Jerin Sanatoci 20 cikin 109 da Suka Rage a Jam'iyyun Hamayya a Majalisar Dattawa

Jerin Sanatoci 20 cikin 109 da Suka Rage a Jam'iyyun Hamayya a Majalisar Dattawa

Abuja - Akwai sanatoci 109 a Majalisar dattawa tsakanin jam’iyyun siyasa da ake da su. Sai dai kusan an shanye ‘yan adawa a Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abin da rahoton nan ya yi shi ne kokarin tattaro jerin sanatocin da har gobe suna nan a jam’iyyun hamayya duk da rinjayen APC a majalisa.

Majalisa
Wasu sanatoci zaune a Majalisar dattawa a Abuja Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

Sanatocin da ke wakiltar jam’iyyun adawa

A yau 13 ga watan Yuli 2026, sanatocin jam'iyyar hamayya su ne:

1. Aminu Waziri Tambuwal

Aminu Waziri Tambuwal sanata ne a jam’iyyar adawa ta ADC. Tsohon gwamnan yana cikin ‘yan PDP da suka shiga jam’iyyar ADC.

Sanatan na Kudancin Sokoto ba zai nemi tazarce a zabe mai zuwa ba. Tambuwal ya hakura da kujerar bayan shekaru hudu kawai a kan ta.

2. Mohammed Ogoshi Onawo

Tsohon shugaban majalisar dokokin Nasarawa, Mohammed Ogoshi Onawo shi ne sanatan farko da APM ta samu a cewar gidan rediyon FRCN.

Kara karanta wannan

Babu sunan Jonathan a ‘yan takaran PDP, Wike ya samu yadda yake so wajen INEC

Sanata Onawo na Nasarawa ta Kudu ya sauya-sheka daga ADC ne bayan ‘yan kwanaki a cikinta, ya kafa hujja da rikicin cikin gida da ake samu.

3. Binos Dauda Yaroe

Shi ma Binos Dauda Yaroe mai wakiltar yankin kudancin Adamawa yana cikin ‘yan adawa a Majalisar dattawa, yanzu haka yana jam’iyyar ADC.

Duk da gwamnan Adamawa ya sauya-sheka, Sanata Binos Dauda Yaroe ya ki shiga APC, Daily Post ta rahoto shi yana cewa jam’iyyar ta gaza.

4. Austin Akobundu

Mai wakiltar tsakiyar Abia a Majalisar dattawa, Austin Akobundu shi ma yana cikin ‘yan adawa. Sanatan yana cikin wadanda ADC ta dauka.

5. Lawal Adamu Usman

Mr. LA kamar yadda aka fi saninsa ‘dan majalisa ne a karkashin ADC. Sanatan na Kaduna ta tsakiya ya shiga jam’iyyar hadakar ne daga PDP.

A zaben 2023, Lawal Adamu Usman da sauran 'yan takaran sanatocin PDP duk sun ci zabe a Kaduna.

6. Ireti Kingibe

Ireti Kingibe tana cikin daidaikun mata a Majalisar tarayya kuma tana tare da jam’iyyar adawa. Sanatar Abuja ta shiga jirgin ADC da ta bar LP a 2025.

Kara karanta wannan

Yadda alkalin CCT ya casa Tinubu, Saraki da sauran manya kafin ya kare a kurkuku

7. Tony Nwoye

A shekarar nan Punch ta rahoto Sanata Tony Nwoye ya bar LP zuwa ADC, daga baya kuma ya shiga NDC. ‘Dan majalisar na Anambra ya bi tafiyar Peter Obi.

8. Victor Umeh

A watan Mayun 2026 jaridar The Cable ta rahoto cewa Victor Umeh ya shiga NDC. Sanata Godswill Akpabio ya karanto wasikar sauya shekarsa a majalisa.

9. Rufai Sani Hanga

Rufai Sani Hanga shi kadai ne sanatan jam’iyyar adawa daga Kano a majalisa. Dattijon ya rika sauya-sheka tare da Madugun Kwankwasiyya.

Sanata Hanga mai wakiltar tsakiyar birnin Kano ya ci zabe a 2023 a NNPP, daga baya suka koma ADC amma bayan ‘yan kwanaki suka shiga NDC.

10. Abba Moro

Tsohon ministan cikin gida, Abba Moro wanda yanzu sanata ne, yana cikin masu kare adawa a majalisa. Sanatan na Benuwai yana nan a jam’iyyar PDP.

Majalisa
Hoton Sanata Aminu Tambuwal, 'Yan majalisa da Sanata Rufai Hanga Hoto: Aminu Waziri Tambuwal Media Office, Nigerian Senate da Rufai Sani Hanga
Source: Facebook

Sauran ‘yan adawa a Majalisar dattawa

Kara karanta wannan

Bincike ya shiga matatun mai, EFCC ta kai tsohon shugaban matatar Fatakwal kotu

11. Seriake Dickson

Seriake Dickson da ya bar PDP ya shiga sabuwar jam’iyyar nan ta NDC kuma ya zama jagoranta, a karkashinta Sanatan yammacin Bayelsa yake takara.

12. Enyinnaya Abaribe

Enyinnaya Abaribe yana jam’iyyar hamayya ta LP kuma Premium Times ta ce an sake ba shi tikiti ya shiga wata takarar a zaben 2027 a Abia ta Kudu.

13. Shehu Usman Buba

Wani sanata da bai tare da jam’iyya mai rinjaye a majalisa shi ne Shehu Usman Buba. Daily Post ta ce ya sauya-sheka zuwa PRP da nufin takarar gwamna a Bauchi.

14. Ibrahim Lamido

Sanatan gabashin Sokoto ya bar APC a kwanaki. Vanguard ta ce saboda rashin tsaro ya canza sheka. Shi ma ba zai nemi wata takarar a zabe mai zuwa ba.

Ragowar sanatoci na jam’iyyun adawa

15. Natasha Akpoti-Uduaghan (PDP)

16. Abdul Ningi (ADC)

17. Khalid Ibrahim Mustapha (ADC)

18. Emmanuel Nwachukwu (APGA)

19. Kamorudeen Lere Oyewumi (Accord)

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Shawarar da Shagari ya taba ba mu tare da Janar Shehu Yar'adua

20. Olaka Nwogu (PDP)

PDP ta daura sunayen 'yan takarar shugaban kasa

Sunayen Sandy Onor da Babangida Umaru ne a shafin INEC a matsayin ‘yan takarar shugaban kasa a PDP kamar yadda labari ya zo a farkon makon nan.

Tsagin Nyesom Wike ya tsaida ‘dan takarar shugaban kasar PDP, ana jiran makomar masu neman takarar gwamnonin jihohi da 'yan majalisa na dokoki.

A gefe guda, bangaren Tanimu Turaki ya ba Goodluck Jonathan tikitin shiga zaben 2027 a PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng