Galadima: Mutumin da Ya Samu Tikitin Takara a APC bayan Murabus Din Mukarraban Tinubu 7
- Wasu mukarraban gwamnatin shugaba Bola Ahmed da dama sun yi murabus domin neman takara a matakai daban-daban
- Daga cikin mutane bakwai da suka yi murabus domin takarar gwamna, shida sun tsaya ne karkashin jam’iyyar APC mai mulki
- A zaben fitar da gwani na APC, mutum ɗaya ne daga Adamawa ya samu nasara, yayin da sauran mutane biyar suka kasa samun tikitin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Gabanin zaben shekarar 2027, masu mukamai da dama a gwamnatin Bola Tinubu sun yi murabus daga kujerarunsu.
Daga cikin masu mukaman guda bakwai sun yi murabus domin neman takarar gwamna a jihohi daban-daban.

Source: Facebook
Takarar zabe: Mukarraban Tinunu da suka yi murabus
Rahoton ICIR ya ce mutane shida daga cikinsu sun tsaya ne karkashin jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya domin gwada sa'arsu a jihohinsu daban-daban.
A yayin gudanar da zaben fitar da gwani na APC, Ahmed Galadima Aminu daga Adamawa ne kadai ya samu nasarar lashe tikitin jam’iyyar domin takarar gwamna mai zuwa.
Sauran mutane biyar da suka yi murabus daga mukamansu domin neman tikitin gwamna a karkashin APC sun gaza samun nasara a zabukan fitar da gwani da aka gudanar.
Daga cikin wadanda suka rasa takarar akwai tsohon ministan sufuri, Sa'idu Ahmed Alkali wanda ya yi rashin nasara a hannun Jamilu Isiyaku Gwamna da ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya Sarafadeen Alli ya kayar da shi.
Sauran sun hada da ministan harkokin waje, Yusuf Maitama Tuggar wanda ya yi rashin nasara a hannun tsohon gwamnan Bauchi, Mohammed Abdullahi Abubakar.
Sannan akwai mamba a kwamitin gudanarwa na NDDC, Abdulrazak Namdas da Ahmed Galadima Aminu ya kayar da shi.
Har ila yau, akwai tsohon shugaban kwamitin gudanarwa a Kwalejin Ilimi ta Oyo wanda ya rasa tikiti bayan nasarar Sarafadden Alli, cewar rahoton Punch.
Nasiru Gawuna ya samu takara a NDC
A wani bangare kuma, Nasiru Gawuna ya yi murabus daga kujerar shugaban hukumar gudanarwar Bankin Lamunin Gidaje na Tarayya.

Kara karanta wannan
Jerin gwamnoni 7 da suka samu tikitin takarar sanata na jam'iyyar APC a zaben 2027
Tsohon ɗan takarar gwamna a Kano ya yi murabus ne daga hukumar FMBN, domin neman gwamnan Kano kafin ya koma NDC.
Sai dai daga baya Nasiru Gawuna ya koma neman kujerar sanata a karkashin jam’iyyar NDC a mazabar Kano ta Tsakiya wanda yanzu aka tabbatar masa da tikitin a ƙarƙashin jam'iyyar.
Lamarin ya nuna yadda wasu manyan masu rike da mukamai suka bar ofisoshinsu domin shiga siyasa, amma da dama daga cikinsu ba su samu nasarar cimma burinsu ba.
Minista ya yi murabus saboda takarar gwamna
A baya, an ji rahoton cewa ministan sufuri, Sa’idu Alkali ya mika takardar murabus dinsa ga Shugaba Bola Tinubu a ranar Talata 31 ga watan Maris, 2026 inda ake zargin zai tsaya takarar gwamna.
Murabus din yana karkashin umarnin da shugaban kasa ya bayar cewa dukkan masu rike da mukaman siyasa su sauka kafin karshen Maris din shekarar 2026.
Sa’idu Alkali ya bi sahu Yusuf Tuggar da Yusuf Sununu wadanda suma suka yi murabus domin neman wasu kujerun a zaben shekarar 2027.
Asali: Legit.ng
