Wasu Fitattun Sanatocin Arewa 5 da Suka Hakura daga Neman Takara a 2027
- Akwai alamun cewa akalla mambobi 18 na Majalisar Tarayya ta 10 a Najeriya ba sa neman sake tsayawa takara gabanin zaben 2027
- Daga cikinsu akwai sanatoci da dama da suka goge a majalisar wadanda suka ba da gudunmawa tsawon shekaru a Abuja
- Mafi yawan wadanda suka hakura da neman takarar sun yi hakan ne saboda neman wata kujera fiye da wacce suke kai a halin yanzu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - A Najeriya, duk lokacin da zabe ya gabato ana samun sauye-sauye musamman daga yan siyasa domin neman sababbin kujeru.
Daga cikin wasu sanatoci da suka nuna cewa ba za su nemi takara ba akwai mambobi 14 da kuma ‘yan majalisar wakilai shida.

Source: Facebook
Rahoton Leadership ya ce wadannan ‘yan majalisar ba su neman komawa kujerun da suke kai yanzu saboda wasu dalilai na su.

Kara karanta wannan
Tinubu ya yi karin haske kan zargin shirin sauya sunan Najeriya, rusa shari'ar Musulunci
Hakan na faruwa ne saboda wasu daga cikinsu sun shiga takarar gwamna a jihohinsu yayin da wasu suka janye daga takarar saboda wasu dalilai daban-daban.
Legit Hausa ta yi duba ga wasu daga cikin fitattun sanatoci a Arewacin Najeriya da suke hakura da neman kujerarsu a zaben 2027.
1. Aminu Waziri Tambuwal - Sokoto
Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya nuna dattaku a jihar Sokoto yayin fitar da ƴan takara a jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya.
Tambuwal ya janye daga takarar kujerar Sanatan Sokoto ta Kudu a karkashin ADC domin bai wa wani tsohon kwamishina damar samun kujera.
Jam’iyyar ADC ta ce Tambuwal ya dauki matakin ne domin tabbatar da hadin kai, zaman lafiya da karfafa dimokuradiyya cikin gida gabanin zaben 2027.

Source: Facebook
2. Sanata Ahmed Wadada - Nasarawa
Sanata Aliyu Wadada Ahmed, mai wakiltar Nasarawa ta Yamma a Majalisar Dattawa ya fasa sake neman takarar kujerarsa a majalisa.
Wadada ya fara neman tikitin takarar gwamna a jam’iyyar APC domin jagorantar Nasarawa mai arzikin ma’adanai.
Sanatan, wanda kwanan nan ya fice daga jam’iyyar SDP, ya samu goyon bayan gwamna Abdullahi Sule a matsayin wanda yake so ya gaje shi a mulkin jihar.

Source: Facebook
3. Sanata Ibrahim Lamido - Sokoto
Sanata Ibrahim Lamido ya yi magana kan fasa takarar sanata inda ya ce rashin ikon gudanarwa ne ya sa ya hakura da sake neman kujerar na mazabar Sokoto ta Gabas a 2027.
Dan majalisar ya bayyana cewa matsalar tsaro a Sokoto ta Gabas na bukatar shugaba mai ikon aiwatar da tsare-tsaren gwamnati kai tsaye.
Yayin da ya gaza samun tikitin takarar gwamna a karkashin ADC, Sanata Lamido ya bayyana matakin da ya dauka a matsayin abin da ya dace.

Source: Facebook
4. Sanata Shehu Buba - Bauchi
Dan majalisar dattawan da ke wakiltar Bauchi ta Kudu a karkashin jam’iyyar APC, Sanata Shehu Umar Buba, ya shiga takarar gwamnan Bauchi a hukumance.
Buba ya sayi fom din nuna sha’awa da tsayawa takara na APC na Naira miliyan 50, sannan ya halarci tantancewar jam’iyyar, cewar Premium Times.
Sai da Sanata Buba ya janye kafin rasa tikitin neman takarar gwamna a APC inda jam'iyyar ta ba Mohammed Abdullahi Abubakar tikitin domin takara a zaben 2027.

Kara karanta wannan
Tinubu ya fadi tukwicin da zai saka wa 'yan Najeriya da shi idan ya koma Aso Villa
Al'ummar Bauchi da dama sun nuna damuwa bayan zaben fitar da gwani inda suke bayyana rashin goyon baya ga tikitin da aka ba MA Abubakar.

Source: Facebook
5. Sanata Saliu Mustapha - Kwara
Dan majalisar dattawa mai wakiltar Mazabar Kwara ta Tsakiya, Saliu Mustapha, ya hakura da neman sake tsayawa takarar kujerar majalisa, inda ya fara neman tikitin APC domin takarar gwamnan jihar a zaben 2027.
A halin yanzu kuma, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq wanda wa’adinsa zai kare a shekara mai zuwa, na shirin tsayawa takarar kujerar Sanatan Kwara ta Tsakiya, cewar The Nation.
Tuni APC ta zabi kakakin majalisar jihar, Rt. Hon. Salihu Yakubu a matsayin dan takarar jam'iyyar a zaben gwamnan bayan rikici ya barke kan wanda gwamnan jihar ke so tun farko.
Goje ya rasa tikitin takarar sanata a 2027
A baya, an ji cewa tsohon gwamnan Gombe, Danjuma Goje ya rasa tikitin jam'iyyar APC na tsayawa takarar Sanatan Gombe ta Tsakiya karo na biyar a zaben 2027.
DCP Muhammed Ahmed, wanda gwamna Inuwa Yahaya ke goyon baya ne ya samu nasara a zaben fitar da gwanin da aka gudanar a Gombe.
'Dan takarar na APC ya ce an gudanar da zaben cikin lumana ba tare da wata matsala ba a kananan hukumomin yankin Gombe ta Tsakiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
