Majalisar Dattawa Ta Tallafa wa Iyalan Wadanda Suka Mutu wajen Ceto Daliban Oyo

Majalisar Dattawa Ta Tallafa wa Iyalan Wadanda Suka Mutu wajen Ceto Daliban Oyo

  • Majalisar Dattawan Najeriya ta bada tallafin Naira miliyan 50 ga iyalan mutum biyar da suka mutu a ƙokacin ceto daliban Oyo
  • Rahoto ya nuna cewa malamai biyu sun mutu a hannun masu garkuwa, yayin da jami’an tsaro uku suka rasu a aikin ceton
  • Dakarun sojoji da wasu jami'an tsaro sun yi nasarar kubutar da dalibai 39 da malamai bakwai bayan sace su a jihar Oyo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Majalisar Dattawan Najeriya ta bayar da tallafin Naira miliyan 50 ga wadanda suka rasa rayukansu a kokarin ceto malamai da daliban da aka sace a jihar Oyo.

Majalisar ta ba da tallafin ne ga iyalan malamai biyu da suka mutu a hannun masu garkuwa da mutane, da kuma iyalan jami’an tsaro uku da suka rasa rayukansu a aikin ceto daliban jihar Oyo.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan ta'adda suka lakadawa dalibai da malaman Oyo duka a daji

Majalisar dattawa.
Sanatoci na tsakiyar zama a zauren Majalisar dattawa da ke Abuja Hoto: @NGRSenate
Source: Twitter

Leadership ta ruwaito cewa an ceto dalibai da malamai da aka sace daga makarantun Ahoro-Esinle, Yawota da Alawusa da ke karamar hukumar Oriire ta jihar Oyo a ranar 15 ga watan Mayun 2026.

A yayin aikin, jami’an tsaro sun kama mutane takwas da ake zargi da hannu a garkuwar, yayin da aka kashe wasu daga cikin 'yan bindigan.

Godswill Akpabio ya yaba wa jami’an tsaro

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne ya sanar da tallafin Naira miliyan 50 a zaman majalisar na ranar Laraba, 15 ga watan Yuli, 2026.

Akpabio ya bayyana cewa hakan wata karamar gudunmawa ce domin nuna godiya ga sadaukarwar malamai da jami’an tsaron da suka rasa rayukansu.

Ya yabawa Hafsan Sojin Kasa, Shugaban Hukumar DSS, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Ministan Tsaro da kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa rawar da suka taka wajen nasarar aikin ceton.

Akpabio ya ce:

“Tun daga Hafsan Sojin Kasa zuwa Darakta Janar na DSS, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Ministan Tsaro da kuma Babban Kwamandan Rundunonin Najeriya, muna yabawa da kokarinsu.”

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace shugaban makarantar firamare, suna neman N30m kuɗin fansa

Ya ce sanatoci sun yaba wa jami’an tsaron bisa jarumtakar da suka nuna tare da bukatar su ci gaba da kokarin ceto sauran yara da ke hannun masu garkuwa a sassan kasar nan.

Shugaban Majalisa.
Shugaban Majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio yana jagorantar zaman majalisa a Abuja Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

Za a raba N50m ga iyalan mamatan

Akpabio ya bayyana cewa shugabannin Majalisar Dattawa sun yanke shawarar tallafa wa iyalan mamatan, musamman yana ambaton wani Laftanar na sojoji mai shekaru 28 da ya rasa ransa a aikin.

Ya kara da cewa wannan tallafi wata hanya ce ta nuna godiya ga sadaukarwar da suka yi domin ceton rayukan daliban da malamansu, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Yadda aka ceto daliban jihar Oyo

Kun ji cewa sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro sun ceto dalibai da malamai 44 da aka yi garkuwa da su a jihar Oyo tun ranar 15 ga Mayu 2026.

An samu nasara a aikin ne a ranar 10 ga Yulin 2026, inda Manjo Janar CR Nnebeife, wato Babban Hafsan Rundunar Soja ta 2 da ke Ibadan, ya jagoranci dakaru zuwa daji.

Jami'an soja sun bukaci al'ummar Najeriya da su ci gaba da ba hukumomin tsaro labarin da suka sani domin taimakawa wajen kare rayuka a fadin ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262