Kamfanin Amurka Mai Alaka da Atiku zai kai Karar Tinubu wajen Trump
- Wani kamfanin Amurka mai alaƙa da Atiku ya ce zai sanar da gwamnatin Donald Trump game da kama Adeniyi Adeyemi
- Kamfanin ya yi zargin cewa an kama Adeyemi ne kafin ya gabatar da hujjoji da bayanai ga jami'an gwamnatin Amurka
- Ya kuma yi zargin cewa an hana Adeyemi isar da bayanansa ga Amurka, sai dai kamfanin bai gabatar da wata hujja ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Wani kamfani da ke Amurka, Von Batten-Montague, wanda Atiku Abubakar ya ɗauka aiki, ya bayyana cewa zai sanar da jami'an gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump game da kama Adeniyi Adeyemi.
An kama Adeyemi ne bayan ikirarin shi ne Darakta Janar na PFIPC, wata hukuma da a ake ta ce-ce-ku-ce a kanta a Najeriya.

Source: Facebook
Kamfanin mai hedikwata a birnin Washington ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Laraba, sa'o'i kaɗan bayan kama Adeyemi bisa sammacin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Me yasa za a sanar da Trump?
Kamfanin ya yi ikirarin cewa an kama Adeyemi ne a daidai lokacin da ake shirin haɗa shi da manyan jami'an gwamnatin Trump domin tattauna zarge-zargen da ya yi kan wasu manyan jami'an gwamnatin Najeriya.
Sanarwar ta ce:
“Mun samu labarin cewa jami'an tsaron Najeriya sun kama Adeyemi a daidai lokacin da muke shirin haɗa shi da manyan jami'an gwamnatin shugaba Donald Trump.”
Kamfanin ya ƙara da cewa ana sa ran Adeyemi zai gabatar wa jami'an Amurka da takardu da kuma rubutacciyar rantsuwa domin tabbatar da zarge-zargen da yake yi.
Ya ce:
“An sanar da mu cewa an kama shi ne jim kaɗan bayan da aka bayyana cewa muna hulɗa da shi, kuma kafin ya miƙa mana hujjoji da kuma takardar rantsuwa kan bayanansa.

Kara karanta wannan
Bayan umarnin kotu, an kama shugaban hukumar bogi da ake ta cece kuce a kanta a Najeriya
“An shirya isar da waɗannan hujjojin ga manyan jami'an gwamnatin Trump, waɗanda suka buƙaci mu miƙa masu duk wani bayani da ya shafi zarge-zargen da Adeyemi ya yi.”
Karin zargin da kamfanin ya yi
Kamfanin Von Batten-Montague ya kuma yi zargin, ba tare da gabatar da wata hujja ba, cewa an kama Adeyemi ne domin hana shi gabatar da bayanai ga hukumomin Amurka.
Ya ce:
“Gobe za mu sanar da gwamnatin Amurka cewa an kama Adeyemi. Haka kuma za mu bayyana damuwarmu kan yadda aka kama shi..."
"Ciki har da bayanan da muka samu da ke nuna cewa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, ne ya matsa lamba a gaggauta kama shi domin hana shi gabatar da hujjoji ga gwamnatin Amurka.
“Za mu ci gaba da sanar da jama'a duk wani mataki da muka dauka a gaba.”

Source: Getty Images
Punch ta rahoto cewa sanarwar ta biyo bayan wani saƙo da babban abokin gudanarwar kamfanin, Karl Von Batten, ya wallafa, inda ya ce ya riga ya yi wa wasu jami'an gwamnatin Trump bayani.
An kama Adeyemi a Osun

Kara karanta wannan
PFIPC: Kamfanin Amurka ya kawo ɗauki ga shugaban hukumar bogi da ake ta surutu a Najeriya
A wani labarin, mun kawo muku cewa an kama Adeyemi ne ranar Talata a jihar Osun, sa'o'i kaɗan bayan mai shari'a Mohammed Umar na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya bayar da sammacin kama shi.
An kama shi ne bayan shafe kwanaki yana hira da 'yan jarida a boye saboda zargin kafa ma'aikatar bogi da aka ce ya yi a Najeriya.
'Yan sandan Najeriya sun zargi Adeyemi da ƙirƙirar jabun takardun gwamnati, ciki har da wasiƙar naɗin mukami ta bogi wadda ake zargin an sa, Femi Gbajabiamila hannu a kanta.
Asali: Legit.ng
