Tinubu Ya Fadi Tukwicin da Zai Saka wa 'Yan Najeriya da Shi idan Ya Koma Aso Villa
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyan wasu daga cikin abubuwan da zai mayar da hankali a kai idan 'yan Najeriya suka ba shi dama a 2027
- Daga cikin abubuwan da Tinubu ya kuma magana a kai akwai tattalin arziki da tsaro, wanda ya ce su ne suka fi daukar hankalin gwamnatinsa a yanzu
- Ya zargi wasu da kokarin tayar da zaune tsaye saboda manufofinsa kan cire tallafin mai da yaki da damfara wanda ya ce suna taimaka wa kasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Ogun - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa zai fi mayar da hankali kan manyan matsalolin siyasa da suka dabaibaye kasar nan idan ya shiga wa’adinsa na biyu.
Ya ce a halin yanzu gwamnatin sa ta fi mayar da hankali ne kan tattalin arziki da kuma tsaro, yana mai cewa wadannan abubuwa biyu su ne ginshikin dorewar kasa.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa Tinubu ya bayyana hakan ne a Legas yayin taron kaddamar da littafin kungiyar NADECO tare da bayar da lambar yabo ga masu fafutukar dimokuradiyya da abokan aikinsu.
Bola Tinubu ya magantu kan 2027
Jaridar Tribune Online ta kawo labarin cewa tsohon gwamnan jihar Ogun, Olusegun Osoba ne ya wakilci shugaban kasar a wajen taron.
Shugaban ya bayyana cewa wasu marasa kishin kasa ne ke haddasa matsalolin tsaro saboda adawa da manufofi da shirye-shiryen gwamnatin Tinubu.
Osoba ya isar da sakon shugaban kasar ga mahalarta taron da aka gudanar a cibiyar Muson da ke Onikan a Legas, inda ya ce:
“Shugaban kasa ya ce in gaya maku cewa zai aiwatar da manufofin siyasa a wa’adinsa na biyu. A yanzu hankalinsa yana kan tattalin arziki da matsalolin tsaro.”

Source: Twitter
Ya kara da cewa:
“Akwai wani yunkuri da aka shirya domin tayar da hankalin kasar daga wasu da suka fusata da manufofinsa kan cire tallafin mai.”

Kara karanta wannan
Bola Tinubu na amfani da kudin da ya ci bashi wajen gina ababen more rayuwa a Najeriya
An yabi fafutar dorewar siyasa
Tsohon gwamnan ya yaba wa kungiyar NADECO bisa rawar da ta taka wajen fafutukar dawo da dimokuradiyya a Najeriya.
A cewarsa, da ba a dawo da mulkin dimokuradiyya ba, da Bola Ahmed Tinubu bai samu damar zama shugaban kasa ba a halin yanzu.
Sai dai ya bayyana cewa ba a kafa kungiyar NADECO ne domin fafutukar zaben ranar 12 ga watan Yuni kadai ba, illa domin yakar mulkin danniya da tabbatar da dawowar dimokuradiyya.
Ya ce:
“Ba mu kafa NADECO saboda ranar 12 ga Yuni kadai ba, mun kafa ta ne domin fafutukar dawo da dimokuradiyya. Lokacin da MKO Abiola ya fara fafutukarsa ne aka shigar da shi cikin NADECO.”
Shugaban APC ya gana da Tinubu
A baya, mun kawo labarin cewa jam'iyyar APC ta bayyana yakinin cewa za ta warware duk wasu matsaloli da rikice-rikicen da suka biyo bayan zabukan fitar da yan takara Shugaban APC na kasa.

Kara karanta wannan
ADC: Atiku ya gurfana gaban kwamitin tantancewa, ya gabatar da muhimman manufofinsa
Farfesa Nentawe Yilwatda ne ya bayyana hakan jim kadan bayan ganawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Legas yayin da jam'iyyar ke ci gaba da gudanar da zaben fitar da gwani a fadin Najeriya.
Ana ci gaba da samun sabani da rigingimun tsakanin masu neman takara a inuwar APC, inda wasu ke nuna fushinsu a fili kan tsarin masalaha tare da bayyana zargin cewa ana yi masu rashin adalci
Asali: Legit.ng
