'Sai da Ku': Kwankwaso Ya Tuno Alakar Arewa da Kudu gabanin 2027
- 'Dan takarar mataimakin shugaban kasa a NDC, Rabiu Musa Kwankwaso ya aika bukata ga 'yan Kudancin Najeriya yayin da ya hada kai da Peter Obi gabanin 2027
- Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce shugabannin Najeriya na baya sun nuna muhimmancin yafiya da haɗin kai bayan yaƙin basasa
- Kwankwaso yana wannan batu ne a yayin da babban zabe ya ke kara karatowa inda ya ya ke a matsayin 'dan abokin takarar Obi da ya zo daga Kudu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar NDC a zaben 2027, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi kira da a sake farfado da kyakkyawar alakar siyasa tsakanin Arewa da yankin Kudu maso Gabas.
Sanata Kwankwaso ya bayyana hakan ne a yadda ake yunkurin hada kain Arewa da Kudu gabanin babban zabe da za a fafata tsakanin manyan yan siyasar kasar nan.

Source: Facebook
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana haka ne ta cikin hira da ya yi da kafar BBC Igbo da aka wallafa sashenta a shafin Instagram.
Kwankwaso ya nemi a hada kai
Jaridar Punch ta kawo labarin cewa Kwankwaso ya ce ba yau aka fara samun kyakkayawar alaka tsakanin bangarorin biyu ba, kuma akwai bukatar a farfado da tsohuwar alakar.
Ya ce tarihi ya nuna cewa Arewa da Kudu maso Gabas sun dade suna aiki tare a fagen siyasa, saboda haka lokaci ya yi da 'yan Najeriya za su rungumi yafiya da hadin kai.
A cewarsa:
"Dole mu yafe wa junanmu. Dole mu yi aiki tare a matsayin yan uwa. Kudu maso Gabas sun kasance abokanmu da kawayenmu tsawon shekaru."
Tsohon gwamnan Kano ya tuna cewa a Jamhuriya ta Farko, jam'iyyar NPC ta yi kawance da NCNC karkashin jagorancin Nnamdi Azikiwe.
Kwankwaso ya tuno alakar Arewa da Kudu
Ya kuma ce a Jamhuriya ta Biyu, shugabannin NPN karkashin Shugaba Shehu Shagari sun ci gaba da hada kai da shugabannin yankin Kudu maso Gabas.

Source: Facebook
Sanata Kwankwaso ya ce bayan karewar yakin basasa a 1970, shugabannin kasar sun nuna hangen nesa ta hanyar rungumar yankin Kudu maso Gabas maimakon ci gaba da nuna gaba.
Jagoran ya ce hakan ne ya sa aka bai wa marigayi Alex Ekwueme mukamin mataimakin shugaban kasa, kuma abokin Arewa ne shi.
Ya kuma tuna cewa ya halarci jana'izar Ekwueme a garinsu na Oko da ke jihar Anambra domin mutunta shi bayan rasuwarsa.
Har ila yau, ya yi magana kan dawowar marigayi shugaban Biafra, Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu, daga gudun hijira.
A cewarsa, shugabannin NPN ne suka taimaka wajen dawo da Ojukwu domin ya shiga siyasar dimokuradiyya, duk da rawar da ya taka a lokacin yakin basasa.
Kwankwaso ya ce:
"Ba za mu iya kasancewa a kasa daya muna ta fada ba. Dole mu zauna lafiya, ko wane bangare ne ya yi wa dayan laifi."
Sai dai ya jaddada cewa kokarin karfafa alaka da Kudu maso Gabas ba yana nufin adawa da Kudu maso Yamma ko wani yanki ba.

Kara karanta wannan
Kwankwason APC ya ari bakin 'yan Arewa, ya yi magana kan tikitin Tinubu da Shettima a 2027
Kwankwaso ya mika bukata ga gwamnati
A baya, mun kawo rahoton cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bukaci gwamnatin tarayya ta gudanar da sahihiyar kidayar jama'a da gidaje ba tare da wani karin jinkiri ba domin amfanin kasa.
Sanata Kwankwaso ya ce Najeriya ta shafe shekara 20 ba tare da gudanar da sabon kidayar jama'a ba tun bayan wanda aka yi a 2006 wanda hakan zai iya jawo nakasu ga shirya ayyukan ci gaban kasa.
Tsohon gwamnan wanda shi ne 'dan takarar mataimakin shugaban kasa a inuwar jam'iyyar NDC ya jaddada cewa amfani da fasaha da tabbatar da gaskiya zai kara ingancin sakamakon kidayar idan an shirya.
Asali: Legit.ng

