ne dai mataimakin shugaban kasa, Kwankwaso ne. Kuma Kwankwaso Kano kurum yake da ita, Kano ma rabi-da-rabi.
"Shi Peter Obi iyakar inda zai iya cin zabe a hasashe shi ne Anambra, sai kuma hatsin bara - ya tsinci nan, ya tsinci can."

- Sanata Rufai Sani Hanga

Kwankwasiyya ta rage karfi da aka shigo NDC

Rufai Sani Hanga ya ce a lokacin da suke cikin ADC, suna da karfi a jihohi irinsu Jigawa, Kaduna, Bauchi da makwabtansu, Katsina.

Sauya-shekar Rabiu Kwankwaso da mutanensa zuwa jam’iyyar NDC ya sa tsofaffin mutanensu na NNPP sun yi zamansu a cikin ADC.

Express Radio ta ce sanatan ya koka da cewa yanzu ba su da kowa a wadannan jihohi, an datse tasirin Rabiu Kwankwaso a mahaifarsa kurum.

Kara karanta wannan

Jerin sanatoci 20 cikin 109 da suka rage a jam'iyyun hamayya a Majalisar Dattawa

Peter Obi da Kwankwaso
Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a Abuja sai Rufai Hanga a gefe Hoto: Peter Obi/Rufai Hanga
Source: Facebook

Sanata Hanga ya ce Atiku zai iya nasara

Da aka yi masa zancen Atiku Abubakar, kwararren ‘dan majalisar ya ce akwai yiwuwar ya iya zuwa na daya a zaben shugaban kasa.

A hasashen Hanga, Atiku zai yi galaba a duka jihohin Arewa maso yamma, in ban da Zamfara da ya ce ita ma zai samu kaso a kuri’unta.

Haka nan kuma ya ce ADC za ta kwashe kuri’un Adamawa, Gombe da sauran jihohin Arewa maso gabas a 2027, yankin da Atiku ya fito.

Daga nan jam’iyyar ta ADC za ta rika samun kuri’u a jihohin Kudu, alhali kuwa yana ganin Bola Tinubu ba zai kai labari a Arewa ba.

Hanga ya fadi abin da zai kashe Tinubu

Sanatan na Kano ya ce abin da zai hana Tinubu nasara shi ne halin kuncin da rashon tsaro, yake cewa har a Kudu ana kuka da mulkin APC.

Kara karanta wannan

Abin da ya faru tsakani na da ita in ji malamin da ake zargi da neman matar aure

Hanga ya kuma nuna akwai yiwuwar shari’ar da ake yi da NDC a kotu su kawo cikas, ya ce ADC ce ta ke da karfin tunkarar gwamnati mai-ci.

Rufai Sani Hanga yake hasashe:

“Ni abin da na ke ji, Arewa idan dai ba karfa-karfa za a yi ba, da kyar Tinubu zai iya cin zabe saboda kullum kukan da ‘yan Arewa su ke yi. Ba su jin dadin abin da yake faruwa…”

Abba Gida-Gida ya kara karbuwa a Kano

An ji labarin Kwamishinan yada labaran Kano, Kwamred Ibrahim A. Waiya, ya karɓi bakuncin tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli na jihar.

Ƙungiyar tsofaffin jami'an gwamnatin ta bayyana cikakken goyon bayanta ga manufofi da shirye-shiryen gwamnatin Abba Kabir Yusuf tare da alkawarin taya sa kamfe.

'Yan siyasar waɗanda suka yi mulki a lokacin mulkin soja na 1997/199 sun kuma nemia biya su hakkokinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng