An Kama Mai Ciki Tana Kai wa Ƴan Boko Haram da ISWAP Kayan Aiki a Borno
- Sojoji sun kama wata baiwar Allah mai juna biyu da ake zargin tana kai wa 'yan ta'ddan Boko Haram/ISWAP kayan amfani a jihar Borno
- Matar ta shiga hannu ne bayan hannu ne bayan jami'an sun hango ta a lokacin da ake binciken ababen hawa, lamarin da ya sa aka kara bincike
- Hukumomin tsaro sun ce ana ci gaba da bincike domin gano waɗanda za a kai wa kayan da kuma alaƙarta da hanyoyin tallafa wa 'yan ta'adda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno – Sojojin Najeriya sun kama wata mata mai juna biyu da ake zargin tana kai wa mayaƙan Boko Haram da ISWAP kayan amfani a jihar Borno.
Majiyoyi sun ce an kama matar mai suna Falmata Adamu, mai shekara 28, a ranar 13 ga Yuli, 2026 yayin da sojoji ke gudanar da bincike a shingen tsaro da ke kan hanyar Mandaragirau zuwa Biu.

Source: Original
Zagazola Makama ya bayyana haka a shafinsa na X, inda rahoton ya ce jami'an tsaron sun tare matar ne bayan binciken da suka yi ya nuna akwai wasu kayayyaki da ta ɓoye a cikin tufafinta.
An kama mai yi wa ISWAP/Boko Haram aiki
The Cable ta ruwaito cewa majiyoyin sun ce kayayyakin da aka gano sun haɗa da fitilun hannu guda 17 da kuma batirin Tiger guda 19, waɗanda ake zargin an nausa da su zuwa sansanin 'yan ta'adda.
Bayan kama ta, jami'an tsaro sun tsare matar domin ci gaba da bincike kan inda aka nufa da kayan da kuma ko tana da alaƙa da hanyoyin samar wa ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP kayan aiki.
Rahoton ya bayyana cewa kamen na daga cikin matakan da Operation Hadin Kai ke ci gaba da ɗauka domin katse hanyoyin da ake amfani da su wajen isar da kayan tallafi ga mayaƙan Boko Haram da ISWAP a yankin Arewa maso Gabas.
Ana ci gaba da dakile Boko Haram/ISWAP
A cewar majiyoyin tsaro, rundunar na mai da hankali ba kawai kan fafatawa da 'yan ta'adda ba, har ma da dakile hanyoyin da suke samun kayan aiki.

Source: Facebook
Wannan zai taimaka wajen rage masu karfin samun sauran abubuwan da ke taimaka masu wajen gudanar da hare-hare da hallaka bayin Allah ba ji ba gani.
An kuma bayyana cewa duk da cewa yanayin tsaro a yankunan da ake gudanar da aiki na da ɗan sauƙi a halin yanzu, sojojin sun ci gaba da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana.
Fada da Boko Haram ya kashe amarya
A baya, mun wallafa cewa wani mummunan harin Boko Haram ya jefa ango da sauran mazauna wani yankin jihar Borno a cikin tashin hankali bayan an rasa rai yayin wata arangama tsakaninsu da 'yan sanda.
Yan ta'addan Boko Haram sun kai hare-hare kan sansanonin sojoji biyu a Maiduguri da safiyar Juma'a 10 ga watan Yuli, 2026, inda aka yi asarar ran wata amaryar da ke dakin mijinta makonni uku bayan aure.
Rundunar Operation Hadin Kai ta ce ta dakile duk yunkurin kutsawar 'yan ta'addan ISWAP da Boko Haram cikin Maiduguri, saboda haka an samu saukin barnar da ake yi na asarar rayuka da dukiyoyi.
Asali: Legit.ng

