Kofin Duniya: An Hango abin da Zai iya Kawo Cikas ga Wasan Ingila da Argentina
- Ana fargabar tsawa da guguwa kafin wasan Ingila da Argentina, amma jami'ai sun tabbatar cewa wasan zai fara a lokacin da aka tsara
- Filin wasan Mercedes-Benz mai rufin da ake iya buɗewa da rufewa zai ba da damar gudanar da wasan ba tare da matsalar yanayi ba
- Rahoto ya nuna cewa FIFA na bin dokokin Amurka kan tsawa, amma jami'an filin sun yi karin haske kan abin da zai faru a irin yanayin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka - Ana ci gaba da fargabar yiwuwar tsawa da guguwa kafin wasan kusa da na ƙarshe na gasar Kofin Duniya ta 2026 tsakanin Ingila da Argentina.
Yayin da ake wannan fargaba, wasu jami'an filin wasan sun tabbatar da cewa za a buga wasan kamar yadda aka tsara, ba tare da wani tsaiko ba.

Source: Getty Images
FIFA na bin dokokin hasashen yanayi a Amurka
Ƙasashen biyu za su fafata a daren Laraba, inda wanda ya yi nasara zai kara da zakarun Turai, Sifaniya, a wasan ƙarshe bayan ta fitar da Faransa daga gasar, in ji rahoton The Independent.
Za a take wasan ne da ƙarfe 8:00 na dare agogon Birtaniya, daidai da ƙarfe 2:00 na rana a birnin Atlanta, sai dai hasashen yanayi ya nuna yiwuwar tsawa da guguwa a lokacin da za a fara wasan.
A wasu wasannin gasar bana an samu jinkiri saboda tsawa, ciki har da wasan Ingila da Mexico a zagaye na biyu, wanda aka dakatar na tsawon sa'a guda bayan an ga walƙiya a yankin.
FIFA na aiki da dokokin Hukumar NOAA ta Amurka, waɗanda suka sanya sharadin cewa dole ne a dakatar da wasa idan an gano walƙiya a cikin mil takwas daga filin wasa.
Idan aka sake samun walƙiya, ana sake kirga mintuna 30 kafin a ci gaba, sannan 'yan wasa su tafi hutun dumama jiki na mintuna 15.
Yanayi ba zai kawo cikas a filin wasa ba
Sai dai filin wasan Mercedes-Benz Stadium, wanda ake amfani da shi a gasar a matsayin Atlanta Stadium, yana da rufin zamani da ake iya buɗewa ko rufewa, lamarin da zai ba da damar gudanar da wasan ko da ana ruwan sama.
Jami'an filin sun tabbatar da cewa wasan ba ya dogara da yanayin waje, don haka ba za a samu jinkiri ba saboda guguwa ko ruwan sama, a cewar rahoton The Standard.
Sun kuma bayyana cewa za a buɗe ƙofofin shiga filin awa uku kafin a fara wasa domin bai wa magoya baya damar shiga cikin lokaci idan aka samu sauyin yanayi.
An tanadi matakan kariya ga masu kallo
Gasar Kofin Duniya ta 2026 na gudana ne a Amurka, Kanada da Mexico, a lokacin da ake yawan samun guguwa da tsawa a wasu yankuna.
Saboda haka, an tanadi tsauraran matakan kariya ga 'yan wasa da magoya baya, yayin da masu shirya gasar suka ce za su ci gaba da sa ido kan yanayi domin tabbatar da lafiyar kowa ba tare da sauya jadawalin wasan ba.
Asali: Legit.ng

