Masoyan Tsohon Minista Sun Dawo da Karfinsu, Sun Kalubalanci Hana Shi Takarar Gwamna
- Magoya bayan tsohon Ministan Harkokin Waje, Yusuf Maitama Tuggar, sun yi korafi game da zaben fitar da gwanin gwamna a APC
- Gidauniyar Tuggar ta ce ba a gudanar da zaɓen fitar da gwani ba a Bauchi, saboda haka sanarwar ta saba doka
- Ta buƙaci shugabannin APC su sake duba lamarin, su tabbatar da adalci, dimokuraɗiyyar cikin gida
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Magoya bayan tsohon Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, sun yi magana kan zaben fitar da gwani.
Masoyan na shi sun yi watsi da rahotannin da ke cewa tsohon gwamnan Bauchi, Mohammed Abdullahi Abubakar ya zama ɗan takarar gwamnan APC na zaɓen 2027.

Source: Twitter
Zaben fitar da gwani: Korafin masoyan Yusuf Tuggar
Gidauniyar Tuggar ta bayyana a cewa ikirarin fitowar Mohammed Abubakar a matsayin ɗan takara ya saba tsarin jam'iyya kuma ba shi da ingantaccen tushe na doka, cewar Tribune.
Da yake jawabi ga manema labarai a ofishin gidauniyar, tsohon shugaban CPC a Bauchi, Alhaji Shehu Barau Ningi, ya ce Mohammed Abubakar ne da kansa ya bayyana hakan.
Ningi, tare da wasu manyan jiga-jigan siyasa, ya ce har yanzu APC ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance da ke tabbatar da ɗan takarar gwamna.
Ya ce matsayar gidauniyar ta fito ne cikin wata wasiƙa da aka aika wa shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, tun ranar 2 ga Yunin 2026.
A cewar gidauniyar, ba a gudanar da wani zaɓen fitar da gwani na gwamna a ko'ina cikin Bauchi ba, saboda haka duk wanda ya ayyana kansa a matsayin wanda ya yi nasara ba shi da hujja.

Source: Facebook
Matsalar da za a iya samu a APC
Gidauniyar ta yi gargaɗin cewa tilasta Mohammed Abubakar a matsayin ɗan takara zai iya raunana APC a zaɓen 2027, saboda rashin gamsuwar wasu mambobi da yawaitar sauya sheƙa.
Ta kuma ce Mohammed Abubakar ya sha kaye a zaɓen 2019 kuma bai sake farfaɗo da jam'iyyar daga tushe ba bayan wannan lokaci.
Haka kuma, gidauniyar ta jaddada cewa ya dace a ba yankin Katagum damar samar da gwamnan Bauchi, domin bai taɓa yin gwamna ba tun bayan marigayi Abubakar Tatari Ali a shekarar 1983.
Saboda haka, ta bayyana Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, ɗan asalin Katagum, a matsayin wanda ya fi dacewa da tikitin APC, tana mai cewa ya kasance mai biyayya ga tafiyar jam'iyyar tun daga APP, ANPP, CPC har zuwa APC.
Gidauniyar ta kuma yi ikirarin cewa Mohammed Abubakar ya shiga APC ne kwanaki 52 kafin zaɓen fitar da gwani na 2014, sannan ya nesanta kansa da jam'iyyar bayan shan kayen 2019.
Takara: Tuggar ya karyata sukar Tinubu
A baya, an ji cewa tsohon Ministan harkokin waje, Ambassada Yusuf Tuggar, ya yi martani kan rahotannin da ke cewa ya soki shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
A cewar wasu rahotannin da aka yada, tsohon Ministan ya soki shugaban kasar ne bayan ya rasa.tikitin jam'iyyar APC.
Sai dai, a martanin da ya yi, ya warware zare da abawa kan rahotannin da aka yada a kansa masu nuna ya soki Shugaba Tinubu.
Asali: Legit.ng

