‘Abin da Ke Saurin Fusata Tinubu game da Buhari’: Kashim Shettima Ya Magantu
- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya yabawa Bola Tinubu game da yadda ya ke daukar matakai masu muhimmanci
- Shettima ya ce Tinubu shugaba ne mai daukar alhakin matakansa, baya dora laifi kan wasu, kuma yana ci gaba da kokarin rage tsadar rayuwa
- Ya bukaci 'yan Najeriya su ci gaba da hakuri da goyon bayan sauye-sauyen gwamnati, yana mai jaddada cewa akwai haske a gaba da fatan samun ci gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya yabawa kwarin gwiwar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a Najeriya.
Kashim Shettima ya ce Tinubu bai nade hannunsa ba duk da ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta ta bangarori da dama da ke wahalar da ƴan ƙasar.

Source: Twitter
Shettima ya bayyana haka ne yayin tunawa da marigayi Muhammadu Buhari bayan ya cika shekara daya da rasuwa, cewar Channels TV.
Dimbin albarka da Najeriya ke da su
Mataimakin shugaban kasar ya ce Najeriya tana da dimbin albarka sosai duba da yawan al'umma da take da shi wanda ke da tasiri.
Ya bayyana cewa Tinubu bai taba yarda da daurawa wani laifi ba game da abubuwan da suke faruwa a kasar musamman kan marigayi Muhammadu Buhari da sauran shugabannin Najeriya.
Ya ce:
"Wannan kasar tana da albarka sosai, zan fada muku cewa shugaban kasa, Bola Tinubu mutum ne mai son kawo sauyi.
"Yana karfin halin daukar matakai masu tsauri domin kawo sauyi a bangaren tattalin arziki, kuma mutum ne wanda bai son daura wa wani laifi.
"A shekaru uku da suka wuce, abin da zaka yi ka fusata shugaan kasa da sauri shi ne sukar Muhammadu Buhari."

Source: UGC
Shirin da Tinubu ke yi game da Najeriya
Har ila yau, Shettima ya ce Tinubu a shirye yake a kullum domin tabbatar da kawo sauyi a kasar musamman bangaren tattalin arziki.
Mataimakin shugaban kasa ya ce a kullum burin Bola Tinubu shi ne kawo sauyi da nemo hanyoyin bunkasa tattalin arzikin kasar saboda a samu jin dadi da walwala.
"Shi a kullum a shirye yake da ya dauki alhakin duk abin da ya aikata musamman daga matakan da ya ke dauka.
"Muna da kalubale kan tashin farashin kaya da karancin abinci amma gwamnati ba ta nade hannayenta ba, tana kokari wurin kawo sauyi."
- Cewar Kashim Shettima
Kashim Shettima ya ce akwai haske a gaba inda ya shawarci yan Najeriya da su ci gaba da hakuri da kokarin kawo ci gaba a kasarsu.
Gowon ya yabawa salon mulkin Buhari
Mun ba ku labarin cewa janar Yakubu Gowon mai ritaya ya ce marigayi Muhammadu Buhari ya bayyana salon yadda marigayin ya yi mulki.
Gowon ya ce Buhari ya sadaukar da mulkinsa wajen yi wa daukacin 'yan Najeriya hidima, ya ce ra'ayin cewa ya fifita Arewa ba gaskiya ba ne.
Tsohon shugaban ƙasar ya kuma yabawa Goodluck Jonathan saboda amincewa da sakamakon zaɓen 2015 cikin lumana, yana cewa hakan ya taimaka wajen kauce wa rikici.
Asali: Legit.ng

