A Karshe, Tsohon Gwamnan Kaduna Ya Gaji da Zama, Ya Sauya Sheka Zuwa APC, Ya Fadi Dalili

A Karshe, Tsohon Gwamnan Kaduna Ya Gaji da Zama, Ya Sauya Sheka Zuwa APC, Ya Fadi Dalili

  • Jami'yyar APC ta samu karuwa yayin da tsohon gwamnan jihar Kaduna ya koma jam'iyyar a yau Litinin
  • Tsohon gwamnan, Ramalan Yero ya koma jam'iyyar ce watanni kadan bayan watsar da kashin jamiyyar PDP mai adawa a jihar
  • Yero ya ce ya yanke shawarar ce bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma wadanda suke kusa da a siyasance

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

Sauya shekar na zuwa ne watanni kadan bayan ficewarsa daga jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya.

Tsohon gwamnan Kaduna ya koma APC bayan watsar da PDP
Tsohon gwamnan Kaduna, Ramalan Yero ya koma jam'iyyar APC. Hoto: Mukhtar Ramalan Yero.
Asali: Facebook

Yaushe Yero ya koma jam'iyyar APC?

Wannan na kunshe ne a cikin wata hira da 'yan jaridu a yau Litinin 12 ga watan Faburairu a Kaduna, cewar BBC Hausa.

Kara karanta wannan

Gasar AFCON: An shiga karancin rigunan Super Eagles a Kano, 'yan kwasuwa sun kwashi ganima

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya ce ya koma APC ne bisa dalilai na kashin kansa bayan ya tattauna da masu ruwa da tsaki a siyasa.

Yero ya rike mukamin gwamnan jihar ce daga shekarar 2012 zuwa 2015 jim kadan bayan rasuwar marigayi Gwamna Patrick Yakowa.

A watan Oktobar 2023 ce tsohon gwamnan ya sanar da ficewarsa daga jami'yyar PDP mai adawa a jiharsa, cewar Daily Trust.

Martanin Yaro bayan sauya shekar

Yayin da ya ke martani, Yero ya ce:

"Tun ranar da muka bar jam'iyyar PDP, jam'iyyu da dama sun tuntube mu ciki har da jam'iyyar APC.
"Mun hadu kuma mun tattauna da su tun ranar da muka bar PDP, mun yi zama da Gwamnan mun fada masa cewa za mu shiga APC saboda gayyatar da aka mana."

Yero ya yi takarar gwamna a shekarar 2015 a jam'iyyar PDP inda ya sha kaye a zaben a hannun tsohon gwamna, Nasir Elrufai na jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

AFCON: Ana saura kwana 4 aurensa ya rasu, cewar iyalan marigayi Ayuba a Kwara, bayanai sun fito

Ciyamomi 3 sun koma NNPP a Kano

Kun ji cewa wasu ciyamomin kananan hukumomi uku a jihar Kano sun sauya sheka zuwa jam'iyyar NNPP mai mulkin jihar.

Ciyamomin uku sun hada da na Garum-Malam da Nassarawa da kuma Dawakin Tofa inda suka watsar da jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel